Ni Da Prince 36 - 40

13.8K 429 7
                                    

💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄

*NA AYUSHER MOHD*

NO.3⃣6⃣

Fulani zaune a kilisarta bakar maganar da salman ya fad'a wa d'anta ta dameta dayawa wata baiwa tasa ta kira mata ishaq ganin yau sam bai shigoba da alama shima haushin abinda fulani ta fad'a yake.

Salma ta shirya tsaf, dan salman ya fita makaranta kuma tafad'amai zataje gaida fulani, sun fito itada hanne, azahirin gaskiya gani take kamar bai kamata ace sai lokaci_lokaci take gaida fulani ba, ganin matan gidan kusan kullum sai sun gaidata, tana tsoron kar hakan yaja ma salman wani abun.

Sun isa bangaren, wata baiwa tace kishiga tana kilisarta,tace duk bayin su fita amma ke ai ba matsala, salma tace tom tare dayin hanyar.

Fulani zaune itada ishaq takalleshi tace wai haushi kaji? Yace umma ni narasa me kikeso inyi ki yabeni? Tace ina yabonka ishaq kawai banaso ne kadinga zama na karshe in aka had'aka da salman,ishaq yace nifa umma na tsani ganin yaron nan dan yana takuramin, daidai nan salma tazo shiga sai dai tasa hannu zatai knocking kofar taji fulani tace kodai musa amaidashi kasar waje? Ishaq yace ko? Tace eh mana ni kaina na tsani ganin salman gashi yai tamin kwarjini, inaji dai kawai musan yanda zamuyi yakoma can, dama acan yataso, salma da jikinta yashiga bari sai jitai ance in_law me kike anan? Salma ta juyo ad'an tsorace ta kalli farha, dakyar ta saisaita kanta ta kalli farha tace yanzu nazo tafad'a tare da kwankwasa kofar, fulani ta kalli kofar tace shigo? Salma ta d'aure murd'a kofar, farha ta kalleta tai tsaki tace da alama yau ranar ba sa'a tunda nafara karo da waccen.

Salma jiki a sanyaye ta shiga tazauna tare da gaida fulani,ta amsa itama a sanyaye dan tana tsoron ko taji, ishaq kam ya zuba mata ido kawai yana kallo,fulani ta kalli salma tace ina d'an nawa? Salma tad'aure tasaki murmushi tace yana makaranta, fulani tace salma ki kulamin da d'ana kinji? Kinga maraya ne😊 salma aranta tace lalai akwai 2face dayawa a duniya amma afili tace insha Allahu, ishaq ya kalleta yace ni naza'amin magana ba🤔 tad'an dago ganin kallan dayake mata yasa tamaida idanta kasa tace ban kula kana nan ba tuba nake, sai a lokacin hankalin fulani ya kwanta, indai tajisu to aikuwa tasan ishaq nanan, ishaq yace au hakane? Wato jikinki bai......dasauri fulani ta katse maganar da cewa salma kingadai sarki natsananin san salman dan Allah ki taimakamai karya dinga abinda ransa zai b'aci tace to, tare da kallan ishaq, tana mamakin me yakesan cewa d'azu.

Mikewa tai taredayi musu sallama, tana fitowa ta kalli kofar d'akin tace a waje kamar.......ta juya tai waje duk jikinta a sanyaye, tana shiga d'aki ta zauna abakin gado, lalai yau ta yarda in mutum ya rasa uwa to fa yayi babban rashi, idanta ya ciko da kwalla tausayin salman ne ke ratsata, tace ko ya sani? Can tace da alama ganin yanda
Yake musu.

Bayan isha'I salman ya dawo tana zaune tana game a waya, tanajin motsin kofa ta mike da sauri tad'au turare ta kara fesawa ta gyara zama, salman ya shigo da sallama salma ta amsa tare da murza iso, yashigo yace wai bacci? Tad'an kalli agogo tace kadad'e harna fara bacci☹ yakaraso yace uhmm anya kuwa baccin ake? Tace eh mana🙄, yai murmushi tare da sa hancinsa a wuyanta yace amma kamar yanzu akasa turaren na? Sannan ya sa hannunshi a bayanta yace kamar kuma wayarnan amfani ake da ita? Ta mike da sauri tare da ware ido ta turo baki tace ahhh wai kai ba'a fooling d'inka☹? Yajawota jikinsa yace inafa bayan baki iya pretending d'in ba? Kawai dai kice so kike ind'inga dawowa da wuri ko ba haka akeso acemin ba? Yafad'a yana kallanta, dasauri tashige jikinshi jin wani shock yai daga kansa har zuwa 'yan yatsun kafarsa, jiyai salma tace ni kad'ai d'in ne ba dadi☹ yai gyaran murya sanna yace insamomiki 'yan tayin zama? Tace suwa? Yace inada kanne mata ai ga farh.....tureshi tai tare da zama akan gado, ya kalleta ba shakka wannan kishi salma takeyi, kenan itama tana sanshi? Zama yai kusa da ita yace in mutum baisan abu yafad'a kawai bawai yad'inga had'e rai ba🤔 salma tad'an matsa tare da harde hannayenta tace eh banaso, happy? Yai murmushi batai auni ba taga kan salman a cinyarta, ta runtse ido inama salman na santa? Da gani zatai tafi kowa farin ciki a duniya, a hankali ta bude idanta, salman na kwance idanunsa ta kalla, shima kallanta yake, dasauri tad'auke idanta jin gabanta na fad'uwa, salman ya kalleta tare dasa hannu yadawo da fuskarya kansa yace yau nagaji shiyasa zan d'an kwanta anan, an bani pass? Ta kalleshi tai murmushi tace kunsha yawo kenan da najib ya kankance ido yace ummm da alama matar nan tasa ana bina🤔 salma tai dariya fararrn hakoranta suka fito, tace sai an dubamin? Bayan nasan me kuke a skul d'in? Yace ahh ashe fa hakane.

NI DA PRINCE  Where stories live. Discover now