NI DA PRINCE 5

7K 366 15
                                    


No 5

Tanajin motsin umma a waje amma abin haushi ko tazo ta tambayeta meya faru, Abbanta nadawo wa tamike da sauri taje tagaidashi umma da goggo nazaune bayan ya amsa, goggo tace dazun korar muftahun kikai shima? Salma tai kasa dakai, Abba yace wai ke Basira meyasa bakyaji? Na dade da fad'a miki bana san kina takurama salmah, ko kin manta matar da kamal ce? Tace yahkuri Alhaji ganinai tanata zama a gida ba kamal ba labarinsa.

Abba yace kada ki manta yanda muke da mahaifin kamal mu 2 ne a d'akin mu shine yayana kuma baki isa kisa zumuncin mu yai rauni ba, Goggo tace Allah yabaku hakuri, Alhaji nad'auka salma kamar 'ya take a gurina tunda nina raineta, Allah bai bani 'da ba.....

Da sauri umma ta katseta tace Goggo kidaina wannan maganar, sannan takalli salma tace ke kuma tashi ki bamu guri, salma ta mike duk jikinta yai sanyi tai d'akinta.

Umma takalli goggo tace kiyi hakuri hajiya, Alhaji bai kamata ka mata fad'a agaban wannan 'yar ba, Alhaji yace ai basira ce na dade ina mata magana bata ji, amma yanzu abar maganar nan zan kira kamal inji menene ya tsayar dashi dan ni kaina nasan gaskiya basira take fad'a, yana kai nan yai waje, umma tashiga ba goggo hakuri.

Yau salma na zaune a class suna d'aukan lectures hankalinta nakan karatun da akeyi har malamin yagama koyarwa ya fita zama tai a theater room din tana duba littafinta.

Ganin mutum tai ya zauna a saman desk din datake ta d'ago cikin mamaki tare da matsawa, mamaki ne ya kamata ta zaro ido sannan gabanta ya fad'I ta mike zata wuce hannu yasa ya fizgota tare da maidata inda take yace 'yar gidan Amadu ina zaki batare da uzinina ba? Tace izini? Yace eh ko kinfi karfi? Tai shiru tare da ture hannunshi tace wai menene dalilinka nasan shiga harkata? Yace I won't leave you har sai kin janye maganarki na tausayi daga kaina, in kuwa ba haka ba I promise you sai kinyi dana sani mai karfi.

Salma tai wani murmurshi😏 duk daba ganinta yake ba tace in naki fa?yace then mark my word😠, tace prince I am not afraid of u, yace u are not? Ta daga kai alamar yes yai murmushi yace then I will have to make you, yana kai nan yai waje.

Wata doguwar ajiyar zuciya ta rike hannunta dake rawa murya taji cikin sanyin ance salmah kiyi hakuri ki kuma ba salman hakuri, tad'ago cikin mamaki Najib tagani tace mena mai? Yace bakiyi komai ba amma salman ba abinda yatsana irin yaji ance yana ba mutum tausayi, ya juya ya fita, ta bishi da kallo tare da runtse ido tace yazanyi yaya kamal? 😞

Batafi 1 hr ba zee tashigo dasauri tace salma me kikayi? Salma tace name fa? Tace an kafe sunan ki a notice board an baki suspension na 2 weeks na dasauri ta mike cikin kidema tace suspension? Ni *SALMAH AHMAD MOHD* ? Zee tace wlh sunan ki akasa tace menayi? Tafad'a hawaye na zubo wa daga idanta tace akan me? Zee tace kema kinsani ai, salma tace I have to go an ask dan salman yace a bani suspension dan ni ba 'yar kowa bace sai abani?

Zee tace ki rufa mana asiri kar kisa a koreki daga skul din gaba daga, hannu tasa akai tafara kuka zee ta dafata tana rarrashinta.

Dakyar ta tsayar da hawayenta tare da d'aukar jakarta tace zee na wuce gida kuma plz karki fad'a a gida abinda yafaru tace to salmah.

A hankali take sauka daga steps din gun zuciyarta nakan tunanin abinda ke faruwa
har ta iso titi tana jiran mota.

Motace tazo kusa da ita tai parking tad'ago jajjayen idanunta, ahankali aka zuge glass d'in bayan motar, tana kallan wanda ke ciki haushi da wata muguwar tsanarsa suka mata yawa tadan matsa daga gun ahankali motar takara matsowa gun salman yace sorry limamiya I really pity you☹yanzu what can we do🤔? Jitai kamar tasa ihu d'an bakin ciki kalamansa amma me? Daurewa tai tace u don't have to pity me bawani abin bane dan anban suspension just take it as nasamu rest daga ganin mutanen dana tsani gani tana kainan ta matsa tafara tafiya da kafa.

Salman yai kwafa haushin kalamanta suka kamashi yakalli driver dinsa yace dalla wuce mutafi yace to ranka ya dade.

Salman na isa gida yana fitowa daga mota wanI bawa yazo yace sarki na nemanka, yace to tare dayin hanyar fadar sarki.

Zaune suke su 2 sarki ya kalleshi yace ka kyauta da wulakantani dakai salman yace Abba bangane ba? Yace ai ni ka wulakanta tunda bakaji kunyar sawa abawa d'aliba suspension ba wlh salman sai kasan kayi kuskuren b'atamin suna dasauri ya d'ago yace Abba yarinyarce fa.......yace just keep silent ka kuma bani guri sanda ishaq ya fad'amin zancen nan I thought karya yakema amma yanzu na tabbatar dan haka mike kaban guri😠.

Cikin sanyin jiki salman ya mike yana fita yai hanyar dakin ishaq sai dai yana tsaye daga waje yanajin shewar su ishaq da kannansa maza 4 suna murna kowa nacewa kai yarima ka birgeni, ishaq yace ai na dade da fad'a muku salman d'an karamin kwarone a gurina, ragowar sai jin jina mai suke ahankali ya juya yai bangarensa kansa na sarawa yana shiga d'aki ya zube ya shiga murkususu rike da kirji da kai dakyar yasha magani yashiga karanta *INA LILAHI WA INA ILAIHI RAJI'UN* ahankali yafara jin relief.

NI DA PRINCE  Där berättelser lever. Upptäck nu