Part 35

77 12 0
                                    

*RIJIYA TA BA DA RUWA...!*

*©️OUM_MUMTAZ*

      
*35*

"A madadin kowa da kowa dake cikin wannan wuri dama wayanda basu halarta ba ina mai baka hakuri akan abinda wannan shashashan yaron ya aikata satin daya wuce ABDU..." YAYA babba ya fadi maganar yana kallon Abbah da kansa ke kasa,sakamakon kunyar surukan taka daya shiga tsakanin su.

Cikin murmushin da bai kai har ciki ba Abbah ya ce,"Babu komai wallahi Baba,na kuma dauki abinda ya aikata ne sakamakon bai cikin hayyacin sa a lokacin sabida mutuwar mata a daidai lokacin da ba'a taba tsammani ba nasan dole sai ya taba sa sosai." Abbah ya fada cikin sanyin murya.

"To Alhamdulillah sai kuma abu na gaba don Allah ina neman Alfarma idan babu damuwa jibi nake son Ita matar tawa ta tare a gidan ta wanda nake da tabbacin hakan shine zai saka masu kusanci a tsakanin su da har zasu fahimci junan su cikin kankanin lokaci batare da anja da nisa ba..."

"Ban ki ta taka ba Baba,amma tinda gashi shi wanda ake maganar tarewa a gidan nasa a tambaye sa idan ya amince banda matsala ko yanzu ne ma..." Abbah dake cike da haushin Yaya ya fadi maganar yana mai sakar ma Zulaym din idanuwansa da yasa shi yin kasa da kansa babu shiri kamar wani munafuki sabida kunyar dattijon daya kama sa sosai ba kadan ba. Inda cikin zuciyar sa kuwa fadi yake ko don yafi cin Uban Ummi da lasisi ai dole zai amince ta tare a gidan nasa idan an tambaye sa sabida ya huce takaicin sa.

Tunanin sa ne ya katse a lokacin da muryar YAYA ya ratsa masa dodon kunnen sa da yake fadin, "To kai kaji dai abinda mahaifin matar taka ya fadi ai ko? Shin ka amince ne ta tare a gidan ka ko kuwa?" Cikin kasa da murya sosai Zulaym dake shafa sumar kansa da kwata-kwata babu kyan gadi sakamakon rashin gyaran da yake fama dashi satinnan yace, "na amince ta tare Yaya" Nan kuwa akayi hamdala sannan BABI yasa Zulaym ya durkusa har kasa gaban kowa da kowa ya baima Abbah da Ummi hakuri akan rashin hankalin da yayi. Hmm dik wannan budirin da akeyi tinda suka shigo parlon kan Ummi ke kife akan cinyar mahaifin ta batare data daga idanuwan ta ba,ballantana taga iya adadin mutanen dake cikin parlon ta nausa duniyar tunani,ga wani irin tafasar zuciya dake riskar ta a dik lokacin da ta tuno cewa wai Husnah ce ta rasu. A yan kwanakin nan har kwanan ta uku a asibiti sakamakon shakar da tasha a hannun Zulaym,wanda hakan yasa ta cin alwashin tabbas saita nuna masa yayi da yar halak. Kamar wacce aka tilasta aka ta daga da fuskar ta da babu ko digon kwalli karaf kuwa idanun ta ya fada cikin na Ammah da tinda aka shigo wajen take son ganin fuskar Ummin amma bata samu dama ba,sabida kanta dake kasa.

Wani irin mugun rawa jikin Ummi ya fara sabida kallon fuskar wannan matar,ga wani irin mikewa da take jin tsikar jikin ta nayi sabida yadda ta kafe ta da idanuwa ko kiftawa batayi. Mikewa Abbah yayi da baison Alina ta nuna tasan shi ma cikin wannan jama'ar sannan ya mikar da Ummi da sam taki yadda ta kalli side din da Ammah din take dikda yadda zuciyarta ke azalzalarta da aikata hakan kamar magnet. Gyara mata hijap nata Abbah yayi cike da tsantsar soyayyar yar tasa ya kalli mutanen dake cikin parlon yace, "To jama'atul musulmin mu zamu wuce gida! Allah ya jikan Asma'au, idan tamu tazo kuma Allah yasa mu cika da imani..." da shike dama dik sun riga da sun gama tattaunawar su sai suma suka masu fatar a sauka lafiya.

Ai kuwa wani irin rikitaccen kara Ammah da saki da mugun gudu zuwa wajen su Abbah da suka kusa ficewa daga babban parlon ta wani irin fisgo Ummi da hannun su ke sarke da Abbah hadi da manna ta a kirjin ta tsam-tsam kamar wacce zata maida ta cikin ciki,tana wani irin kuka mai matikar taba zuciyar mai sauraro hadi da sakin tagwayikan ajiyar zuciya cikin kukan nata sabida yadda taji wani irin feeling mai masifar karfi dangane da yarinyar ko tantama bazatayi ba,ballantana kaffara akan cewa wannan diyarta ce,kodaga yanayin mugun kamar da take da kanwar mahaifiyarta marigayiya Iyami.

Ummi kuwa da bata san a wace duniyar take ciki ba sai tayi lamo a jikin Ammah hadi da lumshe idanun ta,tana saurarar yadda kirjin ta keta faman sama da kasa. Wani irin natsuwa ne ke shiganta from no where da zata iya rantsewa da Allah tinda take bata taba jin makamancin sa ba a dik lokacin data rungumi wani mahaluki idan aka dauke mahaifinta Abbahn ta.

RIJIYA TA BA DA RUWA???? Where stories live. Discover now