NI Da Prince 22

6.8K 360 11
                                    

💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄


*NA AYUSHER MOHD*

NO.2⃣2⃣

Salman na fita a kujera ya zauna tare da furzar da wata iska, yace menai? Meyasa nazo nan? Ya mike tsaye tare da bude fridge yad'auko ruwan faro ya bude, ya kafa kai sai daya ahanye ruwan tas sannan ya saki numfashi.

Daki ya koma, salma ya kalla dake shimfid'a ya d'auke kai tare da hawa gado ya d'aure fuska yasa earphone a kunnansa, salma takalleshi aranta tace oh ni salma, jitai yace dani kike? Dasauri tace ba abu kakeji ba? Yace au in nasa earphone gulma ta kike kenan, ta juya baya tace nidai badakai nake ba, yace shine kika kira sunana🤔?

Ta matsa kusa dashi kad'an tace ni? Yaushe? Yace kice baki kira sunana ba? Tace ni wlh sunana nakira, yai tsaki tare da kwanciya, ta harareshi tace oh 🤔 juyawa tai zata wuce, yasa hannu ya rikota, ta tsaya tare da juyowa😳, yace oh me?tace nifa badakai nake ba☹tafad'a cikin shagwaba, jawota yai ta fado kan gadon kusa dashi, ahankali tad'ago ta kalleshi.

Yace oh me? Tace wai dakai nake? Yacs dakanki kike? Tai shiru, yace dazu natambayeki do u resent me kikace eh ko? Ta dan harareshi tace ba gaskiya kakeso nafad'a ba? Kaima kasan dole ne tunda kasa akaban suspension, sannan yanzu bana tunanin zan iya karasa karatuna😕.

Salman yasa hannu ya jawota jikinshi, yazo saitin kunnenta cikin rad'a yace bake kikace ni kike so ba😏? Haushi ya isheta ta zare jikinta tare da mikewa tace Allah yatsaren😠, mikewa yai tare da riko hannunta ta baya da karfi ta juyo dan taji zafin rikon, fuskokinsu ne sukai daf da juna yanda kowa najin numfashin d'an uwansa, salman ya d'aure yace Allah ya sauwake? Ni ya kamata infad'I haka ko ke? Kasa tai da kanta tace hannuna😞 tafad'a cikin sanyin murya, salman ya kalli hannunsa ganin yanda yakama mata hannu yasa ya zare a hankali, ta rike hannunta tare da kallanshi🙄yace Allah ya isa ko? Tace yaushe nafad'a kuma☹? Ya juya ya koma gado.

Ta dade tana kallanshi kafin itama ta kwanta sunyi shiru sai dai dukansu ba bacci suke ba, salma tace bacci? Cikin sanyin murya yace no, tace inada tambaya, yace tame? Tace yarinyar daxu wacece?salman yai shiru, takara cewa wacce? Jin bai amsaba yasa tace sry ina b'atama ra......jitai ya katseta dacewa *FARHA* tamaimata sunan tace wacce farha? Yace u don't have to know, tai shiru duk da bataji dadin amsar ba amma bata kara magana ba, salman yasan bataji dadi ba amma shi kanshi baisan tunowa, dan yanzu maganar dasukai akan farha shikad'ai yasan me yake ji.


wajen 9 yagama shiri tana zaune tana kallansh, tace yau zanje gaisuwa gunsu fulani, yace to, tace aran waya in kira Abba plz kafin kafita, ya mika mata, ta amsa ta kira Abba sai dai an dade ba'a d'agaba harta katse, takara kira, jin muryar mutumin datake kewa yasa ta mike tsaye tare da cewa yaya kamal? Tafad'a tana kallan salman, ganin ya juya baya kamar hankalinshi ba'a kansu yakeba yasa tace yaya kamal ina kwana? Kamal kam duk ya rude jin muryar salma, yace salma Kinga Abba ba lafiya munanan ma asibitin aminu kano, dasauri cikin kid'ema tace what? Yace eh salma jiya da daddare muka kawoshi, dasauri ta kashe wayar,hawaye yafara zubo mata,kusa da salman ta karaso ta rike mai riga, salman ya juyo yana kallanta, ganin hawaye yasa ya rikece yace salma menene?tunda take yaune rana tafarko daya taba kiranta da sunanta, sai dai bata kula ba dan hankalinta nakan Abbanta.

Salman yakara cewa menene? Jikinshi tashige tasa kuka, shikanshi baisan sanda yasa hannu ya rungumota ba yace menene wai? Tace Abba na ba lafiya yana asibiti, prince yazanyi😰? D'agota yai yace meya sameshi? Tace bansani ba nima😪.

Yace wuce kiyi wanka sai in kaiki, tace to nagode, dasauri tai toilet ya bita da kallo, cikin tausayi, salma kam wanka tai tad'auro towel sam ta manta salman na d'akin dan a kid'ime take, ta fito da d'aurin kirji, salman dake tsaye ya juyo ya kalleta, 😳 itama tana ganinshi tai saurin yin kara tare da komawa toilet din, yai murmushi tare da yin falo, sam ta manta yanannan kayan data cire ta maida ta fito, sai dai bakowa a d'akin tai saurin zura duguwar rigar atamfa tashafa mai da huda ta yafa mayafi, ta fito.

Salman dake zaune a falo ya kalleta, tace dan Allah ba inda zan sami hijab? Yace ki zo mu tafi dan nima ina sauri ne, tace to tare da binshi.

Sun isa asibitin Aminu kano, ta kira number Abba a wayar salman, kamal ya d'auka tare da musu kwatance, nan suka isa gun, suna sauka a mota kamal ya taho da sauri ganin salma, ya kalleta wani abu na tasomai, itama kallanshi takeyi duk ya rame, salman dake tsaye yana kallansu.

Salma ta daure tace yaya yanaga ka rame? Yace salma kema kinsan dole ne banajin zan iya rayuwa bake😞, idanta ya ciciko tace yaya ina Abba? Yace kuje ciki, ta juyo ta kalli salman dake tsaye ta inda ya fito daga cikin mota yana kallansu, tace muje cikin? Ya zagayo tare da cewa muje mana, kamal ya kalla wanda ya kuramaI ido, kana kallan kamal kasan kallan kiyaya yakema salman, salman ya d'auke ido tare da zagayowa ya kalli kamal yae d'an rakiya muje ko🤔? Kamal ya hade rai yace d'an rakiya? Salman yace wuce mana kana b'ata min tym😏.

Kamal kam ji yake kamar ya shake salman sai daI kafin yai magana salma tace yaya muje mana makaranta zai wuce, tafiya yafara kamar mara lafiya salman ya kalleshi ya tabe baki.

NI DA PRINCE  Where stories live. Discover now