NI DA PRINCE 3

6.8K 355 6
                                    

☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄



*NA AYUSHER MOHD*

*NO. 3⃣*

Motsin bude kofa taji salma ta mike da sauri dan tasan Abba ne takaraso inda yake ta rusunna tare damai sannu da zuwa ta amshi ledar hannun sa, cikin murmushi ya amsa yace andawo? Tace eh Abba, nan yakarasa daki itama tana biye dashi.

Falo yashiga itakuma tai dakim goggo ta mika mata ledar sannan tai falo gun Abba, azaune taganshi umma nakusa dashi, Abba yakalleta yace salma ya akai? Tace Hmm Abba dama......tafad'a tana kallan fuskar umma, Abba yakalleta sannan ya kalli umma yace ko in fito? Tad'anyi kasa dakai, Abba yamike umma tad'aure tace hb Alhaji? Yace ke kinjiki ai yarinya nasan magana da mahaifinta, menene a ciki?

Abba ya fito salma ta biyoshi tana kallan umma na harararta suna fita tace Abba kunyi waya da yaya kamal? Yai murmushi yace jiya daddadare dai ya kirani😊.
Salma tasaki murmushi tace Abba yaushe yace zai dawo? Yace hmm lalai salma tadamu yayanta yadawo tunda harta fara tambaya, salma ta rufe ido tace Abba karatu yafara tsauri inaso insamu mai koyamin ne🙈.....

Abba yai murmushi yace hmm banyarda da wannan wayan ba nida nakeso yana dawowa musha biki😀 dasauri tad'ago sai kuma ta ruga daki da gudu, yabita da kallo tareda murmushi yana san yarinyar duk cikin 'ya'yanshi yafi shakuwa da ita kasancewar uwarta bata shiga harkarta hakan yasa shine ke zama abokin hirarta tun tana karama.

Salma kam gado tafad'a tashiga ajiyar zuciya na farin ciki itakanta takosa tai auren nan ko dangin mahaifiyarta zasu daina mata fad'a.

Shekararta 22 amma tarasa dalilin dayasa idan kowa yake akanta kodayake kannanta 2 sunyi aure suna gama secondary, kaninta namiji kuma na makarantar kwana ta Gezawa.

Wahsegari ta shirya yanda tasaba tafito ta tafi makaranta, 12 suka fito daga lectures itada zee wajen wata kujera suka zauna, zee tafara tambayar salma akan karatun dasukai yanzu, salma sosai tashiga yima zee bayani wani guy ne yazo yace wai ana magana da limamiya, cikin mamaki zee tace limamiya? Antaba kiran macce limamiya dama? Yace haka akacemin nidai taje inji prince, yana kaiwa nan yai waje.

Zee takalli salma tace don't tell me ke ake nufi? Salma tai tsaki tace dalla share d'an iska, zee tace salma karfa asamu matsala dan prince inya tsani mutum har korarsa yanasawa ayi, Salmah tai tsaki tace keni duk wannan abun bai damenba menamai wai? Shine yaci mutuncina? Zee tace tashi mubar gun nan daga gani yaganmu ne.

Mikewa sukai suka fara tafiya, salmah jitai an ja mata hijab dasauri ta juya tare dacewa wani irin iskanci ne.....kalamanta sun katsene ganin mazan jiya su uku Amir na rike da hijab d'inta, cikin zafin nama ta fizge sannan tace meye hakan kakeyi? Amir yace tambaya kike?
Tace eh laifi ne? Mena muku wai?
A tunanina kune kuka min abu amma na nuna ya wuce to why are u bothering me? 😠 tafad'a tana hararra salman duk da cikin zuciyarta taf yake da tsoro amma ta riga tasa aranta bazata juri wulakanci ba.

Zee kam tagama tsorata ahankali tafara ja da baya, prince ne yakaraso inda take daf da ita hakan yasa tad'an matsa dan tanajin sautin numfashinshi, kara matsowa yai kusa da ita , zuciyarta sai bigawa take sai datakai jikin bango ya kara matsowa tadaure tace me kakeyin hakan? Yace dazu kin tambaya me kikayi shiyasa nake kokarin baki amsa, tadaure tace to d'an matsa yace in naki fa? Tai shiru.

Salman yace abinda kika fad'a jiya shine dalilin dayasa nadawo yau kikace maza irinmu nabaki tausayi? Mamaki ya kama salma itakam sam ta manta ta fad'I haka to meye inta fad'a karya tayi? Jin salman tai yace meye abin tausayi agareni? Bayan ubanki ba d'an kowa bane? Ta dago ido cikin b'acin rai tace arziki shine komai kake tunani? Yace ke yar gidan Amadu mai gini kishiga hankalinki sannan kiyi gaggawar janye kalmarki ta tausayi agareni wannan shine last warning dina......

Salma mamaki yakamata wato bincike yasa ayi akanta? Tadaure tace kalmace bazan janyeba tunda ba karya nai ba😏gini kuma da mahaifina ke ye ai baiwace wani sana'ar yi ma bashi da ita🙄 tuni zuciyar salman tagama dugunzuma ba abinda yatsana a duniya irin ace ana tausayin sa jiyai kansa yafara sarawa, hannu yad'aga alamar zai mare ta dasauri ta runtse ido ko meya tuna sai yafasa tare da juyawa dasauri.

Salma tabishi da harara Amir ya nunata da hannu sannan ya nuna idansa da hannu tasan meyake nufi wai they are watching me tace oho aikine bai isheku ba.

Salman kam toilet yashiga dasauri ya dafe kirjinsa ya d'auko maganinsa ya had'iya ahankali yafara jin numfashinshi na fita dai_dai........



By Ayusher mohd📚

NI DA PRINCE  Where stories live. Discover now