Ni Da Prince 8

5.9K 342 8
                                    

☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄


*NA AYUSHER MOHD*

NO.8⃣

Abba tare suka taho da mustafa dakuma matarsa, salma na kwance a kasa inda tai sallah batasan sanda bacci ya dauketa ba.

Mafarki take mai dadi, wai gata rike da hannun wani sai dai bataga fuskarshi ba sun je bakin ruwa sun zauna, yasa hannunsa a kafad'arta tare da kwantar da kanta a jikin kafad'arsa murmushi take sosai, tareda jin wani sanyin shaukin kauna na ratsata, a cikin bacci taji anacewa ke! Ke firgigit ta mike tare da kallan umma dake tsaye akanta, umma tace tashi ku gaisa da baffanki tace to tare da mikewa.

A falo tagansu ta gaishesu suka amsa cikin farin ciki mustafa yakaleta yace salma inaso kisan duk abinda yafaru dake to ba shakka mukaddarine sannan mahaifinki dani masu sanki ne bazamu yanke hukunci akan abinda mukasan bazai taimakeki ba tace hakane baffa, Abba yace ungo nan ya mika mata d'ari 500 yace kije kisiyoma baffanki lemon fata da ayaba tace to tare da fita, taxo fita taga goggo tadawo nan tagaisheta ta wuce.

Haka ta tafi tana murmushi haka kawai tunda tai mafarki takejin farinciki.
Can bakin titi taje tana tafe cikin nikaf tana murmushi.

Mustafa shi dakanshi yazaunar da umma da goggo da matarshi dake ciki time din batasan meke faruwa ba ya musu bayanin halin da'ake ciki, Goggo kam tayi murna ta kuma yi bakinciki.

Tana murna salma zatai aure sai dai tana kishin auran d'an sarkin dazatai sai dai yaxatayi? Tunda batada 'da.

Hafsa matar mustafa tace amma kamal.....dasauri mustafa ya katseta yace inhar kamal yadamu da salma da tuni ya dawo sannan daya dinga nemanta ta hanyoyi daban daban amma ina sane baya nemanta, umma kam batace komai ba.

Abba yace kada kowa yafad'ama salma halin da ake ciki yanzu harsai bikin yazo kusa gudun kar sanda takema kamal yaja mata matsala sukace to.

Salma tadawo gida tawuce d'aki tare da d'aukan hoton kamal tace yaya inaji ajikina munkusa fara rayuwa tare ganin irin mafarkin danai.

Nace toh fa🤔 anya kuwa?.

Fulani dakanta ta kira Zainab da Zeena 'ya'yanta manya masu aure kuma sune kesan salman nagaskiya, nan ta sanar dazu umarnin sarki na lefem salman da zasu hado, murna sosak sukai, fulank tace sai dai yarinyar yar talakawa ce dan haka kusan irin kayan dazaku hado? Cike da mamaki zeena tace bangane ba? Dan zai auri talaka sai akace ita ba mutum bace? Zainab tace mudai zamuyi abinda muka saba, fulani tace kukuka sani😠 sannan ance kar wanda yama salman zancen auran.

Zainab tace bangane ba?baya santa ne ko me? Tace nidai nafad'a muku umarnin mahaifinku ne.
Suka kalli juna cikin mamaki.

Shirye shiryen biki ake sosai agidan sarki an tsaida lokaci nan da 3weeks, salman kam yafahimci akwai shirin biki da ake a gidan sai dai ganin ba wanda yamai maganar yasa shima ya basar ya nuna baisan me sukeyi ba.

Haka gidansu salma ita ba makaranta take zuwa ba sai dai itakanta batasan shiga da fitar da ake a gidan ba gashi kullum goggo sai ta kawo mata abu a kofi tace tasha intai magana sai tace bayam inakallan yanda kikeyi da jiki gabadaya shawara da basir sun kamaki, shiyasa ko makaranta bakya iya zuwa tace hmmm.

Yau saura sati 1 biki haka kuma yau ne sarki ya kira salman da daddare suka zauna a turakarsa, sunyi shiru na wasu lokutan sannan sarki ya nisa yace salman menene matsayina agunka? Salman ya d'ago da mamaki yace Abba yazaka tambayi 'da matsayin uba a gareshi? yacigaba Abba bani da kamarka aduniya, sarki yai shiru can yace nasani salman sai dai inasan intunatar dakaine yanda kakejin matsayin na agunka nima haka nakejin matsayinka aguna.

Salman yai kasa dakai idansa ya kad'a yai jaa, Sarki yacigaba salman na maka mata ina fatan kuma zakamin biyaya a matsayina na wanda bakada kamarsa, cikin kid'ima salman yad'ago ya kalli sarki yace Abba mekake nufi da mata? Sarki yace eh salman wannan shine my first and last request to u a matsayina na mahaifinka, salman bakinsa yashiha rawa kanshi yafara zafi samun kanshi yai dacewa bakomai Abba, sarki ya saki murmushi yace nasank sarai bazaka bani kunya ba.

Salman yai kasa dakai, sarki yace gobe ka shirya Mannir ya rakaka yace a'a nikadai zani, sarki yace a'a ko ishaq to kad'auka yacd zanduba, harya mike sarki yace nan da kwana 6 za'a d'aura auren ragowar sha'anin biki sai ta tare za'ayi tunda ba hali garesu ba, haushi yakamashi talakace ma kenan? yace da wuri haka? Abba yace mezamu jira salman? Kannanka fa sunyi aure yai murmushin yake tare da mikewa.


Salma kam tanata sharar dakuna dan yau tun safe 'yan gidan suka tafi gidan baffanta, tagama da d'akuna tashiga falon Abba ta share sannan tad'auko tsinma ta fara goge_goge tazo goge gun tv taga invitation Cike da mamaki tad'aga dan ganin auran wa za'ayi? Mamaki ya kamata ganin sunanta daro_daro wai ana gayyatar walimar bikinta ranar juma'a da misalin karfe 4, takalla dakyau basunan namiji, tace mekenan? Badai yaya kamal bane zai dawo akaki fad'amin😬.

Jitai ana kwamkwasa kofa tafi to dasauri makocinsu ne tagaidashi yace babankine yakirani wai inkawo miki waya zai kira tace to.

Basu dadeba Abba yakira tad'aga yace salmah kiyi hakuri naso in nadawo nafad'amiki wata muhimmiyar magana sai dai I am too late, tace na me fa? Abba yace ki shirya zakiyi bako sannan dan Allah inhar kinsan darajata karki wulakantamin bako, da mamaki tace to amma bakon guna zaizo? Yace eh ki tambatar kin shirya sannan karki manta karki wulakantashi indai......ta katseshi da sauri to Abba naji😊.

Yace kin yarda dani aiko? Tace in banyarda da Abba na ba dawa zan yarda yace good dan haka kitaimakeni karnaji kunya nida yayana tace Abba karka damu, nan sukai sallama.....


Hmmmmm😱

By Ayusher Mohd📚

NI DA PRINCE  Where stories live. Discover now