Ni Da Prince 27

7.2K 380 11
                                    

☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄


*NA AYUSHER MOHD*


NO.2⃣7⃣

Salman zama yai afalon yai shiru tunaninsa shine meke sashi farin ciki bayan da ba haka yake ba? Idansa ya lumshe fuskar salma ya hango tana murmushi dasauri ya mike tsaya yafad'a a fili mai ke damuna🤔?

Salma kam kwanciya tai ganin salman bai dawoba yasa ta mike tayi hanyar falo, lokacin salman ya kashe wutar falon yai hanyar d'aki, salma data fito ganin duhu yasa tafara laluba bango ko zataji makunnar wutar gware sukai, salma ta saki wata kara, dasauri salman ya jawota ya rufe mata baki, yakai bakinshi kunnenta yace is me🙂 ajiyar zuciya tai ya rike ta tare da kunna wutar ta kalleshi tasa hannu tad'an bigi kirjinsa kad'an tace ka tsoratani wlh😰, salman ya rike hannun da ta dakeshi yace dakin d'auka meye? Ta turo baki cikin shagwaba tace tokai meyasa zaka zauna a duhu? Yace d'akin zan shigo shiyasa nakashe, tai ajiyar zuciya tace bakaji zuciyata ba wlh☹ yace kedai kawai kinfiya raki, ta kwace hannunta tare da juyawa,,ya kalleta yace me kika fito yi? Tace hmm.... yace don't tell me fitowa nemana kikai?ta harareshi tace ni? Dalili? Ran salman ya soso yaso tace gunsa tazo, salma kuwa takarasa fridge tad'auko ruwa tace ruwa nazo sha, tawuce d'aki tabarshi agun.

Dakin shima ya shigo batare dayai magana ba ya fad'a gado, salma tuni tai bacci, sai dai salman sam yakasa barcin sai juyi yake, kallan salma yake wacce da alama tai nisa a bacci.

Ganinai salman ya mike yazo kusa da salma a hankali ya d'agata yakaita kan gado ya kwantar da ita tare da lilibeta, yazauna kusa da ita yana kallanta, mamaki yake yanda sam baisan yadaina kallonta, yadade a haka kafin ya mike ya d'au pillow ya sauka kasa.

Ga mamakina gani nai ya kwanta a gunda salma ke kwanciya😳nace prince din?hmmmm...


Salma kam bacci yayi dadi gashi sai mafarkin saurayin nan take, suna zaune a bakin ruwa taga ya mike ya far gudu itama ta bishi, ganin yanda yake gudu da alama wani gurin zaije, ita kuma sam batasan ya tafi, gudu take sosai tanaso ta kamoshi sai dai gudun da saurayin yake yafi nata, ganin ya mata nisa sosai yasa ta zauna a kasa tahau kuka, yau ma bataga fuskarshi ba, a zabure ta mike, dai_dai nan salman ya fito daga toilet yayi alwala.

Yace lafiya? Ga mamakinta hawaye taji a idanunta, salman ya zauna kusa da ita ya dafata cikin kid'ima yace menene?rungumeshi tai tsam batace komak ba, yace menene? Mafarki kikai? Ta d'aga kai yace mafarkin me? Tai shiru, ahankali ya d'agoda ita yace kidinga addu'a in kikai mafarkin da bashi da kyau, ta d'aga kai tare da kakaro murmushi, yace bari nai sallah tace to, ya juya ya fita.

Binshi tai da kallo sannan takalli inda take, mamakine ya kamata, ya akai taganta a gado? Meya faru? Sam takasa tunano komai, mikewa tai tare da wucewa toilet.

Salman kam da ciwo jiki yatashi, tun dayake ranar ce rana tafarko daya kwana a kasa duk jikinshi ciwo yake.

Sai 6:30am salman ya shigo tana zaune tana karatu, tana kaiwa aya ta rufe qur'anin tareda mikewa taje gunsa, tace ina kwana? Salman ya amsa tace ya akai naganni anan?salman yai gyaran murya tace badai kaika maidani ba😬 ya hade rai yace jiyane naji bayana naciwo shi yasa na kwanta akasa, tai murmushi tace yanzu fa? Yadaina ciwo? Ya kalleta yace a'a, hannu tasa tace in bubuga ma? Ya kalleta yace bansaki ba😏 ta hade rai itama tace dacema akai inaso inma? Ta juya, hannu yasa ya rikota yace serious jikina ciwo yake dannamin plz.

