Ni da Prince 17

6.1K 333 5
                                    

*NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄


*NA AYUSHER MOHD*

NO.1⃣7⃣

Salman yana fita mota ya fad'a yai hanyar Buk, tafiya yake amma ransa duk a b'ace, inda najib yake ya nufa, a kusa da makarantar Buk yake da zama, najib bad'an kano bane daga bauchi yake, karatune yakawoshi nan.

Salman yai parking din mota ya fito ya nufi d'akin najib, knocking yai najib dake zaune yana kallo yataso ya budemai, cike da mamaki yake kallan salman sai dai kafin ya firta wata kalma salman ya ture hannunsa dake jikin kofa ya wuce cikin d'akin, najib yakalleshi yace Ango? Ya haka? Salman ya fad'a gado tare da d'aukar remote yace waye angon? Najib ya rufe kofar tare da karasowa yace salman bai kamatafa aganka a wajeba yau🤔salman yace tunda kaine ubana ba? Najib yace Allah yabaka hakuri dagaji ranka a b'ace yake, salman yai tsaki tare da canza tasha yace nifa banajin zan iya sati 1 da waccen 'yar rainin hankalin a d'aki d'aya😏 najib yace haba salman meyasa kake hakane? Kasani sarai su ishaq dasaninsu suka tinguno zancen auren nan, plz ka jure mubasu kunya.

Salman yace yarinyarce kanta na rawa tagama rainani, sai kace ni din sa'an tane😠.

Najib yace salman yarinyar nan fa batada laifi ina ganin yanda kake mata, ni naji dad.....salman yakatseshi yace kasan wacece ma wai? Najib yace naji dai Amir yace 'yar skul din mu ce, salman yace kyale banza shi baisan me ake ciki ba sai yaje yana yad'a maganarsu mannir, wannan 'yar rainin hankalin nan cefa mai *Ninja*😏najib yace ninja? Salman yace kaifa banza ne ninja mana basune suke rufe fuskarsu da wani bakin kyalleba? Najib ya kwashe da dariya yace amma prince sai a hankali nikaf din ne ninja? Yace to yarinyar cefa? Najib yace badai wacce nakusan bigewa ina koyon nan ba? Salman ya juya kai yakalli gefe sannan ya ceji baki yace ita fa, najib yace ita😳? To dama ka santa ne? Salman yace dalla malam inazansan wannan kucakar?nifa an cucenI wlh, najib yace amma ta hadu akwai kyau😁.

Ran salman ya b'aci yad'au pillow ya makamai yace cemaka akai kyai shine komai?nan dai sukaita musunsu nikam naja jiki nabar gun😒.

Salma kam ta dade kafin tadawo normal nan ta gyara d'akin dan taga falon har an gyara kafin su fito ankuma sa turaren wuta, bayan tagamane 'yan uwa sukaita zuwa yi mata sallama sai azahar tasamu nutsuwa tai alwala tai sallah, so take ta zaga taga gidan sai dai kunyar hakan takeyi, hakan yasa kawai tazauna a d'aki ganin qur'anI yasa tad'auka tafara karantawa, jitai cikinta na kara tasanI yunwace amma fitina irinta salma taki fita taci.

sai karfe 2;30 hanne ta kwankwasa salma ta bude, tace ranki ya dade ankawo abincin rana tace to tare da mikewa nan tazauna a dinning ganin abinci kala_kala yasa tace hanne abincin ai yai yawa🤔 hanne tacs haka ake kawowa sai dai inkungama sai akwashe, salma ta girgiza kai tace oh nan tafara cin abinci, taci sosai sannan tasha lemo ta koma d'aki.

Hartai isha'I salman bai dawoba hakan yasa ta kwanta a gado ta shige bargo, dan sanyi akeyi, jiya data kwanta a kasa sanyi ya ratsata ga ba bargo, da ciwon jiki ta tash.
Jinta mike akan had'aden gadon d'akin yasa tasaki ajiyar zuciya, takwanta tashiha tunanin masoyinta, da ace tanada waya dako Abba takira taji lafiyar kamal😞 tana tunani bacci mai karfi yai gaba da ita.

Salman sai 11 ya dawo ya shigo, ganin d'akin dulim ba wuta yasa ya kunna, mamaki ne yakamashi ganin salma tai dai_dai akan gadonshi, yakarasa cikin bacin rai yad'au sandarshi ya zunguro ta ta farka cikin razana tare da rike gun, ganin salman yasa ta hade rai tace malam banasan haka, nafad'ama kadaina zungurata salman yai murmurshI 😏yace kinfisan in tab'aki? Dasauri tace karka kuskura ehe😗 yace to mike mai guri yazo ai kin mori gadon, salma kam taji dadin bacci akan gado tace ina zani? Yace inazaki? Inda kike kwana mana🤔tace tab aikam yau bazan yarda ba sai dai kanani pillow da bargo😕salman yace bakya ganewa ko? Yafad'a yana nuna kansa, tace oho ko mezakace baxan yadda insake kwana a kasa ba😠.

Salma yace matsalarkice wannan sannan yad'au rigar dayake bacci da ita ya wuce toilet ta murguda baki tace ai naga alama sai nima nadinga zakewa😠.

Ai naga yanada d'an manner nasan yanda zanyi yaban bargo,
Hijab din sallarta tad'auko tasa a tsakiyar gadon, yana fitowa ya kalleta yace baki sauka ba? Tace oho gashinan na raba mana ni nan bangaren kai nan, salman yai wata dariya yace what? Gadon nawa kika raba harda wani ni nan ke nan? Tace eh sannan kar wanda ya kuskura ya gangaro bangaren d'an uwansa😏 salman yace lalai kin girma dayawa tace da nid'in yarinya ce? Yace kin cire hijab dinnan kin sauko ko kuwa? Tace kazabi d'ayan uku, ko in koma falo na kwanta, ko kaban bargo ko kuma mu kwana a haka😏 salman yakalleta yace in zaba? Tace eh u have to choose a'a bama haka ba u most choose😎....





😳🙊nace lalai salma an zake😜

By Ayusher Mohd📚
[11/13,

NI DA PRINCE  Where stories live. Discover now