Part 11

80 9 0
                                    

*RIJIYA TA BADA RUWA...!!*

*©️OUM MUMTAZ✍️*
    
                              

           *charpter 11*

******** Tin daga wannan ranar sai ya zamana Zulykha kan tunowa da mahaifiyarta akai-akai,wanda idan ta kwanta bacci har mafarki take da ida,tana fadi mata kalmomi na zalla da kuma madarar kaunar da take mata,had'i da kewarta data lullube ta.
Amman koda wasa bata sake tinkarar Abbah da zancen ba,sabida nuna bacin ransa da yakeyi karara a dik lokacin da tayi gigin sanar masa wani abinda ya shafi mahaifiyar ta da ko sanin ta ba tayi ba.

A fannin tafiya wurin aiki kuma yanzu ma'aikatar Abbah take tafiya tare dashi bisa ga umarnin sa,wanda ya kasance nata kuwa sai ya daura Oga Musty akai,inda yanzu komai da zai shiga ya fita cikin kamfanin sai da saka hannun sa! Amma kuma umarni bada ga wurin sa yake ba,daga sama ne,wato wajen mai asalin kamfanin Zulaykha!

Inda kuma abubuwa suka sake tab'arb'arewa,kullum cikin zagi had'i da tsinuwa Ummi da mahaifin ta ke kwasa a wajen ma'aikatan,kan wai sun tauye masu hakkin su,basu biyan su albashin su yadda ya kamata! Sannan har wasu daga cikin su suka bar zuwa wajen aikin tare da fadin Allah ya isar masu kan dik wasu kudaden su da aka tauye masu ba tare da an biya su ba!

Shi kuwa Musty da Mamy ko a kwalar rigar su,duniya sabuwa ta sake bude masu ne sabida wannan damar da aka basu! Haka nan a fannin ma'aikatan cikin gida ma,wasu da suka ga basu iyawa da wannan cutar sai suka sallami kansu tare da fadin a lahira za'a biya su hak'kin su da akayi ta faman tauye masu na tsawon watanni wajen shida.
inda wasun su kuwa,suka ce babu inda zasuje,sai sunga abinda ya ture ma buzu nadi cikin wannan gidan!

Dik wannan budirin da akeyi kuwa,sam Abbah da ita Zulaykha d'in basu da labari! Basu ma san maike tafiya ba,sabida irin sakacin da sukayi na yadda da mutunen da bai cancanta su basu dikkan yardar su ba!
wannan kenan.

******** "Oyoyo takwara na sannun ku da zuwa! Sannu da zuwa!" Wani babban mutum ne da a kalla zai kai irin shekaru tamanin a duniya ke wannan maganar! Wanda t'sufa k'arara ta bayyana tattare dashi sabida yadda shekarun sa suka ja!

Dikda kuwa tsufar data riske sa hakan bai hana shi mikewa daga zaunen da yake ba,hannun sa rike da sandar sa,dake taimakon sa wajen tafiya ba tare da gargada ba, da sassarfa kuwa Yaya ya karaso zuwa inda wannan tsohon yake,ya basa kyakkyawar runguma yana fadin "T'soho na mai ran karfe gani nan yi a hankali kar garin murna na ganin takwara yasa ka karashe kakkarya mana guntun kafafun naka."

Wannan maganar da yayi ne yasa Babi dake gefe yana kallon dan uwan nasa da kuma dan nasa dake kaunar junan su sosai sakin dariya, shima kuwa tsohon nan sake rungume d'an gidan k'anin nasa yayi,yana fadin, "ai kuwa dai dan albarka! Kamani mu karashe wurin zamana sabida k'afafun nawa sun fara matsamin."

Tare da Babi suka kama *Yaya babba* zuwa kan wani cushion din da a kullum zaka same shi zaune yana jan carbin sa! Suna yi masa sannu,Babi ya daura da fadin, "ai da baka tashi ba Yaya sabida matsalar nan ta k'afar ka."

"Kayya! Gwanda ka barni na taka da kafafu na *Amadu* ! Sabida ni kaina nafi son ina take su, suma suna jin irin radadin da suke k'unsa man!Balle ma kuma kaima kasan idan ba takwara bane yazo ai ban mikewa daga inda nake ko kuwa?"

Girgiza kai Babi yayi,ba tare da ya bama yayan nasa ansa ba yace, "mun sameku lafiya? yaya iyalin?"

"lafiyan su qlaou alhamdulillah,ina su *Kausara* sarkin rikon tsiya tare dasu *Halimatu* da kuma sauran yaran?"

"Dik suna lafiya Yaya, kuma sunce a mika masu gaisuwa!" Fadar Babi cike da girmamawa. Wani irin dariya Yaya Babba ya sake kamin yace, "Nasan dai Kausara ba za ta ce a gaida ni ba,sai dai ita Halimatun,bana raba d'ayan biyu"

A tare Babi da Yaya karami suka kwashe da dariya sabida jin abinda Yaya Babba ya fada,wanda kuma gaskiyar ya fada,da ace a baya ne idan Ammi tasan wajen sa za'a zo harda guzirin su goro zata bayar a kawo masa bama gaisuwa kawai ba,amma sanadi daya zo ya ratsa sai kuma gaisuwar ma ta daina aiko masa!

