Part 10

75 9 0
                                    

*RIJIYA TA BADA RUWA...!!*
    
                                   

           *charpter 10*

******** Sosai Abbah yabi ya rikice, yana tambayar ko wani ne a cikin gida ya b'ata mata rai? Amma tace masa babu komai,kawai tunowa tayi da mahaifiyarta! Wanda hakan yasa Abbah yi mata wani irin shegen kallo da babu shiri ta hadiye kukan nata,kirjinta na dukan tara tara. Kwafa Abbah yayi,ya fice daga dakin ba tare daya sake ce mata k'ala ba,wanda hakan yasa jikin Zulaykha yin sanyi bana wasa ba,harma taji rashin kyautatawarta akan fitowa fili da tayi ta nuna tana bukatar mahaifiyarta,bacin kuma shi bai rage ta da komai ba a fannin nuna t'sant'sar kulawa,gami da tsafta tacciyar kaunar da bata da algus.

Cike da sanyin jiki ta share hawayen dake kan fuskarta,tana mai jin haushin kanta ba kad'an ba,sandiyyar b'ata ma mahaifinta rai da tayi,akan matar da ta nuna bata kaunarta tin kamin ta fito duniya,zuwa ga ranar da ta haifo ta!
Bayi ta shiga tayo wankan ta fes,ta fito had'i da murza manta mai sanyin k'amshi,sannan ta shirya kanta cikin wata riga doguwa ta roba,da yabi ya lafe mata a lafiyayyen farar fatar jikinta,inda kuma yau y'an saka kallabi na kusa,dan haka saita saka hular rigar,had'i da feshe jikinta da turaren ta mai dad'in gaske! Wayarta guda ta d'auka,ta fito daga nata dakin cike da nat'suwa zuwa inda zata tarda mahaifinta,kasancewar yau lahadi ne babu zuwa wajen aiki.

Mamy ta tarda a parlo tare da Musty suna magana kasa-kasa,ganinta da sukayi ta shigo parlon ne yasa su yin gum da bakin su,dik suka bita dana mujiya daya sa taji wani iri.

Dan haka sai bata zauna ba,gaishe su tayi,had'i da fad'in, "Abbah na yana ciki kuwa Mamy??" wani irin kallo Mamy tayi mata na kasan ido,kamin ta waske had'i da fad'in, "Wato Abban naki ke kad'ai ko Ummi?? shi kuma Mustapha ba Abban sa ba??"

Dan daburcewa Zulaykha tayi kan maganar da Mamyn ta fada,sai kawai ta saki murmushin yak'e ba tare data ce kala ba,tana wasa da yatsarta dake cikin bakinta!
"Ki shiga yana ciki" ta tsinkayi muryar Musty na bata ansa,kamar jira take kuwa ta wuce harda da dan saurin ta,sabida jin yadda idanun Mamy da Musty ke mata yawo a jikinta dik ta tsargu.

"Mamy irin wayannan maganganun bai kamata suna fitowa daga bakin ki ba dai, ko ba komai dai kina da sanin cewa itace yarinyar da nake da muradin ta zam to uwar y'ay'ana ko??"

Wata shegiyar harara Mamy ta watsa masa,ba tare data ce masa ci kanka ba,ta mik'e fuu ta wuce zuwa nata dakin,shi kuwa tabe baki yayi,gami da zunkud'a kafada alamun ko a jiki na,kamin ya bama wandon sa iska zuwa nasa part din,yana kuma sake sawa cikin ransa babu wanda zai mallaki Zulykha a matsayin matar aure idan bashi ba.

Da y'ar karamar sallama ta idasa shigewa hadadden parlon mahaifin nata,da bashi da wani girma,domin kuwa baikai parlon farko girma ba,amma kuma yafi sa haduwa nesa ba kusa, ganin bata tarda sa a parlon bane yasa ta kut'sa kanta zuwa bakin bedroom,kwankwasa kofar tayi kusan sau uku amma bataji alamun da mutum bama,ballantana kuma akai ga bata iznin shiga,d'an turo kofar dakin tayi a hankali,hadi da laika kanta,inda idanunta suka sauka akan fuskar mahaifin nata,daya buga wani uban tagumi,ya lula duniyar tunani tin fitowarsa daga dakin Zulaykha,wanda dik bugun kofar da take masa baima san tanayi ba,sbd zurfin dayayi a cikin tunanin sa.

Nannauyen ajiyar zuciya ya sauke,had'i da lumshe idanunsa a lokacin da yaji Zulaykha a bayan sa,ta kwantar da kanta,hawayen idanunta na zuba akan gadon bayan sa,take yaji zuciyar sa ta karye!
Sake rint'sa idanun nasa yayi da suka kada,sukayi jawur dasu!

