Ni Da Prince 26

6.4K 381 13
                                    

NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄


*NA AYUSHER MOHD*



NO.2⃣6⃣

Salma kam haka ta zauna sukuku a gidan sam batajin dadi gashi tasan duk kiran dazatama salman ba d'agawa zaiyi ba.

Salman kam da yamma yad'au najib sukaje suka dubo Abba yau kam kamal bayanan sai mahaifinsa, sun d'an dade kafin su taho, gidan najib ya koma, najib ya kalleshi yace prince wai meye hakan? Bazaka wuce gida ba? Salman yace malam ba ruwanka dani😠 najib yace amma salman ai hakan bai dace....ganin salman yayi ya mike tare da komawa gado ya kwanta, najib ya kalleshi sannan ya girgiza kai, salman sai juyi yake can kuma ya mike ya d'au makulli yai waje, najib ya bishi da kallo tare da murmushi yace tunda yazo yau hankalinshi baya nan amma yaje inda hankalinsa zai kwanta pride dinsa ya hana🤔

Salman ya isa gida, salma tunda tai sallar isha'I tana zaune akan sallayar ta d'aura kanta akan gwiwarta tayi shiru tanajiran salman, ahaka batasan sanda bacci yafara d'aukanta ba, ahankali salman ya turo kofa sai dai ganin salma tana bacci yakara tunzura shi wato ita ko ajikinta ko? Shigowa yai ya d'au kaya ya wuce toilet yai shirin bacci, yana fitowa ya tsaya a jikin gado ya kurama salma ido, yarasa mai yake tunani, haka kawai yasamu kanshi da rashin san d'auke idanunta, a fili yace tanasan bacci a takure.

Salma dake bacci ahankali ta bude ido, idanun salman tai arba dasu, dasauri ya d'auke idanunsa, salma ta mike da sauri tazo kusa dashi tace yaushe ka dawo? Salman ya shareta, tace yanzu? Ya mata banza gado ya hau yasa earphones akunnensa ta zauna kusa dashi tace sannu da zuwa, salman yai kamar baya jinta, tace plz kace wani abun☹, tafad'a cikin shagwaba, salman kam wani gun ma yake kallo.

Tarasa yazatai, hannu tasa tare da zare earphone na kunne daya ta Matso tasa a nata kunnen, wani sauti mai dadi ke tashi, dagaji piano ne,da mamaki salman ya kalleta, ta lumshe ido jin dadin sautin amma wannan kid'an bazai hana mutum jin magana ba wato yana jinta kenan, ido ta bude, sai dai salman tagani yana kallanta, tace sautin yamin dadi, sa hannu yai ya zare na kunnenta, ta hade rai tace dan Allah ni ka kulani, ko fad'ane kamin, amma ni bansan shirun nan.

Ganin bashida niyyar mata magana yama juya kansa d'aya gefen, itama komawa d'aya part din tai tasa hannu ta zare duk earphone din ta mike da sauri, salman ya kalleta yace bani abuna? Tace um um naki, tafad'a tare da noke kafad'a ta katasa wajen madubi, ya mike yafara tahowa inda take yacd bazaki bani ba? Tace naki sai ka tsaya munyi magana.

Ya karaso inda take, dasauri ta boye a bayanta, ganin yana tahowa yasa sai sauri ta koma wajen gado, yakara tahowa yace bazaki bani ba? Tace naki, inkanaso kacemin ka hakura😉salman ya bita nan fa suka salma tasa gudu shima ya fara binta, ta gado ta haura ta zagayo shima ya bita ta ka ra zagayowa ta hau gado kenan yasa hannu ya kamo hannunta, itama ta fara ja a tare suka fad'a kan gadon, suka yi rigingine kowa na ajiyar numfashi.

Can salman ya d'ago ya matso daf da ita yace bani🤔? Yafad'a tare da mike hannu, itama ta d'ago tace ungu? Ya matso da hannun tace naki sai ka hakura, tafad'a tana kokarin tashi, jawota yai ya kwantar da ita ya matso daf da ita yanda kowa najin numfashin d'an uwanshi, yace kinsan me kika min? Yafad'a cikin wata murya mai rikitarwa ga sanyi, a hankali ta kalleshi zuciyarta sai bugawa take itama cikin sanyin murna tace sry I didn't mean to hurt you, yace then? Tace narasa yanda zanyi ne😞 yace akan me? Tai shiru yace ba amsa? Ya fad'a tare da kokarin tashi da sauri tace banasan asake ma fad'a ne, tafad'a tare da runtse ido.

Juyowa yai da sauri, baiyi tunanin amsar dazata bashiba kenan, yaji dadi har cikin ransa at least ta damu dashi, ganin yanda ta runtse ido yasa ya turo fuskarsa, zuciyarshi na haskomai bakinta, girgiza kai yai tare dasa hannu ya lakuce mata kumatu yace meyasa baki fad'amin ba? Ta bude ido sai dai ganinshi daf da ita yasa tai saurin murginawa d'aya bangaren tare da zama, tace um um to ba inasan ma maganaba ka fita tafad'a tare da turo baki, murmushi yai yace basai ki min text ba? Tace ince me? Yace abinda kikace yanzu, tai murmushi tare da rufe fuska.

Yamike yace kin b'atamin gun kwanciya ki tabbatar kin gyara kafin nasha ruwa😏 yanakai nan yai waje tace ahhhh wai wannan wani irin mutum ne?🤔

Mikewa tai tana gyara tana murmushi, shikanshi a falon zama yai yana murmushi.

Nace ku kuka sani😏

NI DA PRINCE  Where stories live. Discover now