Sosai suka gaisa abin su,cike da tsantsar kauna da kuma fahimtar juna dake tsakanin su! *Hajjo ce* ta shiga parlon mai gidan nata,itama dai tana dingisa kafafu sabida matsalar tasu kusan iri d'aya ne tare da mai gidan nata! itama ma kam ta tsufa sosai,sabida za ta kai shekaru 70 a duniya.

"Oyoyo mai gida na,kana ina ne." Hajjo take fada a lokacin da take idasa shigowa cikin parlon,ai kuwa babu shiri ya mike daga zaunen da yake da sassarfa ya karasa inda take yana sakin dariyar shekiyanci yace "gani nan kuwa my wife a kusa dake"

Tare da taimakon sa suka karasa zuwa inda su Babi suke,ya zaunar da ita a gefen Yaya Babba,sannan shima ya zauna a wajen kafafun ta yana mata matsar kafa,Babi kuma yana daga wajen kafar Yaya!
Sabuwar gaisuwa suka sake yi inda take tambayar su wajen mutan gida,suka shaida masu kowa lafiya.

Gyara zama Babi yayi,ya kalli Yaya yace "ka bamu wuri ko mallam?" Ba tare daya musa ba kuwa ya mike ya fice daga parlon yana shafa sumar kansa dake kwance lup-lup gwanin birgewa,ba kamar idan ya tashi hargitsa su ba.

Bai tsaya daga bakin kofa ba ya kusa kansa zuwa cikin gidan dake da girma sosai, inda ya shiga parlon da yake jiyo hayaniya bakin sa dauke da sallama.

Wata matace zaune kan kujera da zata kai kimanin 35yrs,tare da wani magidancin mutum da zai iya kaiwa 55 da kuma wasu yara guda biyu mace dana miji da suka cika parlon da hayaniya daga can gefe suna wasan su.

Jin muryar da suka jiyo ne yasa su dakatawa daga hayaniyar da suke dik suka shiga taitayin su sabida sanin halin Yaya da rashin son hayaniya.

Wannan magidancin mai suna *Abubakar da suke kiransa da Dad* ne ya mike hadi da bude ma Yaya hannayen sa alamun yazo gare sa,fuskarsa shimfide da zallar murmushi!

kamar wani karamin yaro haka ya karaso zuwa inda yake ya fada masa jikin sa, bubbuga bayan sa Dad yayi,hadi da fadin "sannu da zuwa Baban mu! Fatan kazo lafiya?"

Sai da suka zauna kan kujerar sosai kamin yace, "lafiya kalau Dad,ina su Mom tare dasu Hauwa'u sarkin surutu??"

Dariya Dad yayi yace, "Dik suna nan lafiya kalau,amma fa suna fushi da kai sabida gudun su da kayi baka zuwar masu ziyara."

Shima dariyar ya sake kamar bashi ba yace, "su Hauwa'u Jiddah manyan mata,ina nan zuwa kace mata karsu damu,insha Allah zanzo kwanan nan!"

"Ina wuni uncle yaya?" wayannan yaran suka hada baki wajen gaisar da Yaya, sai da ya wani dan tsuke face wai shi gudun raini yace "lafiya"

Kallon gefen da *khadeeja* ke zaune yayi,inda yaci karo da fuskarta,tana wurga masa harara kamar idanunta zasu zazzago k'asa.

"Malama Dije wannan kallon fa kamar zaki cinye ni?" Ya fada yana mai dage mata gira guda,wanda hakan yasa ta daukar pillow din dake gefenta ta jefa masa,aikuwa babu shiri ya goce yana mai sakin dariya kamar bashi ba!

"Dad ka jimin wannan matar da rashin kunya ban shiga shirginta ba,ita tana kokarin shiga tawa ko??" girgiza kai kawai Dad yayi cikin murmushi yace "kunfi kusa ai Yaya"

Turo baki gama yayi ya tashi daga gefen Dad zuwa inda anty (khadeeja) take,ya zauna a gefenta yace "Mutuniyas ya ake ciki ne,naga sai faman harara ta kike tinda na shigo?"

Tab'e baki Anty tayi cikin sanyin murya tace, "ba dole na harare ka ba,daga shigowan ka har ka kora man yara waje sabida cin zalin su da kakeyi,idan sun ganka kamar sunga dodo."

Wanda shi sai a lokacin ma ya lura ashe har yaran sun bama wandon su iska, sai kuma yaji babu dadi har cikin zuciyarsa,amma sai ya waske kawai yace "To dama so kike na sakarma yarana fuska su rainani?"

Rank'washi ta sakar masa akai tace "Dan baka son raini sai kuma akace ka zamar masu dodo!"

Tab'e bakin sa yayi yace "kyadai ji dashi ai,niba wannan ne ya kawo ni ba! ina wuni Anty?"

Sai a lokacin ta saki fuska sabida jin ance mata Anty,kuma ba kowa ne ya fadi hakan ba sai Yaya tace "lafiya kalau kanina! Yasu Ammi da sauran mutanen gida?"

Aikuwa take Yaya da Dad suka fashe da dariya sabida yadda take wani murmushin son girma! Bama idan tana tare da yaya! Wanda gani take kamar ta basa wasu shekaru masu yawa,nan kuwa shekara guda d'aya ne tal ta basa,tana da 35yr,yana da 34!

*vote*
*comment*
*share*
  
*OUM MUMTAZ✍🏿*

RIJIYA TA BA DA RUWA???? Waar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu