Ni Da Prince 28

7.1K 368 2
                                    

*NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄


*NA AYUSHER MOHD*

NO.2⃣8⃣

Duk shiru sukai ad'akin ishaq ya mike a zuciye zai fita, salman ya kalleshi yace yaya ishaq sai ina? Ya juyo a zuciye yace duk inda zani sai na sanar dakai? Salman yai murmushi yace maida wukar yaya adawo lafiya, fulani ta cije lebe inama d'anta ne haka? Amma tana bakincikin yanda salman ya ninka d'anta komai.

Salma ce tai kasa dakai tace fulani ayi hakuri abunda yafaru rannan munyi kuskure😞 tafad'a tare dayin kasa dakai, salman ya maka mata harara ta gefen ido amma a bayyane sai yace umma kinji hakuri take badawa bayan ninai laifin, fulanI aranta tace wato kana nufin kai kafi karfin bada hakuri kenan? Salman ya kalleta yasan metake tunani amma a fili yace umma bari mu wuce ina tunanin zamu d'an fita akwai inda zata rakani, yafad'a yana murmushi, sannan ya kalli salma yace muje dear😉 salma ta d'ago aranta tace dear😒? Mikewa tai salman yace umma yau nasanar dake ko? Fulani bakin ciki ne ke neman kasheta amma tad'aure kamar tai kuka ta saki yake tace eh mana, salman ya kalli salma yamata alama dakai muje, salma tafara tafiya jikinta yai sanyi, itakanta tasan bakaken maganganu salman ke fad'a amma ita ta d'auka bakar magana rai abace akeyinta?.

Suna Shiga d'aki takalleshi tace dagaske gun Abba zamu😬? Ya hade rai yace saki nai? Tace mene? Yace hakurin da kika bada mana🙄, saki nai? Tace hm ganinai kamar.....yakatseta karki sake banaso, tace amma ai....yace zaki fara ko? Ke ba'a isa ace kaza kice to bako? Salma ta turo baki tace to, salman ya matso yaja leben ta da karfi, ai kuwa ta fara shure_shure, ya saketa tasa kara tace da zafi fa😢tafad'a cikin shagwaba, salman yai dariya yace in ba zafi mezaisa inja? Tace ni wlh ban yarda ba☹ya juya baya yace shikenan in baki yarda ba sai mufasa zuwa gun Abban, dasauri ta dawo gabanshi tace a'a na yarda sosai ma😬 murmushi yai tare dasa hannu ya dungure mata kai yace sai ki fito.

Ya juya yai waje, tsayuwa tai a gun tare da daga gun da zuciyarta take, jitai tana harbawa tacw wayyo ni! Yaya ka....dasauri ta toshe bakinta tare da girgiza kai, fuskarta tad'an gyara ta yafa mayafi ta fito.

A mota tasami salman tashiga tare da murmushi salman ya hade rai yace da ai nafara tunanin fasa zuwa, dasauri takalleshi tace na'am😱? Yatada mota tare da cewa ina nufin da baki fito ba nan da 5min😏, salma tace ahhh ya fara tafiya, tace hmm yauwa kaga kud'in rannan a jakata sam namanta ban baka ba, tafad'a tana mikowa, hannu yasa ya dunkule hannunta da kud'in yace keep it, salma kam tai sororo jinyanda ya rike hannunta.

Shikanshi wani abune ke ratsashi da sauri ya saketa, sai dai salma tana rike da kud'in kuma bata d'auke hannunta ba, akasarima batasan yad'auke hannunsa ba, juyawa yai yakalleta a yanda ya barta, hanni yasa a kafadarta yace menene? Dasauri tai firgigit tadaure tace bakomai tunanin Abba nake.

Salman yace karki damu zai warke, kallanshi tai tad'an karkatar dakai aranta tace yaxanyi? In nikad'ai nafara sansa? Tasani sarai ita bata iya so ba.

A wani karamin mall ya tsaya ya fita, yana fita salma taji karar waya, wayarta ta duba taga ba ita bace ahankali ta kalli wayar salman, tace oh ankirashi gashi bayannan, tafad'a tare da kallan wayar, number ce, harta kai hannunta zata d'aga tai saurin girgiza kai tace ba ruwana😕.

Salman na dawowa tace mai ankiraka yace wa? Tace number, yace ok, yace bazaka kiraba? Ya kalleta yace 4get, ta tabe baki tace nima haka zai dingamin in na kira baya kusa? Batasan afili tafad'a ba jitai yace in kin kira sau d'aya bazan kiraki ba amma in sau uku kika kira bana kusa I promise to call u back.

Haushi ya kamata wato sai ma tayi sau uku?tace au in sau d'aya nakira bazaka kira ba? Yace yes saboda inkika kira sau d'aya ai abun ba important bane kenan, salma tadafa kanta aranta tace na shiga uku ni salma🤔.

Asibiti suka sauka ahankali suka karasa d'akin Abba, kamal na ganinta yashiga washe baki, sai dai yau salma murmushi kawai tamai tad'auke idanunta, sun gaisa da Abba, nan Abba yasakema salman godiya yace kaganmu ashirye sallama za'a bamu yanzu, salman yace Abba baka gama warkewa ba wacce sallama? Abba yace kayya ai nikam yau gida zani, goggo tace ai fa yadage sai hakuri, salman yace shikenan bari in anso sallamar sai in kaiku gida.

Sunzo shiga mota salman ya kalli kamal yace kai sai ka biyomin ko a mashin ne dan gun bazai ishemu ba ko? Kamal ya harareshi yace sai ka fad'a😠nan suka shiga mota sukai gida.

Tunda suka iso unguwar salman ke kallan unguwar tausayi duk ya kamashi, yanzu anan salma take? Amma ya hanata karatu a skul? Dasuka iso gidan jikinsa duk yai sanyi ya daure ya ajiyesu ya kalli salma yace ana la'asar zanzo tai murmushi tace to zan kula da wayata😊 yanda inka taho sai ka kirani yace to, harta juya ta dawo tace sai na ganka😊 yace hmm sai kin ganni😊 wani murmushi sukama juna yad'ago zaiyi magana aka sake kiranshi, tace bye tare dayin ciki shikuma yabita da kallo tare da d'aga wayar yasa a kunne.

Jiyai ance yayana is me? Cikin kid'ima da rudewa yace what? Aka kara cewa haba yayana ai sai in fishi in kace baka ganeni ba, Ur Farha ce, salman yace what? Farha? Tai murmushi tace naji kunya yayana dabaka d'au muryata ba☹anyway gani a airport kainake jira😊 tana gama fad'ar haka ta katse layin.

NI DA PRINCE  Where stories live. Discover now