Part 18

73 12 0
                                    

*RIJIYA TA BA DA RUWA...!!*

    *©️OUM MUMTAZ✍️*
      

           *Charpter 18*

******** Wani irin gumi ne ke t'sat'st'safo ma Alina a lokacin da ta gama jin labarin da Baba Rabi ta bata mai tarwatsa k'wak'walwa.

Sosai ta shiga cikin mat'sanancin ciwon kai gami da tashin hankali mara misaltuwa,dafe kan ta tayo,dik wasu memories nata da tayi loosing sun fara dawo mata cikin k'wak'walwarta daki-daki,
sosai gaban ta yayi wani irin mummunar bugawa,a lokacin da k'wak'walwarta ta hasko mata d'anyen haihuwarta data tsallako ta bari dik dan sabida abin duniya da ba mai dore wa ba!! Mahaifiyar ta Iyami ne ta sake fad'o mata cikin k'wak'walwarta,gami da d'an uwan ta,kuma mijin ta mai k'aunar ta da dikkan nin zuciyarsa,amma ta watsa masa k'asa a ido dik dan sabida _KWAD'AYI_ !

Wani irin rikitaccen kuka ta fashe dashi mai cike da t'sant'sar nadama da kuma dana sani! Baba Rabi kuwa tuni ta fice daga d'akin simi-simi sabida kar Alhaji ya gano su ta cikin madubi ta shiga uku,domin kuwa babu tantama idan yasan cewa ta fad'a ma Alina ko shi wanene tin kamin ya cika kud'irin sa karshen ta ta bak'unci lahira a yau yau d'innan! Sai dai kuma abinda bata riga ta sani ba,tin farkon fara zancen su! Har suka dasa aya akan idanun Alh ne! Tare da mutane marasa tsoron Allah ire-iren sa da suke k'ok'arin aiwatar da idasa cike nasu k'udirin ta hanyar aika Alina barzahu su bama dodon tsafin su jinin ta!

Wani irin gagarumin b'acin rai ne ya ziyar ce su baki d'aya,a lokacin da suka ga Alina ta k'ank'ame yaran ta baki d'ayan su tana bulbulawar ruwan hawaye,sannan kuma tana tofa masu dik wasu addu'oi da suka zo bakin ta,wanda hakan yasa dik wasu power nasu ya fara raguwa! Hakan ko ba k'aramin sake b'ata masu rai yayi ba,cikin abinda bai gaza minti d'aya ba,sai ga Alina rungume da yaran ta,tare da Baba rabi durk'ushe gaban way'annan munatanen da suke zindir haihuwar uwar su!

"Kin aikata gagarumin kuskure a rayuwar ki Rabi! Wanda hakan da kika aikata dai-dai yake da kawo k'arshen shan ruwan ki a duniya! Tabbas yau ba sai gobe ba!!! Yanzu ba sai anjima ba zaki bak'unci lahira! Zaki je ki tadda masu bakin akku irin naki da basu iya shuru su k'yale akan dik abinda zasu gani cikin gidan nan! Wanda nake tunanin hakan shine hukunci mafi sauk'i da zan iya yi maki!"

Alhaji ne ke wannan maganar cikin tsananin b'acin rai da yasa har halittar jikin sa ke fara canzawa daga na d'an Adam zuwa wata halitta ta daban! Take jikin Alina da Baba Rabi ya fara d'aukar b'ari suna sakin gigitaccen kuka mai tada hankalin mai sauraro! Dik wata addu'ar data zo bakin ta Alina yi take babu k'ak'k'autawa,tana rungume da yaran ta tamkar zata mai da su cikin cikin ta!

Allah sarki Baba Rabi! Banda karkarwa babu abinda jikin ta keyi,ga kuma addu'ar da itama take da buk'atar yi hakan ya gagara,domin ko abinda yasa Alina Allah ya bata ikon yin addu'ar sabida tonuwar asirin su ne da tayi kamin su kai ga cimma manufar su akan ta!

Take cikin wannan d'akin ya kacame da wani irin gurnani mara dad'in sauraro ga cikakken d'an Adam.

Sai kuma wasu irin dariya mai tafe da kuka mara sa dad'in ji daga mabanbantar murya daya karad'e cikin wannan d'akin kamar zai t'saga bango!!! Wani irin duhu ne ya mamaye d'akin da ko tafin hannun ka bazaka iya gani ba,wanda hakan ya sake razana Alina matik'a! A dai-dai wannan lokacin banda kaico da masu halin kwad'ayi irin nata babu abinda takeyi! Bata t'sagaita da yin addu'ar dake fitowa daga bakin ta ba, sai dai kuma yanzu idanunta a bud'e yake tana lalumar gefen da Baba Rabi take da k'afafun ta amma wayam bata ji ko alamar numfashi ba,ballantana mutum!

