Ni da Prince 19

5.6K 361 4
                                    

*NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄


*NA AYUSHER MOHD*

NO.1⃣9⃣

Salma da salman zaune a gaban fulani, sun gaisheta ta amsa fuska a sake tare da cewa salman da ai jiya kasa hakuri nai nafara tunanin inje inga salma da kaina dan randa aka kawota banganta sosai ba saboda mutane dake bangarena😀.

Salman ya kalleta yasani sarai munafurci ne amma sai yai murmushi shima yace gashi ai tazo gaisheki, fulani ta kalli salma tace salman kayi dace yarinyar tamin sosai😊, ya kalleta sannan ya kalli salma yace nima tamin fulani😊, salma ta kalleshi tasan sarai karya yake amma batasan meyasa ta jin wani abu aranta? Salman ne ya kalli fulani zai yi magana yaji an turo kofa, baijuya ba dan yasan su ishaq ne, dasauri ishaq ya karaso ya zauna kusa da fulani, ishaq ya kalli salma yace Amaryarmu ya kike? Salma tad'ago ta kalleshi ganin yanda yake kallanta yasa tai kasa dakai tace lafiya, yace kanina dai baya wahalar dake ko? Takalli salman, tai murmushi tare da cewa a'a, ishaq yad'an hade rai yace salman akula da ita fa? Salman yace basai ka fad'aba, maganar taba ishaq haushi amma ya daure harsu salman suka fita yai tsaki yace ni wlh an cucen.

Fulani datasan halin d'anta sarai inyaga kyakyawa tace kul! Wlh ishaq ka fita daga idona, yace menai kuma? Tace nafad'amaka dai dan nasanka.

Salma kam suna isa d'aki ta kalli salman tace kai nafijin dadin fulani kamar kunfi shakuwa😀 gaskiya tanada mutunci, amma.....wani mugun kallo yawatsa mata yace will u keep ur mouth shut?tace me kuma nai? Dan nace fulani nada..karasowa yai ya jawota jikinsa yace what did u know? Idanta a runtse, ahankali ta bude idanunta ya kalleta jiyai wani abu na tsirgamai dasauri ya saketa, ya juya baya yace in bakisan komai ba kiyi shiru banasan magana😏 itama ta juya tace to.

Falo salman ya fita, ya kunna tv, ta fito ta tsaya a jikin labile tace aran waya please? Ya juyo yakalleta yace bangane ba? Tace uhm Abbana nakesan ma waya, yace sai kije kimai ai🤔tace to ai banda waya☹.

Kallenta yai tare da murmushi ya taso ya shigo d'akin tare da d'auko wayarsa dake kan side bed, ya kalleta yace baki da waya?tace eh mana baka kula ba? Yai dariya yace in these era? Tace to dole ne? Yace a'a ba dole bane amma in har kinaso inbaki aran wayata kidinga waya tofa dole kidinga bin umarnina😉 , tace da bana bi🙄? Yace inafa kike bI? Tai shiru can tace ai kai din ne, yace ni me? Tace kaima kasani ai yace bansani ba, tace to yanzu dai kaban nai waya sai musa rule din daga baya, yace a'a banyarda ba, ta turo baki tace to naji zan d'inga bi bani nai wayar, ya mika mata tare da zama akan gadon, takalleshi tace bazaka fita ba? Yace infita kimin bincike a waya? Tace ni😳? Yamata alama da ido yes, ta koma can jikin kujera ta danna number Abba, ringing biyu ya d'aga.


Tai sallama ya amsa tace Abba salma ce, yace salma nagane ya gida? Tace lafiya Abba yasu umma? Yace duk lafiya, tace Abba yaya kamal fa?

Salman dake zaune ya d'ago ya kalleta dama tanada yaya? Sai dai yanda yaga ta kalleshi ta kuma sa hannunta ta toshe wayar yasa jikinshi yabashi da wani abun, Abba yace salma meke damunki? Wani kamal kuma? Tai kasa da murya tace nasani Abba so nake naji ko yana gari ko ya koma? Abba yace bansanI ba kuma indai akanshi zaki dinga kira to karki sake kirana tace Abba.....jitai an kashe tace Abba☹.

Salman ne ya taso tare da fizge wayarsa yace daga wayar farko harkim b'atamai rai? Tace bafa haka bane😕yakoma jikin gado ya tsaya yace bari inkira inji dakaina me kikai?tunda ke dama haka kike dasan b'atama mutum rai😏.

Dasauri ta taso tace dan Allah karka kira, takaraso gunsa tace karka kira plz, ran Abba baci zaiyi inyaji kanannan nai waya, salman yace ohhhh kinsan bakida gaskiya kenan, kamal ko? Tace a'a mikon wayar ingoge number Abba, yace naki yafad'a tare da d'aga wayar sama, tafara dage tana kokarin kamowa, kafarta tad'anyi rawa tafada jikin salman wanda shikanshi d'agen yai dama kafarsa ba a daidai takeba nan sukai baya dukansu suka fad'a akan gado, salma tafad'a saman sa.

Ahankali suka bud'e ido, zuciyoyin biyu suka shiga bugawa salma kallanshi take shima haka, dasauri tafara neman tashi salman yai saurin sa hannunshi a kugunta ya rikota ta kalleshi, yaI murmushi yace haka kikeso dama ina kuma zaki gudu? Tace yaushe nace haka nakeso? Tafad'a cikin shagwaba, ya kwaikwayi maganar ta, ta turo baki tace sakeni plz? Ahankali salman yasaketa ta mike dasauri tai toilet, shikanshi jikinshi tsima yakeyi key yad'auka yai waje....


Hmmmmm

By Ayusher Mohd📚
[11/13,

NI DA PRINCE  Where stories live. Discover now