Mai do da ita ta gefen sa yayi,inda shima ya juyo yana kallon ta,yana jin zuciyarsa sam babu dadi kan kukan da take,kwantar da kanta yayi kan kafadar sa,yana bubbuga bata bayan ta alamun lallashi,wanda shima tabbas da ace zai samu wanda zai lallashe sa d'in yana so! Amma kuma yasan tabbas babu wannan a duniya kwata-kwata sabida shidin bashi da kowa a duniya sai yarsa k'wallin kwal guda daya wato zulaykha!!

******** "Sannu da aiki Ammi na!" Yaya ya fada a lokacin da ya karbi tankaden da mahaifiyar tasa keyi,wanda har zuwa lokacin murmushin dake kan fuskar tasa bai gushe ba! Sam fuskarta babu wata walwala a lokacin sabida shidin ma haushin sa take ji! tace, "yawwa." A tak'aice.

Take kuwa Yaya yasha jinin jikin sa,sabida yasan tat'suniyar gizo bata wuce ta koki! Gum yaja bakin sa ya t'suke,yaci gaba dayi mata tankad'en daga durk'ushen da yake,wanda har a jinin sa yake jin kaifin irin kallon da mahaifiyar tasa ke jifan sa dashi,wanda yasan ba kallon komai take masa ba,sai kallon wanda baya kishinta kwata-kwata a matsayin ta na mahaifiyarsa.

"Jarababbe kawai" Ammi ta fada a lokacin da take mikewa daga inda take ba tare data sake masa magana ba. Dariya ce ke son kamasa,amma haka nan ya gint'se abarsa sabida gudun sake tafka wani laifin,yana mai ci gaba da tankade mata garin nata,fes kuwa ya gama,had'i da rufewa kirif a cikin kafilas d'in,ya karkade hannayen sa da suka baci da gari,ya d'aga murya ta yadda zata jisa yace "Ammina na gama maki tankad'en na wuce masallaci"

Can ciki Ammi dake cikin dakin ta tare da y'ay'anta,tana juyo sa tace "To Allah ya tsare man ku baki daya."

Tare da Babi suka dawo daga masallaci sallar la'asar,inda a dawowar su gida suka tarda har Husnah ta farka,tana sanye da wani rigarta na sanyin daya hurata ba kadan ba,sabida yadda yayi mata girma,wanda asalin rigar ta Yaya ce amma yayi mata kyautar sa.

Ammah,Waleed tare da Husnah na zaune daga kofar dakin su akan tabarma,sai kuma su hidaya dake karkashin bishiyar dirmi su ukun su,suna assigment nasu da aka basu a school,wanda shima Waleed Husnah ce ke koya masa.

Ammi kuwa tana can cikin madafar su ta langa langa tana had'a masu abincin dare sbd yau itace take da girki.

Kamar yadda Babi yace yana naiman Yaya din kuwa,tare dashi suka sake fitowa daga gida,inda suka tari abin hawa akan babban hanya zuwa cikin garin Abuja daga Suleja.

******** Bayan wata hudu.

Zuwa wannan lokacin sosai cikin Alina ya girma,domin kuwa ta shiga cikin watar haihuwarta yau ko gobe! wannan acikin wayannan watannin babu irin cin kashin da Waali bai fuskanta ba daga wurin Alina,ga wani irin dan iskan bashin dake kansa dik ata sanadiyyarta! Wanda tasan yanayin samun sa,amma haka nan sai ta murzama idanunta toka tace ita ga abinda take so,bawan Allah kuwa da shike ya kwalllafa ransa akan wannan cikin jikinsa na mazari zaije ya kawo mata koda kuwa bashi da ko sisi! Iyami tayi fadan,ta kuma yi nasihar amma dik a banza domin kuwa Alina kam tayi nisa sam batajin kira! Ga wani dan iskan rashin kunyar data tsiro dashi cikin gidan,na yau daban,na gobe daban! Amma haka nan Waali ke kauda kai kamar baiga abubuwan da take masa ba.
Wanda abin nata da har yakai ya kawo ta matsa ma Waali kan lallai lallai sai ya saketa dik randa ta haifa masa wannan banzan cikin nasa! Badon yanajin zai iyaba,sai don a zauna lafiya yace mata yaji ya yarda.

sannan kuma bugu da kari akoi wani dan iskan mai kudi da yazo masu bakunta a unguwar tasu magidanci,shine yabi ya sake zuzzuge Alina,sabida tin kallon farko da yayi mata ta sace masa zuciya,wanda ita kuma ta masa alk'awarin aure tana haihuwa sabida ta gansa Alaji mai kudi! Kuma dik wannan abu da ake har zuwa lokacin Iyami bata da labari sabida a munafurce sukeyin dik wani shirye shiryen su!
Yau ta kama ranar laraba!

*vote*
*comment*
*share*
  
*OUM MUMTAZ✍🏿*

RIJIYA TA BA DA RUWA???? Where stories live. Discover now