Wani irin haske ne ya mamaye cikin wannan d'akin mai kashe idanu da sai da Alina ta lumshe idanun ta kamin ta bude su bayan tsawon lokaci!

Wani irin zaro idanuwan ta tayi waje cike da t'santsar firgici har tana naiman hant'salawa sabida abinda idanunta ke gane mata! sake murza idanuwanta tayi da kyau domin tabbatar da abinda idanun nata ke gane mata! Ai wani irin cilli tayi da yaran kamar wasu kiyashi sai gasu sun baje a k'asa,a wani irin gigice ta mik'e da niyyar zuwa inda ta gano Baba rabi tare mahaifiyarta rayaye jikin gini tsirara haihuwa uwar su suna kallon ta,suna kuma girgiza mata kai alamun karta k'araso inda suke,kamar abu a iska, sai ji kawai tayi anyi wani irin cilli da ita daga sama zuwa k'asa da yasa ta callara wani uban ihu tace "IYAMI!!!!!"

********Washe gari da safe.

Zulaykha taji dad'in jikin ta ba kad'an ba,amma kuma sam ta kasa yima kowa magana tinda ta farka,sai dai ta lumshe idanun ta idanun ta na hasko mata fuskar Yaya da Husnah a daren jiya dake ta faman walwali had'i da fidda annuri alamun suna cikin t'sant'sar farin ciki maras misaltuwa sukan ziyar tar kwakwalwarta.

Babu yadda Abbah,Jiddah da kuma Musty basuyi da ita ba,kan ta fad'a masu damuwar ta amma sam tak'i tace masu k'ala sai dai ta bisu dana mujiya! Tana ji cewa a cikin jinin jikin ta ko mutuwa zatayi da son wannan bawan Allah n bazata tab'a barin duniya tasan halin da take ciki ba koda kuwa hakan zai zama ajalin ta!

Wasa-wasa dai sai da Zulaykha ta shafe t'sawon sati guda kamin ta gama dawowa cikin hayyacin ta,wanda kuma Jiddah ta wuce gidan su tin bayan kwanaki uku da suka gabata sabida ganin jikin nata da sauk'i,sannan kuma dik wannan tsawon kwanakin Abbah ya  tare ne a wajen y'ar sa yana bata dik wasu kulawan da suka kamata a mat'sayin sa na uba,kuma sannan mahaifiya!
Musty ma dai ba'a bar sa a baya ba,dik da shine yake fita wurin aiki amma yana bata dik wasu kulawan da suka kamata!

Mamy ce ma dai gashi dai,ba laifi tana d'an bata kulawar dik da ba wani har can ba amma hausawa suka ce da babu gara babu dad'i wai.

"Mama nah akoi maganar da nake so muyi dake dama idan babu damuwa!!!" Abbah ya fad'a yana blushing kamar wanda ke jin kunyar y'ar tasa,Zulaykha dake kwance kan cinyar Abbah nata ta d'an saki k'aramin murmushi had'i da gyara  kwanciyar ta da kyau tana mai fuskantar mahaifin nata tace "karka ji komai Abbah nah,ka fad'i dik abinda ke cikin ranka zuwa gare ni,a kuma dik lokacin da kaga dama Abbah nah,sbd nid'in a karkashin ka nake ba sai ka nemi izini nah ba a dik lokacin da ka son yin magana da y'ar ka!!"

Cike da jin dad'in maganganun d'iyar tasa Abbah yace "To - to-to y'ar albarka nako ji dad'i sosai da wannan kalaman naki! Ina so na sanar dake ne dama idan Allah ya yarda cikin ikon sa nan da 1month zan kawo maki sabuwar Mommy cikin gidannan"

Cike da t'sant'sar mamaki Zulaykha ta zaro idanuwa waje tana kallon mahaifin nata da shima ke kallon ta domin ganin a yanayin da zata amshi batun nasa!

Mik'ewa daga kwancen da take Zuly tayi tana gyara zaman ta da kyau cike da tsantsar farin ciki daya gazo b'oyuwa akan fuskar ta tace "gaskiya na matik'ar jin dad'in haka nan Abbah nah! Allah yasa mutuniyar arziki ce da zata zauna damu zuciya daya tamkar uwar data t'suguna ta haife ni babu t'sangwama!!!"

Tayi maganar tana mai tunano wasu irin hali na i don care da Mamy ke nuna mata a lokuta da dama,tinda ta kawo kai wanda bata san dalilin canzawar tata ba sabida da ba haka nan takeyi mata ba!

Sosai kuwa Abbah yaji wani irin tausayin ta,had'i da sake d'aura d'amarar sake yin wannan aure da Dad d'in Jiddah yayi masa magana akan auren k'anwar sa wato Anty Khadeeja.

*vote*
*comment*
*share*
  

RIJIYA TA BA DA RUWA???? Where stories live. Discover now