Part 25

77 9 0
                                    

*RIJIYA TA BA DA RUWA...!!*

 
*©️OUM_MUMTAZ✍️*

_WANNAN LITTAFIN TIN DAGA FARKON SA HAR K'ARSHEN SA NA SADAUKAR DASHI GA ~MSS FLOWER🌸🌸~ MARUBUCIYAR:_
~LAFAZI~
~AR SO~
~SARKI~
~GUMBAR DUT'SE~
_SON SO FISABILILLAH❣️💃🥰❣️❣️_                          
   
           *Charter 25*

******** Hankalin UMMA idan yayi dubu ya tashi a wannan lokacin,cike da kid'ima suka fita daga cikin gidan tare da Himu,tare suka kinkimo Alina dake nad'e cikin bargo da bata san ma inda take ba,zuwa cikin gidan nasu da zuciya d'aya,dikda t'sufan daya kama UMMA sosai hakan bai sata zama ba,saima wankan da tayi ma Alina da kanta,sannan ta saka mata kaya dikda yayi ma ALINA d'in yawa amma dai yafi zama haka nan!

Sannan ta gyara mata kwaciyarta suka tofe da addu'a ba kad'an ba,wanda kuma zuwa lokacin wani bacci ne yayi gaba da Alina mai cike da mafarkai barkatai marasa kan gado! Sai a lokacin UMMA da kuma d'an nata suka gaisa,sannan shima yayi sallah suka ci abinci,wanda suka zauna hira a k'aramin parlon nata,anan suka ga an hasko abinda ya faru cikin akwatin talabijin!!
Sosai suka jinjina wannan abin,wanda har cikin zuciyar su tunani suke kan mai yakai d'iya mace wannan wurin?? Fatan su dai Allah yasa kar Alina ta cuce su idan ta farka,kasancewar rayuwar mu ta yanzu taimako ma ya zama abinda ya zama.

A gigice dik sukayi kan Alina sabida ganin yadda ta farka cikin mummunar yanayi kamar wata mahaukaciya sabon kamu,sanadiyyar mafarkin da tayi da Alh yana mata ihu kan ta zama silar ajalin sa!
Da k'yar suka samu damar controlling nata ta hanyar addu'ar da sukayi cikin ruwa suka d'ura mata,sannan kuma suka shafe mata jikin ta dashi! Sai faman rarraba idanun ta take ga dikkan alamu hankalin ta ba jikin ta yake ba,sabida maganar da sukayi tayi mata amma sai dai tabi su da ido alamun bata ma san mai suke fad'i ba,wanda muddin ta rint'sa idanun ta hoton lokacin da Alh ke fard'e mata y'ay'an ta da kuma hanyar da yabi wajen raba mahaifiyarta da duniya ne ke fad'o mata,sai kuma daga nan ta razana!

Ga kuma wani masifaffen ciwon kai da ya sako ta a gaba,sabida fad'owar da tayi akan motar shi Himun!
Saida Himu da kansa yayi mata d'uren kunun hat'sin da UMMA tayi sabida yadda taki cin dik wani abinda suka ajiye mata,saidai ta bisu dana mujiya!

Ana yin sallar isha'i yaje chemist ya taho tare da yaron shagon da ya kasance nurse ne,ciwon dake goshin ta aka wanke mata had'i da dressing na wajen wanda nan d'in ma da kyar aka samu akayi sabida yadda take ta faman fisge-fisge.

.........

Kwanan wannan ranar gaba d'ayan ta UMMA da HIMU sun yi ta ne cikin hidimar Alina da ta kwana cikin mawuyacin hali suna kulawa da ita.
Washe gari kuwa da safe bayan HIMU ya tafi sallar asuba yayi ma limamin nasu bayanin suna da mara lafiya a gida,da suke buk'atar taimakon sa! Wanda hakan yasa tare suka zo da wani malamin da shima d'an unguwar ne,a lokacin UMMA ma ta idar da sallar asuba,sannan kuma Alina ma ta samu baccin da bata samu yi daren jiya ba!

Karatu suka farayi mata baji babu gani a wannan lokacin har wayewar gari kamin suka samu ta mot'sa daga inda take kwance! Wanda nan take suka fuskanci bawai aljanu ne da ita ba,illa firgicewa da take ta faman yi akan wani abinda ta gani da idanun ta!

Bayan sun tafi liman ya aiko masu da wani ruwan zam-zam cikin gora kan su tabbatar da sun bata tasha,da zarar ta farka da yaddar Allah komai zai zama dai-dai!

