Ni Da prince (46-50)

1.6K 26 0
                                    

NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄

*NA AYUSHER MOHD*

_*This page is dedicated to all members of my group " The Queen Bee" thanks for ur love and care.... love u oll.*_

NO.4⃣6⃣

Salma haka ta zauna har saida salman yagama cin abinci tana kalansa, daya ce taci sai tai murmushi tace ni ba yanzu ba, nafisan in kalleka har ka gama, yace in na kware fa? Tace bazaka kware bama in kuma hakan tafaru sai in baka ruwa😊 tai maganar tare da nuna mai jug d'in ruwa, dariya yai yacigaba da cin abincinsa, bayan ya gama ya mike, salma tace ina zuwa, ya kalleta da mamaki, d'aki tai da sauri, ta d'auko jotting book d'inta sabo ta duba rubutun ciki baifi 3pages ba dasaurI tasa hannu ta yage, sannan ta d'au biro ta makala a littafin ta fito da sauri.

Salman na tsaye yana jiranta ta karaso tare da mikamai, yakalleta yace na menene? Tace na karatunka mana😉, salman yace what? Tad'an turo baki tace a class in anyi wani abun ai zakai jotting, salman yace wa? Ni? Salma tace kai my prince☹ irin wannan dizgi😢? Salman ya kalleta yai murmushi yace hakan ne dizgi? Ta juya baya cikin shagwaba tace eh mana gashinan☹, ajiyar zuciya yai ya juyo da ita sannan ya anshi littafin yace happy? Ta kalleshi cikin tsananin farinciki tace alot😊, ya sunkuyo yamata kiss a goshi ya fita, ta dade a tsaye tare da shafa gun kafin ta shiga ciki.

Salman shikanshi a mota ya dade kafin yaja mota, yana isa gidan najib a waje ya tadda shi, bai fita ba najib ne yashigo, salman ya ja mota sukai skul, sai da sukai parking najib ya kalli salman yace yarima gaskita na yarda aure nacanza mutane😁 salman yace bangane ba? Najib yace da ace da ne da gudu zamu shigo muna tada kura amma yanzu baka gudu da mota nakula, ko dan......salman ya kalleshi yace kodan me? Yace ohh ka manta? First had'uwarku da salma ta hanyarne? Salman ya tureshi yace najib na kula kwanan nan gulma ke cinka dayawa, najib yai dariya yace Ango Ango, salma ya bud'e motar tare da ya fita, najib ya kalli kusa da inda salman ya mike ganin littafi da biro yasa shi wani tsananin mamaki, da sauri ya fito, sai dai baiga salman ba, can ya hangoshi yana tafiya, da sauri ya bishi.

Salman sai dayaje kusa da theater d'in dazasuyi lectures ya tsaya, najib ne ya karaso yace kai wasa wasa kana da sauri, salman yace ina zan tsaya ka bayan kana ganin rana ake, najib ya kalleshi yace muje, salman ya kalli hannunshi yace wannan? Da sauri yasa hannu ya fizge, najib yasa dariya yace najib dagaske ne abinda nake zargi? Naka ne littafin? Lalai in nakane da alama za'ai ruwa da kankara, salman yace to parrot sai kai tayi, na matatane menene? Najib ya bud'e baki yace da alama naka ne da gaske😳 u? Littafi? Ha ha ha .

Salman ya makamai littafin akai ya wuce ciki, to ba najib ba salman gani yai kowa na kallansa da sauri ya d'aga rigarsa yasa littafin a ransa yace yazanyi da beauty🤔?.

Fulani zaune tayi shiru, ta kalli farha tace farha ki bani yau zuwa gobe zan samo mana wani plan d'in farha tai kasa dakai, itadai tafara tsoro sai dai salman ne batajin zata iya hakura dashi, farha ta mike tace to fulani Allah yakaimu goben, fulani ce tace farha kirami hindu( baiwar fulani ce) farha tace to, hindu ta iso tare da tsugunnawa, tace gani ranki ya dade, fulani ta kalleta tace kinsanar da ishaq d'in inasan ganinsa? Hindu tai shiru, fulani tace dake nake, hindu tace nafad'a mai amma yace kiyi hakuri bazai samu zuwa ba, kuma bayasa ran har zuwa gobe zai samu dama, fulani ranta ya kara baci,takalli hindu tace fita, hindu tace to dasauri tai waje, fulani ta rike kanta tace ni? Ishaq? Hannunta ta dunkule, aranta tace da alama sai na lalaboshi.

Salman zaune a aji ana lectures, sai dai wayace a hannunsa yana dane_dane, najib yad'an zunguroshi yace yarima bazakai rubutu a littafin love d'in ba? Ga malan nata bayanai? Salman ya ture hannunsa yace kai rubutun kake? Najib yace yanzu nake tunani da alama gobe zan shigo da littafi tunda matar ka ta sa mu😊 salman ya makamai harara, najib yace kawo naku na love ni sai in muki rubutun, salman yace ka manta kana nufin littafin beauty d'in zan baka kamin jagwalgwalon rubutunka? Najib yace ahhh hmmm ayi hakuri, salman ya juya tare da kallan wayarsa jin karar text, dasauri ya bud'e ganin daga salma ne.

NI DA PRINCE  Where stories live. Discover now