Ni Da Prince 23

6.7K 348 18
                                    

☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄


*NA AYUSHER MOHD*

NO.2⃣3⃣

Sun isa gadon da akaba Abba, salman ya kalli d'akin kusan su bakwai ne a ciki, umma da goggo na zaune kusa dashi, salma da sauri ta karasa kusa da Abba, ta kuramai ido ganin yanda ya rame yasa hawaye kawai ya fara zubo mata.

Salman kallanta kawai yakeyi jiyake hawayen da take har zuciyarshi yake tab'awa, juyawa yai ya kalli su umma da goggo ya tsugunna ya gaidasu da mai jiki, sannan ya mike, idanshi ne ya diri akan kamal dake kallan salma shima hawayen yake, wani mugun kallo yama kamal haka kawai yaji bayasan yaron.

Daurewa yai yakalli goggo yace meke damunshi wai? Tace hawan jininshi ne ya tasha yace ayya nan yace bari inga likita tace to, ya juya ya fita.

Salma kam kuka takeyi, kamal ji yake kamar ya rungumeta ya lallasheta, juyowa tai tace umma meyasa ba'a fad'amin ba? Umma ta juya fuska, goggo tace Alhaji ne ya hana, salma tace su sa'a fa? Goggo tace yace kar afad'awa kowa kema kamal ne yafad'amiki dan baisan ya hana ba.

Tai shiru tare da waigawa, ganin bataga salman ba yasa ta cigaba da lekawa, goggo kam ta fahimceta tace to mara kunya, yaje gun likita, dasauri tace kiji goggo ce miki akai shi nake nema? Kafin goggo tai magana sai ga salman da wani babban likita, ya gaidasu sannan yace zamu maidashi wani d'akin, goggo tace meyasa? Likitan ya kalli nurses din dake bayansa yace ku turo gadon, sukace to.

Sannan salman yace goggo acan sai anfi kula dashi, tace to.

Nan suka meke dukansu salma takalli salman tai murmushi
Shima murmushin ya mata, kamal dake kallansu kishi duk ya isheshi.

Wani babban d'aki aka kai Abba, kana ganin d'akin kasan d'akine na mai matsayi, salma ta kalli salman tace d'akin nan yamana girma, salman ya harareta sannan ya kalli goggo da umma dakesan su fad'I abinda salma ta fad'a yace goggo karku damu ba wani abun bane, goggo tace angode d'an nan.

Salman yai murmushi sannan ya kalli salma ya mata alama da kaI ta biyoshi,sannan ya kalli su umma yace na wuce, dakyar umma cikin kunya tace angode, yai murmushi ya fita, salma ta kalli kamal wanda ya had'e rai sannan ta fita.

Kusa dashi taje tace makarantar zaka? Yace eh kinsan mai martaba yasa mai kula dani, in har banjeba da matsala, tai murmushi tace nikam shekarunka nawa? Salman ya had'e rai yace bangane ba😠 tai dariya tace bakafi 26 to 27 bako? Ya hade girar sama data kasa yace zaki fara ko? Tace sry gani nai ace har yanzu sai ana kula dakai🤔 ya juya yace ki biyoni mota, kallansa tai tare da sakin murmushi.

Kudi yad'auko mata mai kauri yace ki rike in case ko za'a bukaci wani abun,tace a'a nasan da kudi agun.....yace kinsan banasan musu ko? Hannu tasa ta amsa yace ko kefa? Natafi tace to zaka dawo ko in wuce? Yace da ke kad'ai kikazo dazakimin wannan tambayar? Tai kasa dakai, mota ya shiga yaja, har akasan ranta.

Juyawa tai, idanunta suka had'u dana kamal, ta karaso inda yake tace yaya, kamal ya juya cikin b'acin rai da sauri tasha gabanshi tace yaya meya faru? Kamal yasa hannu yaja hannunta ya fara tafiya tace yaya😳? ina zaka kaini? Kamal kam tafiya yake sai da sukai tafiya mai nisa, mutane nata kallansu, har sukaje gunda ba mutane sannan ya saketa.

Tace yaya me kakeyi hakan? Kamal yace tambaya ta ma kike? Salma dama akwai ranar dazaki zauna da wani namijin cikin farin ciki bayan ni? Ta kalleshi da mamaki tace yaya ya kakeso inyi da rayuwata😰? cikin d'aga murya da fad'a yace salma tambaya ta kike? Duk son da kika nunamin dama na karyane? Ni zaki yaudara? Nad'auka yanda nake sanki haka kema kike sona ashe ba haka bane? Me zaki cemin? Itama cikin fad'a da kuka tace yaya ya kakeso inyi? So kake in kashe kaina? Duk jiran danamaka ka manta dani, kabarni da tsananin begenka, ba nema? Kamal ya dafa kafad'arta hawaye ya zubo mai yace salma ban barku ason raina ba y don't u understand? Ta ture hannunshi tace fahimtar dani yanzu😠, kamal yai shiru tace bazaka iyaba? Dama nasan bakada abinda zakace, ta juya tafara tafiya.

