Part 5

110 8 0
                                    

*RIJIYA TA BA DA RUWA*      

           *charpter 5*

******** Washe gari.
Cike da tsantsar kasalar da ta rufe ta a daren jiya ta zuro kyawawan k'afafunta daga kan gadon,bacin ta tsurama agogon da ke manne a d'akin nata ido d'aya nuna mata k'arfe shida har da rabi,ga shi kuma ba ta yi sallar ta asuba ba,saboda makarar da ta yi.

A dan gaggauce ta ida mik'ewa kan k'afafunta zuwa cikin toilet,brush ta fara yi had'i da d'auro alwala ta zo ta gabatar da sallar ta raka'a biyu,ba ta tsaya yin doguwar addu'a ba ta mik'e had'i da tube kayan jikinta tas,ta d'auro wani ficicin towel ta shiga wankan da ya dauke ta tsawon 30mins.

Zama ta yi a bakin mirrow na d'akin da ke shak'e da kayayyakin ta na shafe-shafenta,sai da ta kammala kuwa tsaf,kamin ta gyara gashin kanta had'i da sake tifke shi wuri guda,wata doguwar riga ta atamfa ta zak'ulo daga cikin kayanta,sosai kuwa kayan ya zauna mata a jikinta ya yi das,daga sama ya kame ta,sannan kuma ta k'asa ya bage wanda aka fi sani da A shape.

In dai ta fannin d'aurin d'ankwali ne kam ba daga baya ba,nan da nan ta nad'a d'aurin ta mai kyawun gaske kamar irin na saya a kasuwa.
Wayoyinta tare da kwamutsan tafiya office ta d'akko su baki daya bayan ta saka wani takalmin ta na fashion mai dan tudu sosai take bulbula k'amshin turaren ta fuskar ta na ta faman shek'i duk da babu wani kwalliya idan aka d'auke powder,da kuma lipsglo.

Ta tar da Abba da Mami tare da Musty zaune kan dining suna breakfast,ko wannen su kuwa sai zuba k'amshi yake alamun su ma sun fito cikin shirin tafiya wajen aikinsu ne.

Side hug ta ba ma Abbanta 'bacin ta gaishe sa,kamin ta yi ma kanta mazauni akan kujerar da ke gefen sa ta had'a ma kanta tea a lokacin da take gaisar da Mamy tare da Musty.

"Ai na d'auka ba da wuri yau za ki fito ba Mamana" Abba ya fad'a a lokacin da yake kur'bar tea d'in da ke hannun sa yana sakar mata murmushi,ita ma murmushin ta mayar masa da martani a lokacin da take danna d'ankali a karamin bakin ta ta ce "A kwai wani abin da zan dubo ne yau ya sa zan shiga tin da wuri."

Had'a ido Mamy da Musty suka yi, a zuciyarsu,suna tunanin shin mai zai sa ta je wajen aiki? Duk da da ma sun san ba ta cika yin latti ba saboda tare suke tafiya kusan koda yaushe da Abbanta.

Sun kammala cin abincin nasu tsaf,ba tare da ko wannensu ya sake magana ba,Musty ne ya fara wuce wa wajen aikin bayan ya masu sallama had'i da ce ma Ummi "Sai kin iso"

Har bakin mota Mamy ta masu rakiya hannun ta rike da brief case na Abba,daya daga cikin mutanen daya dauka suke tsaronsa da kuma gidan nasa yana biyan su albashi dik karshen wata ya bud'e masu k'ofa.

Gidan baya suka shiga,sannan driver ya fice daga gidan tare da rakiyar motoci guda biyu masu d'auke da karfafan maza hannayen su kuwa rik'e take da bindiga,sai kuma a can baya d'aya daga cikin su ne ya biyo bayansu da motar Ummi saboda ba ta jiran Abba a lokacin dawowa.

Har cikin ma'aikatar tata Abba suka shiga da ita,sai mik'a masu gaisuwa ake cike da girmamawa,amma kuma fa a zuciya ban da tsine masu babu abin da suke yi saboda gani suke Abba ne ke d'aure ma Ummi gindi har take tafka masu rashin adalci. Domin kuwa albashinsu su ma sosai ake rage masu a wannan ma'aikatar akan wai za a biya su daga baya,ga shi kuma yawancinsu da wannan aikin suka dogara. Wanda kuma da yawa daga cikin su su ma sun ci alwashin ana biyan su kudin su sun bar aiki a wannan campanyn,kowa ya kama gabansa domin kuwa ba su iya zama inda babu cigaba.

Musty ne ya k'araso inda suke a matsayin sa na p a nata ya k'arbi abubuwan hannun ta ya wuce mata da su office,ita ma ta bi bayansa bacin sun yi sallama da Abba da take jin kamar wanda zai mata k'ololuwar nisa saboda shak'uwar su.

"ina so ka kawo man dik wasu information din kudin dake fita da shiga a asusun wannan campanyn." Zulaykha ta fad'a ma Musty da ke tsaye daga can gefe kad'an. "Ok" Musty ya ansa mata kamin ya sa kai ya fice.

