Part 7

77 8 0
                                    

 

*RIJIYA TA BA DA RUWA*

           *charpter 7*

********Musty da dawowar sa daga restaurant,hannun sa dauke da laidar da yayo ma zulaykha order ya wuce office dinta,saboda jin shuru bata fito ba.A firgice ya yi fatali da laidar da ke hannunsa,had'i da kwalalo idanuwa waje saboda ganin Zulaykha da ya yi kwance shame-shame tsakiyar office nata,babu alamun numfashi tattar da ita,ga kuma wani irin fari sol da fatar ta, ta sake yi.

Bai yi watawata ba ya sungume ta a 360 ya fito daga office d'in,saboda ba ta da nauyi ko kad'an,uku-uku yake taka step d'in yana saukowa hankali tashe.
Ma'aikatan da ke harabar wurin kuwa duk tasowa suka yi saboda ganin yanayin da oga Musty ya fito da madam d'in nasu,suna tambayar sa lafiya?

Bai bi ta kansu ba,ya cilla ma d'aya daga cikin ma'aikatan nasu da ya k'ware a harkar tuk'i makullin motar sa.Fahimtar mai hakan ke nufi ne ya sashi take masa ba ya da sassarfa shi ma inda ya shiga driver seat, Musty kuma ya shiga baya tare da Zulaykha.

Figar motar ya yi kamar za ya tashi sama,inda ya wuce babban asibitin dake cikin birnin Abuja.
Da gaggawa kuwa aka an she su zuwa emergency aka shige da ita,wacce ko motsin ba ta yi har zuwa wannan lokacin.

Lambar Abba ya danna ma kira a lokacin da yake ta faman kai kawo bakin dakin da aka shiga da Zulaykha likitoci kusan guda hud'u sun dakufa a kanta sabida ceto rayuwarta.
Har wayar ta gama ringing Abba bai daga ba,wanda hakan ya sa Musty jan dogon tsaki yana ganin kamar da gangan Abbah ya k'i d'auka saboda ba Zulaykha ba ce ta kira sa. Bai hak'ura ba ya sake danna masa wani kiran,sai da ya masa kira kusan na shida kamin Abba ya d'auki a wayar a hasale cikin fada fada yace, "Haba Mustapha! Idan ka kira ni sau d'aya ko biyu ka ji ban d'auka ba ai ka yi tunanin wani abu ne mai mahimmanci ya rik'e ni,tunda dai ka san haka kawai da gangan ba zan k'i dauk'ar wayar ka ba ko??"
Abba ya fad'a a lokacin da ya fito daga cikin hole din da suke meeting bacin rai ya d'auki escuse.

Cike da 'bacin rai shi Mustyn ya ce "To shi kenan ka yi hak'uri!" Kit ya kashe wayar sa ba tare da ya ce ma Abba ga abin da ya faru ba ya fice daga asibitin bacin ya bama wanda ya kawo su kudin da zai hau a-daidaita-sahu,saboda shi gida ya nufa yanzu.

Shi kuwa Kabeer ganin abin da ya faru ne ya sa shi tsayawa a asibitin,ya shaida ma wata nurse kan bari ya je ya sanar ma mahaifinta halin da ake ciki,ta shaida masa babu damuwa.

A-dai-daita-sahu ya hau zuwa babban ma'aikatar Abba, dama yasani sabida dadewar da yayi yana aiki a k'ark'ashin sa. Bai samu ganin Abba ba saboda suna meeting da za su fito nan da mintuna 30,wanda hakan ya sa shi zama daga inda yake da yakinin zai ga fitowar Abban ba tare da ya sha wahala ba.

Bayan 32mins kuwa sai ga mutane nan sun fara fitowa daga hole din manyan mutane ne masu-fada-a-aji a fad'in kasar tamu,wanda kallo d'aya idan mutum ya yi masu tabbas zai gano tsagwaron wadata da ke tattare da su. Abba ya gano tare da wani babban amininsa sun fito a jere suna sake tattaunawa tsakanin su dangane da meeting d'in da suka yi a kan sake ha'bbaka kasuwancinsu.

"Barkanku da war haka yalla'bai fatan kun fito lafiya?" Kabeer ya fada a lokacin da ya iso zuwa inda su Abba d'in suke.
"Lafiya k'alau Kabeeru lafiya na ganka anan kuwa??" Abba ya fad'a a lokacin da yake sa'bar babbar rigar sa.
"A gaskiya ba lafiya ba yalla'bai! Domin kuwa zuwa na yi na shaida maka madam Zulaykha a halin yanzu tana asibiti rai a hannun Allah! Wanda oga Mustapha ya kira ka d'azu zai shaida maka kuma ban san dalilinsa na fasa fad'a maka ba"

Ai a wani irin firgice Abba ya ce "Kana nufin mamana ce ke asibiti..."K'warai ma kuwa yalla'bai!" Kabeer ya sake jadda ma Abba,had'i da fad'a masa asibitin da suka kai ta tare da Musty d'in.

***Kwantar da kanta ta yi kan damtsen hannun sa bacin ya lallashi sahibar tasa,tana sharar kwallar da ta kasa tsayar mata ta ce. "Haka nan kawai ka je ka had'a ni da Babi,wai na ce a mana aure,kuma bacin kai ka fara jangwalo mana zancen."