Kwanciya yai akan gado tashiga danna mai, ahankali yake lumshe ido bacci mai dadi ne yai gaba dashi, salma ganin yai bacci ta matso da fuskarta inda yake ta kalleshi, jitai zuciyarta na bugawa, sai ta hau shakuwa, dasauri tai falo ta bude fridge ta d'auko ruwa tasha.

A kujerar dinning ta zauna tace menene hakan? tadade anan kafin ta dawo d'aki ta kwanta.

Karfe 9 ta tashi dan yau zasu gaisuwa, matsawa tai takalli salman tare da murmushi, ga mamakinta shima murmushin yai cikin bacci, jitai zuciyarta yashiga bugawa dasauri takoma ta zauna,wayarta ce tai kara tad'aga tace waye?zee tace banza nice mara mutunci, salma tace duk ni kadai? Zee tace dazu naje gun Abba shiyaban number ki, tace ayya nan suka shiga hira, salma ganin zata tashi kamal yasa tafi to tai d'ayan d'akin, zee tace badai laulayi kike ba? Daga shiga? Salma tai tsaki tace kefa bakida mutunci, zee tace ah to meza'a jira? Salma tai shiru, zee tace badai haryanzu baki bada kaiba? Salma tace dalla nikimin shiru, dan Allah ni akwai abinda nakesan tambayar ki, zee tacw name?

Salma tace watace intaga wani sai zuciyarta tad'inga bugawa shine ta tambayeni menene dalili, nikuma bansani ba nace bari na tambayeki.

Zee ta kwashe da dariya tace ai kinji matsalar ke bakisan kowa ba sai kamal inafa zakisan karfin soyayya? Salma tace duk sanda nakema kamal? Zee tace oho dai amma kifad'ama mai tambayar ba shakka ta kamo da soyayya mai karfi tunda har zuciyarta take amsawa, cikin tsoro salma tace what? Soyayya? Bakisan me kike cewa ba🤔, zee tace oho sai dai inkim gaskiya zatai amma wannan shine gaskiya, dasauri salma ta kashe wayar tace ah hb? Ni? Ta ina?how?



Tana komawa d'aki ta tadda salman bayannan da alama yana toilet, bayan ya fito takalleshi sai kuma ta girgiza kai ta wuce toilet dasauri, ya kalleta yace wannan kuma lafiya? Salma kam haka tai wanka sukuku, tasa kaya.

Abinci kuwa ruwan zafi kawai tasha salman yace shikenan abinda zakicI? Tace nakoshi😞yace wasa ne, tace in muka dawo zanci to, yace naji amma meyasa tun d'azu bakya kallona?tace hmm bakomai, yace bazaki kallanba? A hankali tamai alama da bayin dake gun, hakan yasa yai shiru suka mike sukai cikin gida.


Sunje bangaren hajiya karama da babba kafin suje gun fulani, ishaq na kalisarta tunda suka shigo yake kallan salma, itakam kasa tai da idanta dan sam batasan wannan kallon,sun gaida fulani nan tace salman rannan ka fita akaita fad'a nikam duk banji dadi ba nasan dai fitar dakai aI da dalili haka kawai bazaka fita ba😞salma takalleta, a iya saninta hanne tace fulani ce taita masifa kodai hannen bata fahimta bane? Muryar salman taji ya ce nasani ai kin damu dani, ishaq ya kalli salma yace salman amma matarnan taka bata magana ne? Salman ya kalleshi yaji haushin tambayar amma ya saki murmushi yace kai ya ishaq ko tana magana yaza'ai ta saki tai ta magana kana gun😏? Haushi ya kama ishaq yace nid'in meye?salman ya kalli fulani yace umma kodan abunda yakeyi zata sake jiki dashi? Yafad'a yana wani mugun murmushi, fulani ta kalleshi ta kalli ishaq bakin ciki ya isheta tace eh mana gaskiya ya fad'a.

Salma ta d'ago ta kalli salman mamaki take yanda yake fad'ar bakar magana yana murmushi, wannan wani irin mutum ne?


Lol nikaina AYUSHER so nake inji😆

NI DA PRINCE  Onde as histórias ganham vida. Descobre agora