Ni Da Prince 41 - 45

14.2K 407 6
                                    

NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄

*NA AYUSHER MOHD*

NO.4⃣1⃣

Salman na gama shiryawa ya hau kan gado tare da jawo salma jikinsa, harta fara bacci, ya kura mata ido shikad'ai yasan me yake tunani a hankali yakai hannunsa gefen fuskarta ya shafa sannan ya sumbaci goshinta, shima ya kwanta, zuciyarshi sai kwad'aita mishi sha'awar salma ya daure ya tuno wahalar dasha, ahankali ya rufe ido,yana tunani baisan sanda bacci yai gaba dashi.

Sai asuba salma ta bude ido, tare da kallan salman, murmushi tasake tare da mikewa, balaifi taji saukin jikin ba kamar jiya ba,tai alwala tana fitowa salman ya bude ido cikin kalar bacci, takaraso inda yake ahankali tace ka tashi? Lumshe mata ido yai alamar eh, tace amma kamar ba masallaci a kusa ko? Naga ba gidaje, ya kalleta sannan yakara lumshe ido alamar eh, tai murmushi tace to ka tashe sai muyi sallar? Yai shiru kawai yana kallanta, ta sunkuyo tace kanaji na? Rigarta ya jawo ta fad'a jikinsa, ahankali yace a taimaken a d'agani nakasa tashi, mikewa tai tace ohh pretending? Yai shiru tare da d'aga mata gira, ta mike tare da kamo hannunsa, ahankali ya d'ago ta taimakamai ya tashi, yana mikewa yace tnx beauty☺, tace oh zaka iya tafiyar ashe, ya kalleta sannan yai murmushi yai toilet ta kalleshi tare da tada sallar nafila, tare sukai sallah sunyi adduo'I sannan salma ta kalli salman tace yaushe zamu tafi? Yace ina? Kin kosa ne? Dasauri tace a'a, yasa dariya yace baki kosa ba? Ta mike tare da kwanciya tace nidai yau inaji tsetse fly ne ya cijeni bacci nakeji, salman ya mike yazo ya kwanta kusa da ita, salma ta kamo hannunsa ta rike tare da kwanciya akan kafadarsa, bacci mai dadi ne yai gaba dasu.

Farha kam tun jiya tashiga d'aki bakin ciki ya hanata fitowa, da safe fulani taje d'akin tace wai farha meye hakan? Farha tace bafa sannan☹fulani tace an fad'amin to shine me? Farha ta kalleta da mamaki tace fulank kinfa san......fulani takatseta tace farha kidaina bani kunya mana, zan miki abu d'aya, zansan yanda zanyi salman yadawo yau ke kuma sai kisan yanda zakiyi ki aureshi.

Farha ta mike tace fulani salman nawa ne tun ina yarinya nasan da haka, ko saurayi nai bana kawo auransa araina salman kawai nake hange, fulani tai murmushin mugunta da alama tasamu wacce zatasa amaida salman kasar waje batare da tayi komai ba.

Salma karfe 9 ta tashi, a hankali ta zare jikinta daga jikin salman tai kitchen, dankali ta fara ferewa nan ta fara had'a kayan potato omelette d'in datake san yi, tana gamawa ta sa tafashen naman da suka siyo na sa, bayan ya tafasa tayanka sirara ta hada da karas da tarugu da albasa tai pepper meat.

Babu abinda kakeji a gidan sai kanshi, ruwan tea ta dafa ta ajiye a dinning,ta gama ta wanke hannu ta wuce toilet, tana fitowa sanye da towel, salman ya bud'e ido, cikin tsoro ta kalleshi😳, tunanin jiya ne ya fad'o mata, salman yai murmushi sarai ya gane, wata sha'awa ce ta tasomai, yq daure bai ce mata komai ba yai toilet, tabishi da kallo sannan tai ajiyar zuciya.

Kaya tasa doguwar rigar material ce ta mata kyau sosai ta tufke kanta bata d'aura d'ankwali ba, salman ne ya fito, ta kalleshi tace muje muyi break, tafad'a tare da matsowa kusa dashi, hannunsa yasa a nata yace harkin had'a mana? Tace eh, yace wooo I think shI yasa naji kanshi a cikin bacci na😎 takalleshi tasa dariya tace ko? Ya maze tace kamar kuma ba haka ba😏, ta turo baki ta kalli gefe, murmushi yai tare da janta, suna zuwa dinning ta bude potato omelette d'in salman yace wow not bad😉 ta hararreshi tare da rufewa, yace to in nace ya burgeni ko da gani zai dadi sai ki kushe shiyasa nima nace haka, tace amma ai.....yace naji amma a bani abinci inaci sai muyi maganar, yafad'a tare da budewa, wuka tasa ta yanka ta d'auramai a plate, yace kai abinnan ya burgeni, naman ta mikomai sannan ta had'amai tea, yace oh karfa dad'I yamin yawa mukoma ince nisai abincin matata🤔, tace nikam bazamu iya zama anan ba?

Ya kalleta tare da sa abinci abakinsa yace tun kafin nai aure naso nabar gidan sarauta sai dai bansan meyasa Abba yake hanani ba, salma tai murmushi tace hala yafisan yaganka a kusa dashi ne, kallanta yai bai magana ba kawai ya cigaba dacin abincinsa, itama shirun tai.

NI DA PRINCE  Where stories live. Discover now