Husnah ta fad'a fuskarta cike da jin haushin cema Babi wai ita ta ce tana son a masu aure,bacin kuma shi ne ya matsa mata da zancen tunda ta farka daga gajeriyar jinyar da ta yo na watanni biyu ,wanda hakan ya sa ta ce masa shi mai zai hana ya fad'a ma su Babi din da bakin sa,amma ji yanzu ya je ya kunya ta ta a wajen Babi.

"To wai ni ma ba na ce ki yi hak'uri ba!!" Yaya ya fad'a 'bacin ya shagwabe fuska kamar wani yaron goye,wanda ya san hakan sosai yake sake narkar da zuciyar Husnah kan soyayyar sa,domin kuwa ita irin matan nanne mai son namiji shagwa'ba'b'be da zai zam to tamkar dan goye a gabanta.

Turo siraran la'b'banta ta yi gaba cike da sanyin murya ta ce "to na ce ai ni ma ya wuce ko Yaya?"  Tsadadden murmushi ya sakar mata da kaf cikin gidansu babu mai samun kwatan kwacin sa had'i da manna mata kyakkyawar sumba akan goshinta.

Nan take kuwa ta ji wani abu kamar almara ya tsarga mata tun daga tsakiyar kanta,har zuwa babbar yatsarta na k'afafunta,sake lumshe idanunta ta yi had'i da sake narke masa a jikinsa saboda jin dad'in yanayin da suke ciki a yanzu.

A 'bangaren Yaya kuwa Allah ne kad'ai yasan irin yanayin da ya afka a dai-dai wannan lokacin,amma kuma saboda jarumta irin tasa dole ya yi controlling na kansa,had'i da lalla'ba ta tare da gaya mata tsadaddun kalamai masu sanyaya zuciya kamin ta shige cikin gida,tana mai sake jin k'aunar yayan nata na yawo a sassan jikinta.

A lokacin k'arfe 1 ta yi,da sallama ta shiga dakin Amma ,inda ta tarda mahaifiyar ta-ta da girma ya fara kamata zaune kan abin salla hannunta rike da carbi,tana jiran lokaci ya ida cika ta gabatar da sallar azahar.

"Sannu da hutawa Ummana!"  Husnah ta fad'a a lokacin da take zuge zip na doguwar rigar atamfar da ke jikin ta,gyad'a mata kai Amma ta yi alamun ta ansa mata ba tare da ta mata magana ba,sallamar da ta jiyo daga tsakar gida ne ya shaida mata da dawowar su *Mima* daga makaranta.

Ba ta ma yi gigin tarbar su ba,bacin ta ansa masu sallamar da suka yi a lokacin da ta fito daga d'aki,jikin ta sanye da zanin wankan ta,inda ta d'auro hijjap babba akai,wanda ya saukar mata har k'asa.

Wani irin kallon uku-saura-kwata Hidaya da Hamad* suka yi ma d'akin Amma had'i da jan doguwar tsaki suka fada d'akin da ke mak'waftaka da na Amman,bakinsu d'auke da sallama.

"Allah ya shirye ku to."  Husnah ta fad'a a lokacin da take dosar hanyar bandakin nasu da ke tsakar gida,Mima da ke k'ok'arin shiga d'akin da su Hamad suka shiga ne ta dakata had'i da daga murya ta yadda Husnah za ta jiyo ta ta ce "Shiriya ta addinin musulunci idan ya kai har cikin zuciyarki."

Girgiza kai kawai Husnah ta yi ba tare da ta ba ma Mima ansa ba,had'i da shigewa band'akin bakinta d'auke addu'ar shiga.

A lokacin da ta shiga ne kuma *Waleed* ya shigo gidan shi ma,jikin sa sanye da uniform irin nasu Mima,Hidaya da kuma Hamad,alamun daga makaranta suka taso,inda shi kuma ya shige d'akin da Husnah ta fito bakinsa d'auke da sallama.

******** "Ko kai fa dan Allah! A ce mutum kullum tuwon dawa tuwon masara babu wani canji saboda a kan mu farau talauci? Ai idan kana kawo man ire-irensu shinkafa tare dasu macaroni Allah ba za a na jin kanmu da kai ba a mak'ota,ni ma in takaice maka ma ka jima ba ka yi masifar birge ni irin na yau ba *Yayana* "

Alina ne ke wannan maganar a lokacin da take ta faman aika shinkafa da miya a bakinta da ya ji nama akai,wanda saida Waali ya ciyo bashi ya kawo mata duk wasu cefane ta dafa shinkafa da miyar kamin ya samu kansa,shi ne take ta faman yi masa wannan Sambatun,shi kuma ba ma sauraran ta yake ba,tunaninsa kwacokan ya tattara ne izuwa tunanin hanyar da zai biyo wajen ganin ya biya Idi mai shago kud'in sa har naira dubu biyu da ya ranta,duk dan ya biya ma gimbiyar tasa buk'atarta na cin shinkafa da jar miya.

Ba su san daga inda ta shigo ba,basu ji motsin ta ba,sai ji kawai suka yi Iyami ta kwad'a ma Alina wani irin gigitaccen mari da ya sa ta fasa wani irin k'ara saboda babu karya marin ba k'aramin shigarta ya yi ba. Cike da tsananin bacin rai Iyami ta bud'i baki ta ce.

_comment and share plss_

RIJIYA TA BA DA RUWA???? Where stories live. Discover now