NI DA PRINCE 2

8.8K 461 4
                                    

☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄


*NA AYUSHER MOHD*

NO.2⃣

Salmah kam karkashin wata bishiya tasamu tazauna dan tarasa dalili tunda ta taho ake binta da kallo, cikinta taji ya murda tasani yunwace ke damunta hakan yasa tadauko jakarta tabude tashiga irga kudin ciki ~N~350 ne aciki ta ciro dari ta mike tai hanyar shop, har alokacin mutane na binta da kallo cikin rashin damuwa takarasa tare da mikama mai shop din kudi tace abani buns sai dai me? Kafin mai shagon ya amsa taji an wafce kudin ahankali ta juyo dan ganin wannan rainin hankalin wani saurayi tagani cikin mamaki ta dauriya tace malam mekenan? saurayin yace indai kinasan siyan abu anan to lalai ne ki kwabe wannan munafikin abinda kikasa muga mai kika nunama prince har ya tsugunna kusa dake tace me kake nufi da kalamanka? Yace oh kindauka bamusan manufarki ba? Salmah ta runtse ido tadaure ta juya batare da ta amshi kudin ba, jitai an mazan gun sun kwashe mata da dariya, ahankali take naga kafarta dan jin kafar take tamata nauyi.

Sai datai tafiya mai nisa sannan tasamu guri tazauna kwalla ya cika mata ido,
tunda tafara zuwa makarantarnan bata tunanin wani yasanta banda mutanen datake gaisawa dasu yau gashi anjayo mata duk inda ta wuce ana binta da kallo😰hoton kamal tadauko tafada afili yaya kamal kadawo plz😔 jitai ance lalai salmah soyaya har a skul? Tadago danta gane mai muryar tace zee ashe kin shigo, zee tazauna tare da cewa salmah meya hadaku da prince? Tace au kema harkinji? Zee tace hmm ni fa muna zaune munajiran Professor mannir kawai wani ya shigo class da gudu yace yan class kunsan salmah ai kawar zee? Sukace eh mai nikaf yace to tanacan ana show itada prince ya cire mata hijab da nikaf😂 nan yan class sukashiga dariya tundaga nan nafito nemanki banganki ba,
Salma tai murmushin yake tace zee kodai inhakura da makarantarnan? Injira kamal yadawo inmunyi aure sai inkarasa.
Zee tace haba salma akan wani can zaki durkushe rayuwarki? Kinsan prince yakai 2yrs a skul din nan kuwa? Tace haba? Zee tace hmm amma kinsan me? Haryanzu fa a level 200 yake salma cikin mamaki tace haba dai? Baya jaa ne? Zee ta kwashe da dariya tace inafa? Ance blanksheet fa yake submitting😝.

Salma tace blank? To ya akai ya wuce level 100 zee tace ance wai da shugabar makarantar taso tadinga bashi mark sai dai shi dakanshi yace mata bayaso karta karamai haka, salma tace meyasa😳? Zee tace oho ba wanda yasan dalili, tadan tabe baki tace shiyasani zee tace waje iskanci cikin fanko😜nan sukasa dariya.

Salman kam bai dade a skul ba ya wuce yawansa dan dama ba lectures yake shiga ba sai wajen magrib ya shiga gida ya ajiye mota yai bangarensa bayi nata gaisuwa yana isa daki yai wanka yazura doguwar riga yafito tareda bayinsa dake kuladashi yai bangaren fulani zuciyarshi taf take da bakin ciki suna isa harabar gun yacema bayin su jirashi yashiga, ahankali yakarasa kofar dankin bayin dake kula dagun suka budemai yashiga sai dai bakowa a kilisar da fulanin ke zama yai shiru zuciyarshi na bugawa da karfi.

Wata baiwa ce tazo tace tana daki bari insanar mata, yace a'a bari in karasa tace to ranka ya dade, ahankali yakarasa dakin yakai hannu zai kwankwasa yaji maganar Ishaq (yayansa ne agun mahaifinsu) yanacewa yau ma dai kamar kullum salman yawansa yaje, fulanice ta saki dariya tace ka tabbatar dai kana kula da takunsa dukda kaini dan sarki nafarko bai zama lalai ka gaji sarki ba ehe.

Ishaq yace haba ummi yaxakina fadar haka ke kina tunanin wannan shashashan Abba zaiba mulki? Yaranda banda yawo ba abinda yake? Haryanzu yakasa gama karatu? Tai dariya tace kasan sarki na tausayinsa ganin bashida uwa, ishaq yace tab aikin banza kenan to sau nawa yana zuwa gaida sarkin amma baya amsawa?

Ahankali salman yafara yin baya idanshi yakada yayi jaa dakinsa ya koma yai saurin dafa kansa da kirjinsa jiyake kamar zai mutu dasauri ya bude drawer yad'auko magani ya hadiya yashiga karanta *INNALLILAHI WA INA ILAIHI RAJI'UN* ahankali yafara jin nutsuwa tana zuwa mai.

Salmah zaune a tsakar ta zuba tagumi ga kwanukan wanke wanke a gabanta da alama shi takeyi tashiga tunani, abinda salman ya mata take tunani tai ajiyar zuciya aranta tace da yaya kamal nanan munyi auranmu da duk haka bata samen ba jitai an daka mata dundu a baya tadago cikin mamaki goggo tace kinci gidanku, wanke_wanke zakimana ko tunanin wancan dan iskan? Salmah tace goggo wai meyasa kika tsani yaya kamal? Ba dan uwan Abba bane? Tace oho ko dan uwa nane mai yadameni? Kedai kinji asara kannenki duk sunyi aure ke kinfi karfin iyayenki, salma tace nima da yaya kamal nanan ai...jitai an kwabe mata baki goggo tace mara kunyar banza kawai ke baki da aiki sai zancen kamal duk mutanen dasukazo neman auranki kim koresu shima Alhaji ai duk laifinshine aikin banza, tana zuwa nan tai gaba salma tabita da ido itakam bakomai zatajira kamal dinta 😗.

By Ayusher Mohd📚

NI DA PRINCE  Where stories live. Discover now