NI DA PRINCE 4

6.7K 385 5
                                    

☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE
☄☄☄☄☄☄☄


*NA AYUSHER MOHD*

NO.4⃣

Salmah kam suna tafiya gun ta tsugunna ta shiga maida numfashi ta dade ahaka kafin ta mike ganin mutane tai agun suna kallanta ta dauke idanta tare da kallan agoggon hannunta, gani saura 15 mins su shiga next lectures gashi ko sallah batai ba yasa tai saurin wucewa, tana dubawa ko zataga zee.

Salman yauma sai magrib yashigo gun mai martaba ya wuce, ya dade kafin sarki yabashi izinin shiga, cikin nutsuwa ya shiga mai martaba yakalli fadawan gun yace kubamu guri suka amsa tare da mikewa.

Sarki ya kalli salman yace matso nan, cikin sanyin jiki salman ya matso kusa da sarki tare da sake gaidashi ya amsa fuska a d'aure, sannan ya cigaba haryanzu baka da aiki sai tsokanar mutane a makarantar ko? Salman yai kasa dakai Yace Ranka ya dade ba........
Cikin b'acin rai sarki ya katseshi yace anfad'ama duk abinda kake a makarantar bana sani? Ka kasa maida hankali kai karatu sai bin kawayen banza da wulakanta mutanena, sannan kana kallo kaninka Nazir yai aure amma kai banda shegantaka bakada aikin yi😠.
Salman kam idansa ya kad'a yai jaa batare da sarki yajira amsarsa ba yace wato yanzu rashin mutuncin ka ya kai wani mataki daka fara wulakanta mata ko? Salman yad'ago cikin mamaki sarki yace ina nan ishaq yazo yasanar dani ka cirewa wata hijab a makaranta ko karya aka ma? Gaban salman ne ya fad'I amma yadaure yace a'a, sarkj yace nagode salman kacigba da bakanta min rai.

Salman yai shiru zuciyarshi na rayamai kabada hakuri, can wata zuciyar tace ka manta me suka ma? Jin bashi da niyar bada hakuri yasa sarki yace dama kai bakasaba yin laifi kabada hakuri, tashi Kaban guri, ga mamakin sarki gani yai salman na kokarin mekewa ranshi yakara b'aci yace kakuma tabbatar ka fito da matar aure nan da wata 1 dan bazan d'auki iskancin da kakeji dashi ba, salman yace Abba wata 1 ai......dasauri sarki ya katseshi yace wlh ka fita daga idona ka sani bana magana 2 dan haka ka kiyaye.

Salman yai tsaye yakasa magana kuma ya kasa wucewa, wani bawa ne ya shigo yace ranka ya dade *Ishaq* na neman iso, sarki ya d'agamai kai alamar yashigo, dasuri ya juya, bai dade da fita ba ishaq ya shigo ganin salman yasa yasaki wani murmushi😏 tare da tsugunnawa ya gaida sarki, cikin sanyin murya ya amsa ishaq yace salman yanaganka a tsaye? Salman ya kalleshi sannan ya d'auke kai tare dacewa sarki nabarka lafiya, sarki bai amsaba salman kam da sauri yai waje.

Ishaq yace Abba Allah yasa dai d'an kanin nan nawa ba laifi yama ba? Inkuwa laifi yai ina bada hakuri a maimakon shi, sarki yace kyale sokon yaro zanyi maganinsa, sannan kafad'ama fulani ta fara nemo yarinyar dazai aura dan in bai kawo wace zai auraba nan da wata 1 to ba shakka aure zan mai.

Ishaq yace to ranka ya dade, sannan shima ya fita zuciyarshi fal farinciki lalai yau sunada karamin party.

Salmah kam tagama aikin gida takoma d'aki ta d'auko littafinta kenan taji yaro na sallama sai dai kafin tafita goggo ta fita tace yaro ya akai? Yaron yace wai ana sallama da salmah inji Muftahu tace muftahu? Wanne kenan? Yace muftahu mai babban shagon can tace au toh nagane, je kace gatannan yanzu zata iso, yace to tare da yin waje.

Goggo ta taho dasauri tana washe baki takaraso dakin salmah dake zaune duk taji abinda sukai da yaron, goggo tace tashi 'yar nan alkairi yasamemu😁 salmah tace name fa? Goggo tace gidan ku kina nufi bakiji me mukai da yaron can ba😠? Salmah tace au nad'auka sa'a yake nema( kanwarta da akai aure wata 4 dasuka wuce).

Goggo tace kaji min 'yar rainin hankali sa'ar datai aure za'azo nema? Tace kin manta ne goggo kwanaki.....ta katseta rufemin baki yar iskar banza to ke ake nema kuma muftahu ne mai katan shagon can salma tad'an tabe baki tace goggo kinsan fa ni yaya kamal nakeso, goggo tace lalai dalla rufemin baki kamalo ba kamalu ba kinsan Allah salma😠 tashi kafin na fasa miki baki.

Kasa tai dakanta tare da jan hijab dinta tai waje tana turo baki.

Muftahu kam ansha shadda da hula ga motarsa Civic ya ajiyeta yana tsaye ya juya baya, yanajin motsin kofa ya juyo yana murmushi takalleshi tare da d'auke kai tace ina wuni? Yacw lafiya lau *Salmat*😊 tace salmat? Yace eh mana ni haka zan dinga kiranki ta juya kai tare da yin shiru, yace salmat plz nazo da magana mai girma hope zaki fahimceni? Ta juyo tare da kakaro murmushi tace am sorry muftahu nasan kasan inada Wanda zan aura.

Muftahu yace salmat, kamal ba baida niyar auranki, inba haka ba shekararsa nawa acan? Kaf 'yan layin nan gulmar abin suke mahaifinki yabarki kina jiran d'an uwansa bayan kila shi yamanta daku.
Salma kam ranta yagama b'aci batare datace komai ba tai hanyar gida ta bude kofar tai dakin ta da sauri tafad'a kan gado ahankali hawaye yafara zubo mata.
...


By Ayusher Mohd📚

NI DA PRINCE  Where stories live. Discover now