Ni da Prince 20

6.2K 367 5
                                    

*NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄


*NA AYUSHER MOHD*

NO.2⃣0⃣
Salma ta dade a toilet ba abinda takeyi tana tsaye, jin motsin bude kofarsa yasa ta fito daga toilet din, akan gado ta zauna tare dayin ajiyar zuciya.

hanne ce ta kwankwasa mata, ta bude tare da cewa hanne ya akai? Hanne tace ranki ya dade bakiga gidan ba kuma naga ko falo bakya fitowa, Salma tai murmushi aranta tace wani gida tunda basan juna muke ba, afili tace muje kirakani, tare suka dinga shiga salma tayi mamaki ashe akwai wani d'akin bayan tagama dubawa tad'an zauna a falo, hanne ce ta kawo mata madara nan salma ta amsa tasha, salma tace wai haka zanta zama ba abinda nake? Hanne tace eh mana aikinki shine ki huta, salma ta mike tare dacewa nama tuno, littafinta na makaranta tad'auko tafara dubawa, itakanta tausayin kanta takeyi tanasan karatunta amma batasan kozata cigaba ba.

Yauma sai 9 salman ya dawo lokacin salma na d'aki rike da littafinta salman yashigo tare da sallama, salma ta amsa batare data kalleshi ba ya shigo yare da cewa yau kuma karatu ne ya motsa? Tace eh thanks to someone, I can't even finish what I start🤔 salman ya karasa kusa da ita yace is that someone
Me? Yafad'a tareda nuna kansa👉🏻.

Ta d'ago tace eh mana, ya juya tare da cewa ko kika ja ma kanki ba? Tace hmm wai kai yaushe zaka koma skul? Yace ke share sai sanda nai ra'ayi tace ra'ayi? Yace eh ko kinada ja? Ta tabe baki a hankali tace dama mutumin da bai zuwa makaranta ina zaici jarabawa?.

Salman yace I can hear you, dasauri ta rufe baki tace wannan wani irin mutum ne? Can tace hmm nikam zan koma d'akincan da kwana😞yace ban bada permission ba, tace ehye? Yace kin manta menace miki ko? Tace banmantaba amma....kallon daya mata yasa tai shiru, ta kike ta fita ganin ya shiga toilet, pillow da bargo tad'auko a d'akin ta dawo, yana fitowa ya kalleta baice komai ba ya kwanta.
Tanaso ta tambayeshi yaci abinci? Amma takasa.

Salman kam yana kwanciya yai bacci, salma tayi shimfid'a ta kwanta, sai dai ta dade kafin bacci ya d'auketa.

Yau kwanansu 8 da aure sai dai rayuwarsu tananan ayanda take.



Salma kwance Cikin bacci takejin kamar ana nishi, idanunta ta bude tare da kalan gadon da salman yake, da yake da haske yasa taganshi a durkushe, da sauri ta mike ta matsa kusa dashi, ganin yanda yake zufa gashi ya rike kirjinsa sai nishi yake da kyar yasa dafashi cikin kid'ima tad'an birketoshi kankameta yai yana *inalilahi wa ina ilaihi Raji'un* salma ta kankameshi itama tace prince menene? So yake yai magana amma ya kasa ta kara rikecewa, tunda take bata taba ganin wani a irin wannan yanayin ba cikin rudewa tace bari insa akira likita tafad'a tana mai zare hannunsa daga jikinta, kara rikota yai ya girgiza mata kai.


Hawaye ne yafara zubo mata tace banganeba, kaganka fa😰? Ya d'aure azabar dayakeji ya nuna mata drawer din jikin gadon, ta kalleshi tare da budewa, ganin magani a 'yar farar roba yasa ta mikamai tare da janye jikinta ta miko mai ruwa, ya amsa ya had'iya ahankali yafara jin relief, can ya saki ajiyar zuciya,salma kam hawaye kawai take gani takw kamar mutuwa zaiyi, tariga tasa a ranta indai yasha magani bai warkeba ba ruwanta nemowa zatai akaishi asibiti ko a kira likita.


Salman ya d'ago ya kallI hannunshi data kankame tana hawaye,ganin ya d'ago yasa itama ta kalleshi, yace is ok I am alright, cikin hawaye tace wani irin ciwo ne wannan? Kana zuwa asibiti kuwa? Salman ya kakaro murmushi yace Is not a big deal fa, ta janye hannunta tare da mikewa zata wuce, hannu yasa dasauri ya kamo hannunta ta tsaya batare data juyo ba har a lokacin hawaye take, salman yace please karki fad'awa kowa, kinji? Ta juyo a fusace tace abinda zakace kenan? Wace irin rayuwa kakeyi? Bakada lafiya baza'a sani ba? Ya runtse ido batare da yai magana ba yasaki hannunta, dasauri takara matsowa tace jikin ne😰? Ya bude ido ahankali yace bacci tai ajiyar zuciya.

Salman bacci ne yai gaba dashi saidai salma takasa bacci kusa dashi tazo ta zauna tai shiru, batasan sanda bacci yad'auketa ba, cikin baccinta mafarkin rannan tasakeyi gata da wani hannunsu a rike suna kallan ruwa, sosaI dadin mafarkin takeji, dan murmushi harkan fuskarta.

Salman daya farka ya kura mata ido tana kwance tana bacci sai dai da alama mafarki me dadi take, abinda yaban mamaki shine ganin shima salman ya saki wani murmushin.

A hankali ta bude idanta salman ta gani kusa da ita tad'an turo baki tace ya jikin😞? Yace I am ok👌🏻zatai magana yace a haka kika kwana? Ta kalleta akan kujerar jikkn madubi data jawo take a zaune ta kwanta a jikin gadon, tace hmmm, yai murmushi tare da mikewa, haryaje jikin toilet ya juyo yace tnx 4 ur concern😉


By Ayusher Mohd📚
[11/13,

NI DA PRINCE  Where stories live. Discover now