Ni da Prince 14

5.6K 349 2
                                    

☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄


*NA AYUSHER MOHD*

NO.1⃣4⃣

Takarasa ta zauna a kujera fuskarnan a hade, najib ya kalleta ya kalli salman yaga shima fuskarnan a hade, yace oh god yad'an matso yace hb prince kad'an saki ranka mana 'yan jarida na kallo fa? Salman ya kakaro murmushin yake, sannan najib yakalli salma itama tad'an kakaro murmushi.

Angama shagali nan aka fara d'aukan hutuna kana ganin salma da salman sai kasan murmushin yake suke a hutunan, bayan an gama 'yan uwanta suka mata sallama suka shiga mota, idanta ne ya ciciko ganin Asabe ta sata a motar da aka kawota sannan takalleta, tace salma kiyi hakuri, ki manta da kamal a ranki, yanzu ke matar wani ce dan haka ki kula da hakkinsa.

Salma ta kalleta hawaye ya fara zubo mata tace Aunty meyasa kuka had'ani da salman? Cike da mamaki Asabe tace me salman din yai? Tace shikenan Aunty a bar maganar, Asabe tace koma dai menene ki rike mijinki, karki kuskura ki wulakantashi.

Salma kam hawaye take ta rike hannun Asabe tace Aunty kicema yaya kamal......dasauri ta katseta tace salma me kike shirin yi? An fa d'aura miki aure, salma tai kasa dakai Asabe tace mun tafi sai munzo, Allah yabaku zaman lafiya.

Salma ta bita da kallo hawaye na tsiyaya a idannunta,salman kam yanacan suna sallama da mutane sai can ya shigo shida kamal, lokacin salma kam ta hade kai da gwiwa tana zuba kuka, jin motsin bude kofa yasa tad'an sai_saita kukan salman yashigo ya zauna.

Nan suka fara tafiya salma kam sai kuka take.
Salman ne ya Kalli salma ta gefen ido dataketa shesheka tsaki yai yace malama dalla kimana shiru kin cikamana kunne, salma tad'ago ta makamai harara, ya juyo yakalleta tare dayin kwafa, najib ya ce salman hakuri zaka bata ba fad'aba.

Salman ya kalleshi ta glass sannan yace ni? Yafad'a tare da nuna kansa, yacigaba ni wai kake nufi? Najib yace eh mana, salman yace over my dead body.
Salma ta d'ago jajjayen idanunta tace kwantar da hankalinka nima I won't let that happen.

Daga nan kowa ya d'auke kai ita ta jingina kanta da window, shikuma yad'au waya.

Najib yace oh god.......

Sun isa gida sai dai a bakin gun sukaga su zeena a tsaye nan suka kama salma sukai ciki da ita, dakinta suka kaita su ka sata a gaba wai sai taci abinci, nan ta daure tad'anci kadan sannan suka mata sallama suka tafi.

Mikewa tai tacire gwagwaron tai alwala tazo tai sallar ish'ai tana zaune agun ta zuba uban tagumi , salman ne ya shigo dakin tare da sallama ta amsa kamar bataso ya shigo ko kallan inda take baiyi ba ya bude drawer yad'au kayan baccinsa yashiga toilet din dakin.

Ruwa ya watsa sannan yasa kayan yana fitowa ya fad'a gadonsa, salma ta kalleshi da mamaki tace malam meye hakan? Ya d'ago yace mefa? Tace anan zaka kwana? Yace da dakinki ne? Tace ba haka nake nufi ba amma tunda nazo nan aka kawoni, yace wannan matsalarkice sai kinemi inda zaki kwana ko ki kwana a kasa, tace what? Yace oho kardai ki kuskura kibar dakin nan dan bayi suna falo in baki kwana anan ba zasu fad'ama fulani dan haka dolene ki dinga kwana a kasa, tace dole? Yace yes kinada jaa ne? Tace mikomin bargo inshimfida a kasan? Yace bargo? Nikuma fa? Tace sai ka yaye bedsheet din ka rufa dashi.

Salman yace kin ma rainan hankali ana sanyin zakice inkwanta na bargo? Ko in ja bedsheet? Ce miki akai zan iya bacci akan katifa zalla? Ran salma ya b'aci tace to ya kakeso inyi? Yace oho miki amma bazanyi abinda kikeso ba salma ta cika tai taf sannan tad'aure tace miko pillow, yace I can't do that dan ni haka nake bacci in kwanta a d'aya in kuma rungume d'aya salma tai tsaki tace u are so selfish tana gama fad'ar haka ta mike tai hanyar kofa, dasauri salman yai dungure ya damko hannunta yace are u crazy? Tace mayb yace naga alama to ina zaki? Tace falo inje in kwana yace baki fahimci abinda nake nufiba kenan😡 tace ina zan fahimta? Yace go back yafad'a yana nuna mata cikin d'akin tace I can't🤔 da karfi yasa hannu ya fincikota yai ciki da ita yasa makulli ya cire makullim yasa a aljihu. Salma ta fizge hannunta tace karka kara tab'ani😠yace ina kika ga jikin daza'a tab'a? Haushi ya isheta kawai tashige toilet, salman yai tsaki yace kawai za'azo a takuramin nida dakina😏 wannan aure ne ko takura🙄?


Nace ba ka tambayeni ba salman katambayi kanka😏.


By Ayusher Mohd📚

November/2013

NI DA PRINCE  Waar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu