Ni da Prince 15

5.7K 366 4
                                    

NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄


*NA AYUSHER MOHD*

NO.1⃣5⃣

Salma kam tsaye tai a band'aki kara karema bandaki kallo tai, aranta tace band'aki shine akama wannan kwalliyar oh, sai kuma tai tsaki tace wlh nikam an cuceni mezanyi da salman?fuskarta ta shiga wankewa a sink dan bazata iya wanka a gidan da batasan kanshi ba, tad'an dade kafin ta fito, salman tagani kwance ya rungume pillow yana narkar bacci...

Haushi ya isheta ganin ko bargon baiyi karar ajiyewa ba takai hannu kamar zata dakeshi, tad'an daki iska sannan tace d'an rainin wayau ni da wannan ai gwara abarni ko shekara 10 zanyi a barni na jira kamal ko a had'ani da d'an garuwa😏.

Ta koma kan sallaya ta tada sallah, ta dade tana nafila sannan ta d'aga hannu tashiga jero adduo'I tanayi tana hawaye, sai wajen 2 sannan ta mike dan kashe wutar dakin, ta kashe ta juya zata zauna taji ance I can't sleep while light is off, dariya ma abin yabata a hankali tace dayake nepar a gidanku take😏 salman yace I can hear u, kuma ki kunnan wuta,tace gaskiya ni ban iya bacci da haske ba, yace wannan kuma matsalarki ne.

Salman yace ki kunna min wuta ko? Dasauri ta matsa daga gun takaraso inda yake ta kunna yar karamar fitila ta dum light dakd side bed dinshi, zaiyi magana tai saurin juyawa zata koma kan sallayarta hijab dinta ya kamo ta baya yace ke! Ta juyo tace waye ke? Yace ke wannan hasken yamin kad'an,nida d'akina fa baki isa ki takuran ba😠 ta fizge hijab dinta tace sai kai hakuri da wannan inba hakaba ka bani makulli na fita🤔 tana kainan ta karasa kan sallaya ya kalleta taredayin kwafa.

Itakam salma nan ta kwanta tare da takure jikinta, kan kaceme? Bacci yayi awon gaba da ita.

Kamal kam tunda ya tsugunna a wajen nan bai tashi ba mahaifinsa yace kar wanda ya kulashi nan kowa ya watse aka barshi, sai wajen karfe 10 Abba yakasa jurewa yazo dakanshi ya d'agashi suka shiga ciki, sai dai kamal sam yakasa ko magana kawai idansa zaka kalla kasan yana cikin matsanancin bakin ciki.

Da Asuba karfe 4:30am salman ya tashi,ya sauko yaga yanda salma ta takure dariya tabashi yace kad'an kika gani tunda ke kika ce ni kikeso, harzai samata bargonshi sai kuma yafasa yai toilet.
Alwala yayi sannan ya fita, salma kam gajuya da rashin baccin wuri ga jikinta ba karfi saboda zazzaben datai agida yasa bacci mai karfi yai gaba da ita, sam bata farka ba lokacin sallah.

Salman na dawowa ya kalleta tananan ayarda ya barta yai tsaki yace a waje kamar ustaziyar gaske amma ace mutum ko sallar asuba bai farkawa? Daga gani ba yau tasaba makara ba🤔 karasa wa yai inda take ya d'au sandar dake ajiye a d'akin yad'an zungureta dashi, cikin bacci tace Abba kafito? Salman ya tabe baki sannan ya kara zungura mata da karfi, cikin razana ta mike, sai dai me? Saman tagani ya harde hannunsa biyu.
Haushi ya isheta tace wani sabon cin mutunci ne wannan? Bai mata magana ba ya juya ya hau kan gado takara cewa haka ake tashin mutum daga bacci?yace ke ni da sanyin safiyarnan bansan magana meye dan an zungureki?tace what? Kwanciya yai tare da juya mata baya, tai toilet batare data mai magana ba.

Alwala tai sannan ta fito ta tada sallah, bayan ta idar ne ta kwanta wani baccin ne yasake d'auketa.

Wajen karfe 9 sukaji anan knocking, salma ta mike da sauri ta bude kofar, wata baiwa ce tace ranki ya dade dafatan kin tashi lafiya? Salma tace lafiya, baiwar tace sunana Hanne baiwarki, salma tace baiwa? Tace eh zuwa nai nasanar dake karfe 10 zakuje gaida sarki, sannan karfe 12 baki zasu fara yimuku sallama.
Salma tace toh😳 hanne takara kasa dakai tace karfe 9:30 zan kawo abinci, salma tace hmm to, nan hanne ta juya salma takoma ciki sannan tace nizan iya zuwa gun sarki kuwa? Tai maganar a fili, salman yace I can hear u, salma tad'an murguda baki tace mutum sai kunne kamar maciji? Yace inajinki fa? Tace oh ni😱 ta shiga duba drawer ko zataga kayanta sai dai kayan salman ne a jere tace oh wai nI ina akasamin nawa? Salman najinta amma ya shareta ya mike ya shiga wanka tabishi da harara.

Tana zaune ya fito sanye da kayan daya shiga dasu yazo yad'au kaya a drawer yakoma toilet, tace ba laifi he has manner🙄
ta mike takara duba kayanta, sai dai bata gansu ba, salman ne ya fito sanye da wata dakakiyar shadda ya kalleta sannan cikin magana kamar bayaso yace ki duba akwatina, yanakai nan yaI waje ta bishi da harara wato yasan inda suke shine ya shareta, ta mike ta hau kujera ta janyo akwatin dake kusa aranta tace wad'annan akwatin masu kyau sune na lefen kenan? Cikin hanzari ta duba tarr da d'auko wani swiss less mai masifar kyau tace amma kayan sunyi kyau nan tashiga neman hijab dazata sa, sai dai babu da alama wanda tai sallah dashi shi kad'aine gashI na sallar irin burum din nan ne, kawai ta wuce tai wanka, tasa kaya sannan tazo ta shafa mai ta murza huda, nan taji an murda kofa ta juyo salman yace malama ki fito ga abincin anan, ta kalleshi shima kallan ta yai she is natural beauty haka yaji zuciyarshi tafad'a ya kauda zancen yace mekike shirin yi hakan? Ganin ta d'auko hijab din ta zura, tace me nake kuwa? Yace ki tambattar kin cire hijab din nan kinsa mayafi kalar kayan, yarinya sai kace a rigar fulani😏

Ta kalleshi tace waya sani? Ya juya batare daya amsa mata ba tai raurau da ido tace da ace mutumincan karami ne da sai na mai dukan tsiya💪🏼👊🏻

Nace hmm 😜

By Ayusher Mohd📚Mohd📚

[11/13, 10:23]

NI DA PRINCE  Unde poveștirile trăiesc. Descoperă acum