Ai kuwa suna bata d'in ta kwanta wani nannauyen bacci yayi gaba da ita, wanda cikin baccin nata sai faman had'a zufa take baji ba gani! T'sawon lokaci ta d'auka tana bacccin kamin ta fardad'o,wanda kuma cikin ikon Allah garas ta farka babu wani alamu na tab'in hankali kamar yadda ta fara da farko! Sai kuma ta fashe da wani irin rikitaccen kuka da ya sake tadar ma dasu UMMA hankali ba kad'an ba, sunyi lallashi iya lallashi da kuma bada baki kamin suka samu kanta! Sallah suka fara saka ta tayi,kamin suka bata abinci taci,had'i da bata magungunan ta na jiya tasha nan da nan kuwa wani baccin ya sake gaba da ita,sabida akoi maganin bacci cikin magungunan nata.
T'sawon kwana uku su UMMA suka d'auka suna bata t'saftatacciyar kulawa kamar jinin su babu kyara ko t'sangwama dik da har zuwa lokacin ko sunan ta basu sani ba!!

UMMA ta k'ira YAYA kan tana naiman sa shida BABI,wanda kuma a ranar suka kamo hanya zuwa Kaduna,sai kuma suka tarda bak'uwar fuska,nan UMMA ta masu bayani kamar yadda HIMU yayi mata,wanda a ranar kuwa suka saka ta a gaba tana kuka da komai ta basu tarihin rayuwarta kaf,babu dad'i babu k'ari!
Tare kuma da jaddada masu nadamar ta k'warai da gaske,ta kuma buk'aci da su taimaka mata da kud'in mota zuwa maiduguri sabida dubo y'arta da kuma yayan ta! Washe garin ranar BABI ya koma suleja,inda YAYA da HIMU kuma tare da UMMA suka wuce Maiduri tare da Alina!

Wanda basu suka isa ba,sai magriba,don haka sai suka samu masauki a hotel tinda dama YAYA kam yana da arziki babu laifi,washe gari da safe waja jen k'arfe sha d'aya suka tafi unguwar su Alina d'in tana masu kwatance har k'ofar gidan sabida bata manta komai ba!
Kan kace me?? Mutanen unguwa suka ankare da Alina wanda nan da nan aka taru a wajen ana mata tofin ala t'sine tare da Allah ya wadai da masu irin halaiyar ta tinda gashi a ta sanadiyyar bak'in cikin ta mahaifiyar ta tabar duniya! Sannan kuma Waali da y'arsa sun shiga duniya da ba'asan inda sukayi ba bayan ya saida gidan su!

Ai kuwa ba k'aramin tashi hankalin ta yayi ba,jin cewa ba'a san inda Waali da y'arta suke ba,wanda ta fara tunanin k'ila sud'in ma ALH ne ya kashe mata su kamar yadda ya kashe mata mahaifiya akan idanun ta.
Sun bar number na wayan su kan don Allah dik ranar da WAALI ya waiwaye su su k'ira su shaida masu,sabida zasu tafi tare da Alina can KADUNA,sanna kuma suka basu adress nasu!

Haka nan suka koma babu wani daddad'an labari suna ta lallashin ta tare da nuna mata kuskurenta akan abinda ta aikata.
HIMU da YAYA sun koma ABUJA,sannan suka bar ALINA tare da UMMA  kamar yadda ta buk'ata.

…………

Tin daga wannan lokacin sai ya zamana dik wasu aikace-aikacen gidan Alina ce ke ma UMMA da ta d'auke ta mat'sayin mahaifiya,bata barin UMMA tayi ko dai dai da nad'e sallayar da tayi sallah,gashi kuma HIMU da kansa ya aiko ma UMMA kud'i ta saka ta a ismiyya wanda hakan ko sosai yayi mata dad'i!! Rana ku d'ai-d'ai ne Alina bata kuka idan ta tuno da WAALI tare da y'arta da bata san ma sunan ta ba!

Cikin k'ank'anin lokaci Alina ta saba da family na UMMA baki d'ayan su kowa ya santa itama ta sansu sabida zuwar masu da ta tab'ayi,sosai kuwa YAYA K'ARAMI jinin su ya had'u da ita,wanda yasa akai akai yake kaima UMMA ziyara idan sunyi hutu,wanda kuma da ba haka bane,sai ya zamana UMMA takanyi masa t'siya kan wai kodai za'ayi y'ar gida ne irin lik'ema y'ar kyakkyawa haka.

Tayi sabo da mutane sosai kuwa,t'sawon shekaru biyu suka d'auka tare da Alina,wanda kuma har zuwa lokacin babu wani kyakkyawan labari game da bayyanar Waali da kuma y'ar tata.
Soyayya ce mai k'arfi ta k'ullu t'sakanin HIMU da ALINA wanda kuma hakan yayi ma su UMMA dad'i ba kad'an ba,an saka ranar auren nasu,inda YAYA shine yayi mata komai na auren kamar yadda ake ma y'ar gata,shima gidan sa da ya gina a suleja ne,wanda suke makwaftaka da BABI,katanga ce kawai ga raba su!
Anyi aure lafiya an wat'se an bar UMMA da kewa wacce girma ya riga da ya kamata.

*vote*
*comment*
*share*
  

RIJIYA TA BA DA RUWA???? Where stories live. Discover now