Hawaye take harta isa d'akin, goggo ta kalleta tace daga rakiya shine kila dade? Batai maganaba ta zauna kusa da Abba ta kama hannunsa ta rike tana hawaye.

Salman kam dama inya shiga class wayarsa yake d'auka yai ta d'annawa ba ruwanshi da abinda akeyi, yau kam yayi shiru tunanin salma kawai yakeyi, ko mahafin nata ya farka daga allurar baccin da akamai? Ko jikin ya kara tashi? In ya tashi ya salma zatai? Wannan dalilin yasa yai shiru, har malamin ya fita baimasan me akeyi ba.

Najib ne yatab'ashi yace Prince ya akai? Amir yace hala tunanin Amarya ake, salman ya mike yace tunanin Amarya? Allah ya sauwaka, ya fita waje najib ya bishi yace ina zaka? Salman yace hm wani guri, sai gobe.

Dasauri ya fad'a mota yai hanyar asibiti.

Salma na rike da hannun Abba taji yayi motsi, dasauri ta d'ago tace Abba😥? Yakalleta tare da lumshe ido tasa kuka tace Abba laganka kuwa? Murmushi ya kakkaro ta kalli umma tace umma me za'a bashi? Ta mike ta zubo mata faten tsaki wanda yasha manshanu da yakuwa, salma ta amsa tare da taimakawa Abba ya mike, nan ta shiga bashi,ahankali ya dinga amsa har ya shanye.

Salman gudu yakeyi ya kai wajen titin gyad'I_ gyad'I mota tamai faci, haushi duk ya isheshi ga yamma tafarayi, waya yama driver dinsa yace ka kawomin prince 4 yanzu, yace to ganinan ranka ya dade.

Salman nazaune a mota haushi duk ya isheshi ga salma bata da waya, sai wajen 5 ya iso.

Dasauri ya amshi motar tare da barin driver din anan gun d'ayar motar.

Salma ganin Abba ya koma bacci, ga goggo ta tafi gida, umma ce a ciki yasa ta fito waje ta zauna a dakalin gun, kamal ne yazo yazauna kusa da ita, ta d'ago ranta a had'e ganin kamal yasa ta mike, dasauri yasa hannu ya kamota yamaida ita inda take, tace yaya.

Kamal yace salman jarabawa na fad'I sai dana zauna wata semester din tazagayo na sakeyI😞 kiyi hakuri dana barki ke kad'ai.

Kallansa take tana hawaye tace yaya meyasa baka fad'aba ko ta waya? Yace banso kisan saurayinki rago ne gun karatu, ta runtse ido kwalla sai zubo mata take, yace muje ki rakani na siyoma umma lemo, nima inasan kati.

Ta mike suka jero suna tafiya, salman da tun da ya iso yana kallan sanda kamal ya rikota duk yagansu duk da baisan me suka ce ba amma ranshi yagama dugunzuma.

Ganin sun taho tare yasa ya kunna mota, cikin tsananin bakin ciki da bacin rai ya kunno motar da karfi, da gudu ya taho, saura kiris ya kadesu, dan sukam sun gama tsorata kamal ya kamo hannun salma yasata a bayansa da sauri, salman sai dayazo daf da kamal ya taka burki jikake kiiiiiiiiiiiiii...


Kallan kallo suka fara, sai a lokacin kamal yaga ashe salman ne, salman kam hannun kamal daya rike salma ya kalla, daure wa yaI tare da fitowa daga motar, ya saki murmushi kamar ba komai ya matso kusa da kamal ya zare hannun salma sai alokacin tasan salman nema, ta kalleshi cikin tsoro, saidai ga mamakinta murmushi ya saki tare da kallan kamal yace ayya kamar baka gani? Ka dinga kula in kana tafiya karkaja a ragema farashi😉.

Kamal kam mamaki ya hanashi magana, salman ya kalli salma yasa hannu yajawota yace kema kamar bakya gani? Tace hm hm bankula bane🙁 yaceina zaki? Without my permission? Ta kalleshi sannan ta kalli kamal tace dama....ya katseta yace muje muduba Abba mu wuce gidanmu, yafad'a tare da kallan kamal.

Salman yafara tafiya itama ta bishi a baya, kamal kam ya kame yama kasa tafiya yana kallo har suka shiga ciki haushi ya isheshi yakaima motar naushi da kafa, sai dai maimakon yaji sauki sai zafin dayaji akafarsa😕













Hmm to fa🤔



NI DA PRINCE  Where stories live. Discover now