Part 15

80 10 0
                                    

*RIJIYA TA BADA RUWA...!!*

*©️OUM MUMTAZ✍️*
                           

           *charpter 15*

******** Bayan wata biyu.

B'angaren Hajiya Alina kuwa duniya ce sabuwa ta bud'e mata,sabida yadda take fantamawa abinta cikin kud'i da kayan alatu na more rayuwa babu ji,babu gani! Domin kuwa sosai Alh ke sake jikata da nairori tana wadak'arta yadda take so! Kuma dik wannan bidirin da ake ko nan da kofar gida Alh bai taba barinta ta taka ba! Wanda a cikin wannan wata biyun rabo ya ratsa tsakanin su,domin kuwa tana da shigar karamin ciki na wata biyu cif cif! Wanda hakan kuwa ba karamin abin farin ciki bane a wurin Alh ,sabida yadda yake gano burin sa na gaf da idasa cikewa babu sauran gurbi.
Wanda zuwa wannan lokacin hatta ga yan aikin gidan saida suka san da zaman wannan cikin,sabida yadda Alh ke bala'in ji da ita,kamar t'soka d'aya a miya.

Akoi wata dattijuwar mata data kasance d'aya daga cikin ma'aikatan gidan,tausayin inda Alina ta jefo kanta kawai take! Domin kuwa ta tabbata cewa da ace tasan Alh wani irin mutumi ne a duniya tabbas ko mai kama da ma'aikacin gidan sa aka nuna mata saita sume tana farfad'owa.

Tabbas ta lura kwadayi ne da kuma son abin duniya irin namu na mata ke neman kaita ya baro ta,wanda ita d'in ma hakance ta kasance mata tin tana budurwata! Wanda har kwanan gobe na duniya takanyi nadama hadi da kuka akan irin k'ask'antaccen rayuwar data kefa kanta,dik don sabida abin duniya.

Gidan Alh babban gida ne mai fadin gaske! Wanda ko ta wani kusurwa ke cike da murdaddun mazaje masu jini a jika dake dauke da manya-manyan makamai masu had'arin gaske.

Sannan kuma akoi flat-flat a cikin gidan da akalla suka kai kusan guda goma,masu zaman kansu! Wanda tin zuwan Alina wannan gidan kuwa bata tab'a taka k'afarta zuwa ko ina na cikin gidan ba,sai nata flat d'in da Alh ya ajiyeta tin farkon zuwanta,amma hakan kwata-kwata bai dameta ba.

Bayan wannan kuma akoi wasu flate guda biyu masu girman gaske dake dauke da dakuna mabanbanta,wanda suka kasance na ma'aikatan gidan,d'aya na mata d'ayan kuma na maza.

Rayuwa na gangarawa,lokuta na tafiya,wanda zuwa wannan lokacin cikin alina yayi wani irin girma na ban mamaki haihuwa yau ko gobe,wanda ko tafiya k'wak'k'wara Alina bata iyayi,komai sai anyi mata wanda kuma har zuwa wannan lokacin ko dai-dai da rana d'aya tunanin mahaifiyarta,tare da yarta data tsallake ta tafiyarta bai zo mata cikin kwakwalwarta ba,sabida formating na kwakwalwarta da Alhaji yayi na karfi da yaji da hanyar gagarumin t'safi.

Yau Alina ta tashi da ciwon nak'uda babu ji babu gani,hankalin kowa a mugun tashe yake cikin gidan,sabida yadda aka kwana aka wuni ana abu daya,ga kuma Alhaji shi a dokarsa yace babu kai matar sa asibiti da sunan haihuwa. Inda ya saka wannan dattijuwar dake tausayin Alina mai suna *Baba Rabi* ta karb'i haihuwar kamar yadda take karb'ar na sauran matan nasa,wanda Alina sam-sam bata da san ma inda kanta yake ba.

******** A wata unguwa na talakawa likis Waali ya samu wani gida d'an k'aramin mai d'aki d'aya tare da band'aki ya saya cikin kudin sa tin a ranar daya sauka cikin garin kano tare da taimakon wani dattijo da suka hadu tin a motarsu daga can Maidugurin. Alhamdulillah Waali ya ambata a lokacin da yaga gidan dake matsayin mallakin sa.

Da shike akoi RIJIYA a cikin gidan,wannan dattijon ne da suke mak'waftaka dashi ya aiko jikansa ya kawo masu bokiti yaro d'an shekaru 6.

Da shike akoi wasu abubuwan su na amfanin gida na yau da kullum daya kwaso daga can gidan nasu,sai baisha wani wahala ba a ranar,domin kuwa hatta ga kayan abincin su daya rage sai da ya kwaso su.

Wanka yayi ma y'ar tasa,tare dashi kansa da ruwan cikin RIJIYAr,dikda irin kukan da yar tasa keyi gwanin ban tausayi,kasancewarta sabuwar haihuwa. Inda ya had'a mata madararta a fida irin na yara tasha ta koshi,kamin shima yasama cikin sa cake tare da zob'on daya saya akan hanya,yanayin sallar isha'i ya shimfida masu karamar katifarsa dayazo dashi irin na yan boarding school mai cin mutum daya,sannan ya daura masu net suka shige bayan ya rufe masu kofar su ta ciki.
Akan cikin sa ya daura yar tasa inda ya tofe masu addu'a,cikin kankanin lokaci kuwa baccin gajiya yayi awon gaba dasu dikkansu.

Washe gari da safe Waali yaji ana buga masu kofa,cike da mamakin wanda yazo masu kuwa ya bude kofar gidan,tare da Ummi dake kan kafadar sa tana sharar baccinta hankali kwance,wanda a daren wannan ranar sosai tama sa rigima wanda sai kusan asuba tayi baccinta.

Wata matashiyar budurwa ya gani da zatayi sa'a da Alina a shekaru kofar gidan,sai faman harare-harare take,fuskar nan ram da kwalliya na kwalli da jan baki kaca-kaca kota ina,sam babu kyan gani. Ga yanda ta d'ano bakin nan gaba yawa k'arin kunama.

"Malama lafiya kuwa?" Wani tab'e baki tayi cike da rashin kunya tace "Mallam dallah kauce man na shige! Ni ba Malama bace,yanzu ma badan Baba ya matsa man sai nazo na maka shara ba ai da bazaka ganni ba!"

Ta fada tana mai bangaje Waali ta kutsa kanta cikin gidan,shi kuwa ya bita da kallon mamaki baki sake! Amma kuma da yayi tunanin wane Baba take nufi,sai ya tuno tsohon jiya da sukazo tare.

A ransa kuwa mamaki yake ta yadda akayi wannan fitsararrar ta zamana y'ar gidan wannan tsohon mai sanin darajar d'an Adam, girgiza kai kawai yayi,had'i da rufa mata baya yana girgiza kai.

Share-sharen gidan take,sai faman mita da tsaki take zubawa akai akai! Shi kuwa Waali banda kallon ikon Allah babu abinda yake yau dinnan a ransa fadi yake na rayu tsawon shekaru da wacce ta fiki fitsara.

Cikin awa d'aya wannan budurwar fes ta kammala share dik wani lungu da sako dake cikin gidan,had'i da jere kayayyakin data gani a inda suka dace,ba tare data ma Waali dake ta faman jijjiga yarsa sallama ba tayi tafiyarta! Harda ladan bugo masu kofa kamar zata balle sa.

Kamar jiya yauma dai da ruwan sanyi sukayi wanka,wanda yauma saida yarinyar tasha kukanta,sabida babu abinda tafi bukata a wannan lokacin sama da ruwan dumi,bawai mai sanyi ba.

Inda ya hada mata garin madarar ta,saida ya tabbatar ta koshi,kamin ya d'auki zanin dayake nannade ta ciki yayi mata goyo mai rai da lafiya kamar bana miji ba,ya bude k'ofar gidan da niyyar fita, sukayi clashing da jikan Baba wanda ya kawo masu bucket jiya(kamar yadda yaji yarinyar dazu ta fada) hannun sa rik'e da wani kwano na samira, mikama Waali yayi bacin ya gaishe sa yace "inji kaka yace akawo maka"

Waali kuwa cike da jin dadi yace "Kace masa na gode sosai."   Wanda dama fita zayyi domin neman abinda zaici koda kosai ne irin wanda ake sayarwa da safe.

*vote*
*comment*
*share*
  
*OUM MUMTAZ✍🏿*

RIJIYA TA BA DA RUWA???? Donde viven las historias. Descúbrelo ahora