Cikin abin da bai gaza mintuna goma sha biyar ba kuwa ya kawo mata duk wasu abubuwan da ya kamata,kuma ga shi nan komai dai-dai ne yadda ya kamata babu matsala ta ko wanne fanni.Wasu cike-cikenta ta yi akan wani file kamin ta mik'a masa ta d'aura da fadin "Ga shi nan,ko wanne ma'aikaci na k'ara masa albashin sa da kud'i naira dubu goma,sai ka had'a meeting ka shaida masu kamar yadda ka saba saboda ni ka san ba zan iya halartar irin wannan wuraren ba saboda ban son hayaniya! Kai kuma na k'ara maka naira dubu ashirin a kan naka."

Wani irin farin ciki ne ya mamaye zuciyar Musty,wanda har ma ya gaza 'boyuwa bisa ga kyakkyawar fuskarsa,yana zuba mata godiya kamar ya ari baki,nan ko farin cikin nasa da biyu ne.

Sai da ya fice daga office d'in kamin ta sauke ajiyar zuciya,tana mai imagining yadda ma'aikatan za su yi farin-ciki idan suka ji wannan batu na k'arin dubu goma-goma akan albashinsu.

Wayar ta da ke cikin jika ta d'auko,had'i da unlock na wayar ta shiga wajen gallery,Hoton Zulaym Ahmad Shuwa da jiya ta d'auka a insta ta tsura ma kyawawan lips nasa idanu tana mai jin wani irin yanayi mara misaltuwa na yawo a jikinta.

********Baban wali shi ne babba,sai kuma mai bi masa wato mahaifin Alina,inda suke zaman lafiya sosai da iyalan su,sannan kuma Wali da Alina su kad'ai iyayen nasu suka haifa,wanda hakan ya sa aka d'ai bi gatan duniya suka zu'ba masu duk da kasancewar su din ba wasu masu arzik'i ba ne na a-zo-a-gani amma Alhamdulillah tunda suna da na rufin asiri,domin kuwa Wali ma ya yi karatunsa a jami'ar Maiduguri fannin business,inda ita kuma Alina ta tsaya a matakin diphloma a Ramad da ke cikin Maiduguri.

Soyayya ce sosai tsakanin Alina da Waali tin suna kanana,wanda da suka girma sai abin ya sake kankama ya rikide daga soyayya ta 'yan uwan taka zuwa soyayya ta aure. Wanda hakan kuwa sosai ya yi ma iyayen dad'i.

Har ma aka saka lokaci na auren su tare da amincewarsu inda bayan aure a cikin gidan iyayen nasu aka ware masu nasu kewayen a can unguwar Madina,saboda har zuwa wannan lokacin Wali bai samu aikin gomnati ba,amma yana shiga kasuwa tare da iyayensu,wanda hakan ya sa abubuwa na rayuwar yau da kullum kan zo masa cikin sauk'i tare da matarsa,kuma 'yar uwarsa abar k'aunarsa.

The first matsalar da suka fara fuskanta a yanayin zaman takewar su daga Alina ne,domin kuwa ita da ma tun fil'azal irin yan matan nan ne masu matikar son abin duniya da suka d'auke ta da fad'i,wanda dama tun can da halin ta,abin da ya sa bai fito fili ba ne har aka shaida saboda yadda mahaifiyarta ke tsawatar mata ne in ba haka ba da kuwa ta yi ta'bargazarta tun tana budurwa kamin aurensu.

Sosai kuwa hankalin Waali yake tashi idan ta buk'aci abu daga wurin sa ga shi kuma ba shi da halin yi mata,wanda muddin bai yi mata ba a ranar wuni zai yi yana kwasan takaici saboda rashin kunyar da take shuka masa,amma ko daidai da rana d'aya bai ta'ba barin wata k'ofa da iyayen su za su gane ba sabida son da yake mata.

A sanadiyyar 'yan fashin da suka fad'o masu unguwa ne cikin dare suna bin gida-gida hadi da yashe su Allah Ya yi ma mahaifansu mazan cika wa saboda yadda suka ba da k'arfinsu akan k'in yadda a keta ma matansu haddi a gaban idanunsu,wanda hakan ya fusata 'yan bindigar suka sakar masu harbi da a wurin ba su sake motsawa ba sun ansa kira na Ubangiji.

Sun yi kuka iya kuka,tare da addu'ar Allah Ya bi masu hakkin su akan mutanen domin kuwa tuni sun tsere kamin 'yansanda su k'araso unguwar domin kawo masu agajin gaugawa.
Haka nan suka cigaba da kula da iyayen nasu da ke cikin tsananin damuwa dangane da mutuwar iyayen nasu. wanda zuwa wannan lokacin Alina ma ta jinginar da mugun halinta a gefe saboda alhinin rasuwar iyayen,wanda hakan kuwa sosai ya yi ma Waali dad'i.

RIJIYA TA BA DA RUWA???? Where stories live. Discover now