Part 17

68 8 0
                                    

*RIJIYA TA BA DA RUWA...!!*
 

    *©️OUM_MUMTAZ✍️*

           *Charpter 17*

******** Komo wa cikin gida Waali yayi,inda ya zauna bakin katifar tasa,ya bud'e kwanon,d'umame ne na tuwon masara da miyar kuka sai tiriri yake alamun da zafi zafin sa,tas Waali ya cinye babu ko ragi sabida dama akoi kwantacciyar yunwa a jikin sa,inda yasha ruwa yayi ma ubangiji hamdala.

Abubuwan da ya dace ya sake yi wajen mai da komai mahallin sa yayi,inda ya fito daga cikin gidan tsakiyar layi yana ta faman kalle-kalle,kowa sai harkokin sa keyi,wasu kanyin k'us k'us idan sun ga namiji da goyo,kuma bak'on fuskar da basu sani ba suyi wucewar su,idanun sa ne ya sauka akan mutumin da suka jiya zaune daga can k'ark'ashin wata bishiya kan tabarma,sai kuma wannan yaron dake wasan sa daga gefe!

Ajiyar zuciya ya sauke yana mai jin dad'in ganin sa,sabida dama so yake ya sayo dik wasu abubuwan da bashi da su na amfanin yau da gobe da baza'a rasa ba.

Har k'asa ya t'suguna ya kwashi gaisuwa cike da girmamawa gami da mutuntawa,inda Baba ya ansa masa cikin sakin fuska had'i da tambayar sa ya kwanan bak'unta? ?? Gaishe sa wannan yaron yayi yana mai lek'a fuskar Ummi dake bacci bayan mahaifin ta hankali kwance,murmushi yayi cike da jin dad'in ganin yarinya k'arama yace "Kaka kaga wata yarinya mai kyau!"

Dik dariya sukayi,inda daga baya ya kunto masu da Ummi dake ta faman fiddo harshe waje alamun ta farka,addu'a sosai Kaka yayi mata kamin Masta ya leko fuskarta yana tayi mata wasa!

Inda daga k'arshe Waali ya shaida ma Kaka abinda ya fito dashi,wani matashin saurayi Kaka ya had'a su bacin ya karb'i Ummi daga hannun sa idan sun dawo sai ya karbe ta,domin kuwa zata sha wahala ne idan yaje kasuwa da ita yadda take a danye danyen ta,saida ya dama mata madarar ta ya bama Baba kan idan ta fara kuka a bata kamin suka masu sallama suka wuce kasuwa.

Sosai Waali yayi masu sayayya bana wasa ba,aljihun sa kuwa ta girgiza amma hakan ko a kwalar rigar sa,inda ya sayo har irin kayan trader dinnan da suka tashi,kayan wasa da kayan sawa masu sauk'in kud'i dik ya sayo ma abar kaunar tasa,Allah-Allah yake dama suyi su tafi sabida baro y'ar tasa da yayi a wani waje,wanda suka dauki wajen awanni hud'u kamin suka fito daga kasuwar da kaya nik'i-nik'i,shatar mota suka yo har kofar gidan,inda wasu yara dake tare da Masta suka fara shigar masu da kayan cikin gida,Waali bai samu ya gama jere komai ba sai wajajen la'asar,sosai yayi ma wanda ya raka sa godiya had'i da basa d'ari biyu ya huce gajiya,aikuwa mutumin da murnar sa ya wuce gida,domin kuwa a wannan lokacin kudi akoita da guntuwar darajarta kamin ta idasa karyewa.

Gidan Baba d'in da d'azu ya nuna masa kamin su tafi ya dosa da suke makwafta ka,kukan Ummi da yayi masa sannu da zuwa ne tin daga k'ofar gidan ya sa shi shigewa ba tare da na masa izni ba sabida tashin hankali,Baba ya tarda tare da mara kunyar y'ar tasa ta d'azu dik sunbi sun rikice sai faman lallashin ta suke amma yarinya kamar ana sake kunnata,ga Masta shima fuskar sa dik ta nuna irin damuwar da yake ciki sabida kukan da Ummi kanyi.

