Ni Da Prince 24

6.6K 377 12
                                    

💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄


*NA AYUSHER MOHD*

NO.2⃣4⃣

Sun isa d'akin, Abba na jingine sai dai ya rame sosai, salman ya karasa tare da gaidashi, ahankali Abba ya amsa tare dama salman godiya.

Salman ya kalli umma ya gaida ita, tai kasa dakai ta amsa, sun d'an yi shiru kafin Abba yace kuje gida dare yayi, salman ya kalli salma sannan ya musu sallama, itama salma ta musu sallama ta fita.

A waje ya tsaya, yanakallan kamal ma tahowa gunsu yai murmushi tare da kallan salma yace muje ko? Ta kalleshi tace eh, ahankali ta matso suka jera suna tafiya, sai da sukazo daf da kamal sannan salma ta kalli kamal idanta taf da kwalla, salman ya kalleta ganin yanda take kallan kamal yasa ransa ya b'aci amma iya basarwa ta salman sai ya kalli kamal yace mr d'an rakiya dan zo ka shiga da ledojin nan tunda ciki zaka😉, kamal ya kalleshi sannan yace kai meyasa dazaka shiga baka wuce dashi ba? Salman yace karaso ka amsa, yafad'a tare da karasawa motar.

Kamal ya kalli salma ranshi duk a b'ace tace yahkuri yaya ba....wani kallo da kamal ya mata yasa tai shiru, kamal ya tsaya kikam salma tafara tafiya ta juya tace yaya? Kamal ya d'aure ya karaso, salman yai murmushi tare da mikomai manyan ledoji guda biyu yace tnx d'an rakiya😊, kamal yace karka kara kirana da sunan nan😠.

Salman ya shiga mota tare da rufowa sannan salma ta shiga, ya zuge glass d'in mota ya kalli kamal yace ban san sunanka ba me kake so ince? Salma zatai magana ya juyo ya kalleta tai shiru tare da turo baki, ya kalli kamal yace nyt😏, yaja mota da gudu ya bud'ama kamal kura.

Kamal ya kalli motar yace wlh mutumincen sai na👊🏻.

Salma kam a mota suna hawa titi salma ta kalleshi tace plz ka dainacemai haka☹. Cikin zafin rai salman yai gefe ya taka burki da karfi, salma kam ta tsorata da sauri ta jiyo ta kalleshi, sai dai yanda taga idansa yasata tai shiru, ya kalleta tare da nunata da yatsa yace karki kuskura!
*karki kuskura ki kara tarema wani a gaba* don't u dare do that again😡.

Salma kam jikinta rawa yake amma ta daure tace menai kuma? Ni meyasa kakemin haka? Tafad'a tare da zubo da hawaye, sai dai ganin tana hawaye yasa jikinsa yai sanyi ya juya tare da fara tafiya batare dayace komai ba.

Salma ta juya kai tana kallan window, wajen mai saida waya ya tsaya baice mata komai ba yafita, takalleshi tare dacewa kada Allah yasa kacemin kana zuwa😗.

Yad'an dade kad'an kafin ya fito, ya bude mota ya shiga, baice komai ba itama haka, har suka isa gida sun fito zasu nufi bangarensu wanI bafade yazo gun salman yace Ranka ya dade mai martaba na kiranka, ya kalli salma tare da mikamata karamar ledar yace wuce dashi ina zuwa tace to.

Amsa tai ta wuce shima yai banaren mai martaba, salma na shiga bangarenta hanne ta taho da sauri tace ranki ya dade kun iso lafiya? Salma tace lafiya, hanne tace ina kukaje ranki ya dade🤕? Bakiga fad'an da fulani tai ba mai martaba ma sai da yai fad'a.

Salma tace bangane ba😳? Hanne tace a ka'idar gidan ba'a fita sai mace tayi wata biyu amma ke kun fita ku biyu ba driver kuma ba wanda yasani😞.

Salma tace bansani ba ai dana sanar😰, yanzu mai zai faru? Hanne tace kawai dai fad'a za'amai tunda ansan ke bakisani ba.

Salma ta mike tai d'aki tare da zama dabas a kasa ta jingina kanta a gado, tasan salman bazai yi bayani ba saboda pride dinsa yanzu tasan anacan anamai fad'a.

A hankali hawaye ya fara zubo mata tace because of me😪 kanta ta had'a da gwiwa, tayi wajen minti 30 a haka sannan salman ya turo kofa kallanta kawai yatsaya yanayi, meyasata kuka? Jin sheshekarta yasa ya kasa jurewa kofar ya rufe tare da karasowa inda take, ya tsugunna yasa hannu ya jawota jikinsa, ahankali tad'ago tace me akacema😰? Ran sarki ya b'aci ko? Sai a lokacin yasan dalilin kuka, hannu yasa ya fara shafo bayanta, ta kankameshi tace am sorry because of me...katseta yai yace ba saboda ke bane, meyasa kike da saurin kuka ne? Salma kam tai luf a jikin salman sai d'an shesheka datakeyi.

Salman shiru yai yana tunanin fad'an da sarki yamai, shifa shiyasa bayasan zaman gidan nan, ace komai sai ka sanar?.

Sun dade a haka kafin hankali salma ta zare jikinta, ta mike salman yasa hannu ya jawota ta zauna a inda take yace wa........sai kuma yai shiru, azahiri so yake ya tambayeta meye tsakaninta da kamal? Amma jiyai bazai iya ba, kamar zata rainashi tai tunanin ya damu da itane, kallansa tai tace wa me? Hannunta yasaka tare da kikewa yai gyaran murya yace hm waya nake nufi wace kika shigo da ita, kiyi amfani dashi in kinaso, yana gama fad'ar haka yai toilet.

Salma ta kalleshi tare da rangwad'ar dakai tana kallon ya shiga toilet tace kace kawai kasai min waya☹ ta mike da sauri ta bude wayar, 😳 kalan wayar tace inazan kai wayar nan? Iphone 6 taga ga an rubuta a jikin kwallin tace ahh wasa yakemin hala🤔 inani ina wannan wayar? Tanajin ya fito ta mike takalleshi ta karaso inda yake tace amma dak ba wannance wayar bako? Ya kalleta dariya takusa zuwa mai ganin yanda takeyi da ido, ya d'aure fuska yace bata miki bane? Tace ni😳ina na isa? Ai wai naga.....ya katseta yace in ta miki to ya isa 😒 ya fad'a tare da matsar mata da hannunta yai ciki, ta karaso da sauri batasan sanda ta rungumoshi ta baya ba tace thanks a lot😊.

Salman jinta a bayansa yasa yai murmushi, salma ta sakeshi tadawo tagabanshi tace nagode sosai prince ta saki wani sanssanyan murmushi tare da lumshe ido shima murmushin yai.......

Nikaina murmushin nai😜

NI DA PRINCE  Donde viven las historias. Descúbrelo ahora