Part 12

68 11 0
                                    

*RIJIYA TA BADA RUWA...!!*
     

*©️OUM MUMTAZ✍️*

           *charpter 12*

******** Yau ta kama ranar laraba.

Waali ne ya shigo gidansa da gajeruwar sallama d'auke a bakin sa,wanda kallo d'aya idan mutum yayi masa,zai fuskanci zallar damuwar dake tattare dashi,ga wani irin rama da yake ta faman zubawa a t'sait'saye sabida damuwar da suka masa yawa bana wasa ba!

Alina ce zaune daga bakin dakin ta,ta mikar da kafafunta inda gabanta kuwa wata laida ce ta bank'ararriyar kaza dake ta faman tururi yana tashin kamshi! Yagar kazar ta takeyi hankali kwance,tana korawa da hollandia!

Da mamaki Waali ya idasa shigowa cikin gidan nasa,sabida abinda idanunsa ke gane masa,domin kuwa shi kam a iya sanin sa dik wasu basissikan da yake ciyowa kansa wajen sayo ma Alina kayan dadi bai taba sayo mata irin wannan kazar ba,sabida kazar sai wane da wane ne kan iya sayan ta bawai yaku bayi irinsu ba!

Zama yayi a bakin tabarmar cikin tuhuma yace, "Alina a ina kika samo kudin sayar wannan kazar kuma?"
Banza tayi masa kamar bata san da ita yake ba,tana mai ci gaba da yagar kazar ta kamar wata koron yunwa!
Cikin kaushin murya yace, "Ba da ke nake magana ba?"
D'an dakatawa daga cin kazar tayi,had'i da yi masa wani irin kallo na shek'ek'e cike da fit'sara tace, "Ina ruwan ka da inda na samu kud'i,tinda kai ka kasa yima matar ka abinda take so?"

Da shike dama yau din zuciyarsa a kusa yake,abinka ga mutumi wanda bai sabayin fushi ba dama ance ka guji ranar da yayi fushin ba zaka ji da dadi ba! Ware muryar sa sosai yayi cike da tsananin hasala ya buga mata tsawar data kusan zautar da ita yace "uban waye ya baki kud'i kika sayi kaza nace!!!!!"

Jikin Alina ne ya dauki rawa sabida sabon yanayin data gani a wajen mijin nata da ba ta saba ganin haka ba! Ta matsa baya tare da laidar kazar ta!

Wani wawan fusga yayi ma laidar dake hannunta,hadi dayin cilli tashi sama,saiga kaza kuwa ta dawo kasa,cikin kwatamin dake daga can wajen makwararin wanke wanke!

Wani irin ihu Alina ta sake kamar wacce aka yanki namar jikinta sabida ganin inda kazarta ta fad'a! Dikda cikinta dake mata kugi akan yanayin da Waali ke ciki ba,hakan bai sata yin wani uban tsalle ba sai gata ta diro a gabansa taci masa kwalar rigarsa cike da t'sant'sar masifa da kuma bala'i gami da tsiwa tace "wallahi Waali baka isa ba!! Nace baka isa ba! Wallahi saika biyani kazata kona tara maka jama'a tinda bakai ka sayo man ba,baza ka hana ni ci ba!!"

Abinku ga zuciya na kusa,wasu irin tagwayen maruka ya fara jere mata su a fuska,cike da tsananin hasala da tinda yake a rayuwarsa bai tab'a yi ba!

Amma da shike taurin kai na mata yawo cikin kwanya,k'in sakin sa tayi,bakinta bai mutu ba,saima uban ashariya dake sakin masa marasa dad'in ji! Wanda har mak'wafta ana juyo su,abinku ga geto area nan da nan mutane suka cika cikin gidan yan gulma,amma aka rasa wanda zai shiga tsakanin wannan fadan,sai faman Allah shi kara ake ma Alina akan irin jibgar da take sha a hannun Waali a dai-dai wannan lokacin yana saita fad'a masa uban daya bata kudi ta sayi kaza tana bazata fad'a ba!

Iyami kam baiwar Allah tin farkon fad'an nasu tana jinsu daga kewayen ta,amma haka nan taki fitowa daga d'akin nata sabida tasan yau Alina takai Waali iya mak'ura ne daya sa shi laftar ta baji ba gani! Wanda kuma tasan muddin taje ta kwaci Alina a hannunsa ba tayi masa adalci ba! Hakan yasata k'in fitowa ma daga cikin dakinta,dikda hayaniyar mutane da take jin ya cika gidan,kuka take a wannan lokacin sabida bak'in ciki da kuma takaicin halin diyar ta,da batasan inda ta kwaso su ba, wannan shi ake cewa ka haifi d'a,baka haifi halinsa ba,kuma albasa batayo halin ruwa ba!

Wannan magidanci mai kudin dake sake hurema Alina kunne ne ya fad'o cikin gidan tare da yan sanda kamar wanda aka koro su! Wanda a wannan lokacin kuwa sosai Alina taci na jaki a hannun waali kamar bazai barta da rai ba! Inda yan sandan sukayi kansu da kyar aka banbare ita Alina din daga hannun Waali! yan sandan suka rirrike sa,had'i da koran dik mutanen dake cikin gidan! Har zuwa lokacin kuwa ko leke Iyami batayi ba,saima kukan ta daya t'sananta sabida bakin ciki gami da takaici!

RIJIYA TA BA DA RUWA???? Where stories live. Discover now