Basu ji alamun shigowar ba,sai ganin mutum sukayi gaban su kamar wanda aka cillo sa daga sama,wanda hakan ya sa su sakin ajiyar zuciya,bayyi wata wata ba ya karb'i yar tasa a hannun AISATA dake ta faman zagaye da ita,kamar anyi ruwa an d'auke sukaji miki'it babu wannan kukan da Ummi take yi sai faman sakin ajiyar zuciya sabida yadda taci kukan ta.

Rungume y'ar tasa yayi cike da t'sant'sar tausayin ta,inda yayi ma su Kaka godiya gami da wuce wa gidan nasa bacin ya karbi feeder na madaran Ummi!

Wanka ya farayi mata da ruwan d'umi daya d'aura kan risho kamin ya fita,inda ya dama mata kunu mai kyau da ruwan dumi,sosai kuwa yarinya tasha sabida uban yunwar dake dankare cikin ta,domin kuwa dik yadda su Aisata suka so tasha ko kad'an ne fir yarinyar nan taki sai uban kuka kamar wacce ake yankar namar jikin ta.

Cikin k'ank'anin lokaci tayi bacci,inda ya kwantar da ita a cikin nata net d'in bacin ya shirya ta ,sai shima ya shiga wankan ya fito ya saka wasu kayan sa kamin ya tada kabbarar sallah,saida yayi azahar da la'asar tare da magriba kamin ya tashi a wurin.

Taliya dafa dika yayi ma kansa,tas ya koshi abinsa,babu abinda yake buk;ata a lokacin kamar yayi bacci,amma sai ya d'auki y'ar tasa kan kafad'a ya fice da ita zuwa gidan Kaka,saida ya k'wank'wasa k'ofa aka basa izinin shiga kamin ya kutsa kansa da sallama d'auke a bakin sa,sai a lokacin ya kare ma gidan kallo,dake dauk'e da d'akunan bacci guda biyu,sai kuma bayi,inda daga can gefe kad'an kuma akoi wata karamar runfa dake d'auke da murhu guda biyu,sai kuma tukwane da d'an sauran kwanika da baza'a rasa ba.

Har k'asa ya kwashi gaisuwa,inda Aisata da Masta ma suka gaida shi ya ansa masu hadi da sake masu godiya bisa ga kulawar da suka bama y'ar tasa,nan ya shaida ma Kaka batin sayo kayan trader da yayi! Basu dai rabu ba,sai da suka tsaida dik yanda saye da sayar war tasa zata kasance ya wuce gidan sa cike da farin ciki da kuma jin dad'i na sabuwar rayuwar da zai shimfida a inda bai da kowa daga shi sai gudan jinin sa da kaf duniya bai had'a ta da kowa ba.

******** Can cikin bedroom nata Uncle j yayi ma Zulaykha masauk'i bisa ga umarnin Abbah da kwata-kwata bai cikin hayyacin sa,Musty ya k'ira Mamy,wacce ta d'an nuna damuwar ta,inda ta samu towel ta tsoma cikin ruwan dumi ta fara shashshafa ma Zulaykha a fuskar ta bisa ga umarnin uncle j kasancewar sa likita ne mai zaman kansa!

Dik cirko-cirko sukayi cike da damuwar dalilin daya sa Ummi cikin wannan yanayin,bacin kuma lafiya k'alaou suka shiga hole d'in suna walwalar su,saida uncle J yaga ta fara sauk'e numfashi hankali-hankali alamun tayi bacci kamin ya ce abar dumama ta haka nan yayi masu sallama ya wuce Abbah yayi ta masa godiya,inda Jiddah kuwa bata tafi ba a ranar,kwana tayi a gidan bacin ta kira mahaifiyar tata,ta shaida mata Zulaykha bata jin dad'i.

******** An kai amarya gidan ta tin a daren ranar,inda kawaye da ma wasu yan uwa dik sun kwana a gidan kamar yadda al'ada ta tana da,ango kuma da aboka nan sa suka wuce can inda zasu kwana.

Washe gari.

Bayan sallar isha'i akayi rakiyar ango bacin d'an nasiha da kuma addu'oi aka masu sallama aka bar amarya da angon ta da kewa harda guntun kukan ta na gulma irin dai yadda amare keyi kamar basu suka ce suna son auren ba.😏😏

*vote*
*comment*
*share*
  
*OUM MUMTAZ✍🏿*

RIJIYA TA BA DA RUWA???? Where stories live. Discover now