Ni Da Prince 7

6K 359 6
                                    

☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄


*NA AYUSHER MOHD*

NO.7⃣

Salma kwance akan gado sam ta kasa barci sai juyi take rashin mutuncin da prince ya mata ne ke dawowa kwakwalwarta dasauri ta mike zaune tare dayin kwafa tace a fili yaron nan da ace nasanshi dasai na rama rashin mutuncin dayamin😠wata zuciyar tace kinsan shi mana sai dai in tsoro kike😀, dasauri ta tashi tsaye tace tsoro? Nidin? Inji tsoron wannan banzan? Alla ya sauwake🤔, haka tai ta shirme a d'aki sai 12 tasamu tai bacci.

Waziri ne zaune agaban sarki yace ranka ya dade daga gun malam nake anyi istihara akan al'amarin nan ba shakka wannan auran alheri zai jawoma salman mai yawa, sannan maganar yarinyar kawai dai 'yar talakace amma halinta kaf 'yan unguwar sun shaida kyan halinta.

Sarki yai shiru can yai murmushi yace Alhamdulila, waziri yace ga kyau dan 'yan unguwar sunce kyanta dayanda maza ke binta yasa take saka nikaf, sarki yace naji dadin binciken nan zancen talauci kuma ai ba wanI abu bane da talaka da mai kud'I duk daya suke agun Allah.

Waziri ya kara tsugunawa yace Allah yajada ran mai martaba, yanzu insanar dashi?sarki yace a'a kasan halin salman taurin kai, kafiya in har yaji to da matsala, waziri yace ai halinku d'aya ranka ya dade yafad'a yana murmushi, sarki yai gyaran murya hakan yasa waziri yace tuba nake ranka ya dade.

Sarki yace yanzu kuje kai da yayana kusamu mahaufinta kuji ko an mata miji, waziri yace bamu zamu kirashi ba? Sarki yace a'a ai mu muke nema, waziri yace angama rnka ya dade yafad'a tare da mikewa.

Sarki yai murmushi shi kanshi yakosa yaga salman ya nutsu, haka kawai yakejin farin cikin zancen auran nan.


Waziri yasa asanar da Amadu zasu shigo da yamma, duk da Abba baisan meke faruwa ba jin ance wai wani mutumi kesan ganinsa akan wata muhimmiyar magana, haka kawai Abba yasamu kanshi da fad'awa d'an aikin in ba damuwa su hadu a sharad'a inda yayansa yake cike da mamaki d'an aiken yace ba damuwa.

Nan Abba ya koma gida yaI wanka yasa manyan kaya, umma takalleshi tace meke faruwa? Yace nikaina bansani ba amma kibari inje indawo nikainan bansan menene ba kawai dai naji dan aiken yace mutumin kamar yanada hadi da gidan sarauta, tai shiru tace to Allah yasa alkairi ne yace Ameen Basira bata dawoba? Tace eh yace salma fa? Najita shiru, umma takauda kai tace inazan sani? Yai tsaki yace sai kiyi tayi ai hakan jiya 'yarnan fuskarta duk ta canza amma wai bakisan menene ba? Yai waje cikin fishi.

Dakin salma ya shiga tana zaune rike da hoton yaya kamal tanajin salamar Abba tai saurin boye hoton yakalleta cike da tausayi yace zan fita tace to Abba d'aurin aure? Yacs a'a tace adawo lafiya yacs amin tare dayin waje, yana tausayinta sosai dan jiya ya duba yaga adadin kiran datama kamal amma bai kira ba shikam dan dai bayanda zaiyi ne amma shikanshi yanaso 'yarsa tai aure.

Yayan Amadu wato Mustapha jin sakon kaninsa yasa aka gyara falon baki tare da siyo lemuka, bayan Amadu ya isone bada dade wa ba kira ta shigo wayar Amadu ya amsa jiyai ance bakin dazasu zone muna sharada gidan wa zamuce? Nan Amadu yashiga kwatanta musu har suka gane.

Su Amadu na zaune da yayansa suna hira suka dingajin hayaniya a waje cikin mamaki mustapha ya mike ya fito Amadu na bayanshi.

Mamakine yakamasu ganin motoci guda 6 sun jeru a kofar gidansa ga fadawa a tsatsaye Mustapha yace hala wani taro nasarauta za'ayi Amadu yace ko kuma hawa ba? Naga in gidan sarauta zasuyi aure suna hawa, nan sukai murmushi tare da juyawa ji sukai ance banan ne gidan Mustafa ba yayan Amadu? Atare suka juyo suka kalli bafaden dayai maganar, Amadu yadaure yace nan amma meke faruwa? Ahankali aka bude motoci biyun tsakiya kowace waziri da yayan sarki Modibo suka fito.

Mustafa da Amadu sukai kuri suna kallo ga kutane sun cika gun, jisukai wani bafade yace a waje zaku barsu? Dasauri Mustafa yace ahhhh ku ku shigo.

Waziri da Modibo suka nufi gidan shikam Amadu jiyai kamar yayi mutuwar tsaye tunaninsa d'aya laifi yayi kawai.

Sun zauna su kuma su Abba sun tsugunna suna kwasar gaisuwa,modibo yaI murmushi yace haka ake neman aure a tsugunne? Cikin sauri mustafa da Amadu suka d'ago ido? Tare da kallan juna sukace aure?Waziri yace kuzauna mana, nan suka zame suka zauna, modibo yace muna namawa Salman d'an gidan sarki auren 'yarku salma, cikin kidima Abba yace eye? Waziri yace eh muna neman alfarma, sai dai in kun mata miji to fa wannan ba yanda zamuyi, Abba yai shiru zufa tashiga keto mai, yakali mustafa shima zufar yake, Abba yadaure yace salma? Waziri yace ita fa, Abba yace ku gafarceni ranku ya dade amma....dasauri mustafa ya katseshi yace mun baku indai Salma ce😬 waziri yace amma kuwa muna godiya, yace a'a ai mune da godiya, Modibo yace to *Alhamdulila* munji dadi sosai sai dai munada magana, Nan su Abba suka d'ago, Modibo yacee bamasan auran ya wuce wata d'aya Abba yace wata 1? Waziri yace eh sannan munaso ku taimakemu karku mata komai nakayan d'aki mustafa yace amma ina ake haka? Modibo yace wannan gudumawar sarkine na amsawa dakukai zaku bamu 'yarku, mustafa yace toh😳.

Nan modibo ya ciro bandir din dubo d'aya guda 3 ya ajiye yace wannan kudin mun gani muna so ne kenan kudin gaisuwa cike da tsoro Abba yakalli kudin zaiyi magana mustafa yarigashi yace mun gode amma kudin nan yayi yawa, guda d'aya zamu d'auka sannan inkun tsaida ranar auran sai a turo afad'amin nan sukaita godiya suka mike.

Abba ya zube a gun yace yaya yazamuyi da kamal? Mustafa yace kamal basan auran salma yake ba tunda haryakai wannan lokacin batare daya dawo ba bayan nasan yagama karatu, Abba yace salma fa? Datake tsananin sansa? Yace intai aure zataso mijinta kasan zuciyar mace ai.


Hmmmmmm babar magana🤔

By Aysuher Mohd📚

NI DA PRINCE  Where stories live. Discover now