Ni Da Prince 30-35

15K 489 15
                                    

*NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄

*NA AYUSHER MOHD*

NO.3⃣0⃣

Atare suka saho, har suka isa part d'insu, sai dai me? Suna shiga falo salma taga wata budurwa zaune tana kallo, mamaki yakamata, budurwar tana ganinsu ta mike da sauri tace yayana......sai dai maganar ta ta tsaya a wuya ganin salma, kallanta ta shiga yi, badai itace matar ba?wannan kyakyawar😳? Salma ma kallanta take, kamar tasan fuskar.

Salman ne ya karasa shigowa tare da cewa yaushe kika zo? Sai alokacin ta d'aure ta kalleshi, cikin sanyin jiki tace d'azu, ganinai baka dawo ba😕.

Salma ta kalleta sannan ta kalli salman tamai alama dakai wace? Murmushi yai sannan yamatsa gun farha yace kefa dadina dake kenan farha, ba hakuri.
Gaban salma ne yafad'I farha? Farha? Farha? Abinda zucuyarta keta maimaitawa kenan, da sauri tai hanyar d'aki, farha ta kalleta tace in_law ku nake jira muyi dinner fa?

Salma ta kalleta sannan ta d'auke kai riga da wando ne a jikinta 'yan kanti sai d'ankwalli data d'aura, salma bata amsa mata ba takara yin hanyar d'aki, salman yace magana take miki fa? Salma ta juyo kamar tai kuka tace ina zuwa, yace alright.

Salma nashiga d'aki ta zauna a gado dabass...ta rike kanta tace nashiga uku, meke faruwa? Can wata zuciyar tace kika sani ko kanwarsa ce uwa_daya uba_daya? Sai a lokacin tai _Hamdala_ sannan ta d'an mari fuskarta kad'an da hannu biyu tace hakane, salma kidaina tunanin komai.

Toilet ta shiga sannan ta fito, suna zaune a dinning farha na kusa da salman, ahankali salma ta karasa tazauna, farha kam ta tsorata dakyan salma sai dai bataso agane.

Har salma takaraso ta zauna idan farha na kanta, daga d'an nesa dasu kad'an taxauna, farha tace in_law kin fito? Salma ta kakaro murmushi tace yp, salman ya kalleta sannan ya d'auke kai, farha ta fara jawo kwanuka tafara zubama salman abinci, salma naxaune na kallam ikon Allah, bayan farha ta gama sai ta bud'e kwanon karashe,tace kai kamar da tafarnuwa, tafad'a tare da d'an d'anawa, dasauri tasha ruwa ta kalli bayin dake gefe tace ke meyasa kuke sawa abincinsa tafarnuwa?salma tace bangane ba? Meye da ita? Bayan magani ce? Farha tace haba in_law yayana fa is allergy to tafarnuwa, jikin salma yai sanyi takalli salman sai dai takasa cewa komai.

Salman ya kalli farha yasaki murmushi yace ya isa, basu sani bane, farha tace nidai akula kar a jama wani abun, in rasa ya zan, salma dake kallan salman tuni ta maida idanta kan farha, cikin tsananin mamaki tace me kika ce? Farha tace bakomai, salman ya kalli salma yace kici abinci, salma dakyar ta zuba sai dai ko loma d'aya takasa ci, farha ta kalli salman tace yayana kasan nima nadainacin tafarnuwa? Yace why? Tace yaxa'ayi inci abinda baka ci☹?

Salma kam ranta yagama b'aci da karfi ta ajiye cukalin dake hannunta, dukansu suka juyo tamike tare da kallansu ko magana bata musu ba tanemi wucewa, tazo saitin salman, yasa hannu ya riko ta, ta tsaya cak,batare da ta juyo ba,idanunta taf kwalla, salman yace kI koma kici abinci,salma ta had'iyi wani abu, ta runtse ido tace na koshi banajin yunwa, salman zai magana farha da kishi ya zo mata wuya tai sarin tasowa ta raba hannunsu ta rike salma tace in_law kici abinci plz? Salma ta fizge hannunta tace nace miki na koshi, ko bakya fahimtar yaren? Tana kainan tai d'aki, farha ta kalli salman tace yayana matarka ta iya fad'a, sannan kamar kuka zatai, an ma.........kafin ta karasa taga salman ya mike, d'akin ya shige ya barta anan.

Salman na shiga ya salma azaune tana kuka, ya kalleta yace ke kuma fa? Dasauri tafara goge hawayenta ta mike zatai toilet da sauri ya jawota jikinsa ya rungume yace menene? Baki da lafiya? Bakin ciki ya kamata wato baimasan meke damunta ba? Salma ta kwace jikinta tace kaina ke ciwo, yace eyya akwai magani a drawer inkin fito kisha, yafad'a tare da juyawa, salma tace ina zaka? Yace gun farha,jitai kamar tasa ihu, tad'aure tace nikam farha ya kuke? Yace oh banfa fad'a miki bako? Cousin d'ina ce,'yar kanwar Abba ce.

NI DA PRINCE  Where stories live. Discover now