Ni da Prince 21

7.2K 352 15
                                    

*NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄


*NA AYUSHER MOHD*

NO.2⃣1⃣

Kallanshi tai tad'anyi murmushi, salman ya wuce toilet itama ta mike ta maida kujerar inda take, bayan salman ya fito ya wuce massalaci itama ta shiga ta d'auro alwala, bayan ta idar da sallah haka kawai tasamu kanta da d'aga hannu sama tana rokarma salman saukin wannan ciwo nashi😰.

Ga mamakinta daya dawo daga massallaci bai koma bacci ba itama hakan yasa ta zauna tare da d'aukan qur'ani, wajen 7 salman ya mike yakalleta yace zan shiga makaranta, salma ta rufe qur'anin tare da kallanshi, tad'an kakaro murmushi tace to, yace do u resent me? Ta kalleshi tace sosai ma☹, yai murmushi tare da wucewa toilet.

Tabi bayanshi da kallo, salman bayan ya fito yad'au kaya ya koma toilet yasa, kananan kaya yasa yayi kyau sosai, salma ta kalleshi tace ka fad'amusu a kawoma abinci ne? Yace nop bana cin abinci da sassafe, tad'an tabe baki tace hmm.

Salman ya dau waya ya fita, takalleshi tace jakar makarantar fa? Yace mezan da ita? Tace au haka ake zuwa? Yai tsaki yace nidai na wuce najib na jirana, takalleshi aranta tace tab.

Mikewa tai tafara kad'e gado, maganin jiya tagani, ta kurama maganin ido, tace ko maganin meye? Ta bud'e drawer ta side_bed ta ajiye zata rufe taga wani karamin album hannu tasa ta jawoshi, ahankali ta bude, hoton wata tagani, suna tsananin kama da salma ga hoton na da ne hakan yasa tai tunanin mahifiyarsa ce, takara budewa hotunan salman ne wanda baifi d'an 20yrs ba alokacin shida wata yarinya, kana ganinsu kasan suna cikin farin ciki, ice cream sukesha, wani gurin kuma suna kan keke, wani kuma suna zaune a kan grass carpet, murmushin dake kan fuskar salman ne ya bata mamaki, bata tab'a ganinshi a cikin farin ciki haka ba, zata bude wani gun taji an fizge album din.

Dasauri ta d'ago, salman ne tsaye ranshi a b'ace yace bincike kikemin in na fita? Dasauri ta mike tace wannan ne bincike? Maganinka naje maidawa nagani, amma wac.....katseta yai tare dacewa bansan tambaya, ya d'au makullin mota daya manta ya fita da album d'in.

Ta bishi da kallo a fili tace wacece ☹? Tadade a zaune haka kawai take tunanin yarinyar, da alama hotunan bama na kasar nan bane, a ina ne? Ganin batada wanda zai bata amsar tambayoyinta yasa ta mike ta cigaba da gyaran d'akin, bayan ta gama tai wanka, ta fito tai breakfast.

Salman kam ya dade a mota rike da album din, idanshi ya kad'a yai ja a hankali ya bude album din ya kalli mahaifiyarsa, sannan ya bude ya kurama budurwar ido, yasa hannunshi akan fuskarta yana shafa, ya dade a haka kafin ya rufe, yaja motarsa.

A falo salma ta zauna tasa kallo, hanne da wata na zaune a kasanta, salma tace hanne ko mu fita nan tsakar gida? Wajen garden d'incan? Hanne tace to ranki ya dade abinda kikeso shizamuyi, ta mike tare da yafa mayafinta suka fito, zamatai a garden tare da littafinta tana karatu.

Ishaq ne yazo wucewa, dama kullum yazo wucewa sai ya leka bangarenta sai dai kullum ba kowa sai bayi, yau kam yayi sa'a yana lekawa yaga salma zaune akan kujera hankalinta gaba d'aya ya tattara akan littafin datake karantawa, kura mata ido yai jiyake kamar yaje ya rungumeta, fadawan dake bayansa ya kalla yace ku tsaya anan, shikuma ya shiga.

Hanne ce ta d'ago jin motsin mutum, ishaq ya kalleta yamata alama da hannu su fita, cikin hanzari suka fita, ishaq ya karaso daf da ita yad'an sukunyo yace Amaryarmu karatu take? Cikin tsananin mamaki ta d'ago tare da saurin mikewa ta matsa baya, salma ta gaidashi, ya amsa tare da cewa Amarya kina lafiya? Yafad'a tare da matsawa, takara matsawa tare da cewa lafiya, amma yarima me kake anan? Ishaq ya tsaya tare da cewa laifine in nazo ganin matar kanina? Yafad'a cikin shagwaba, haushi ya kama salma amma tad'aure tace ayya nagode, zan shiga ciki naga kamar lokacin sallah ya kusa, bata jira mai zaiceba tai saurin wucewa ciki.

Ishaq ya bita da kallo tare da cewa wow yarinyar nan tana kasheni gaskiya👌🏻...


Salma na shiga ciki d'aki ta wuce ta hau kujera tace wannan kuma wani sabon salon fa? Meye namin shagwaba? Tsaki tai tare da cewa ni zaman d'akin ma yafimin😕.

Haka taita zama har tai sallar isha'I, aranta tace wannan rayuwa haka zan d'ingayi? Da yaya kamal na aura nasan bazan kare a haka ba😞 bayan tayi isha'I tana zaune har bacci yafara d'aukanta.

salman ya shigo ganinta a zaune akan kujera tana barci yasa ya karasa inda take ya kalleta, gaskiya tanada kyau, wata zuciyar tafad'amai haka, tuno yanda ta kuladashi jiya yai, tunda yake a duniya jiya shine rana ta farko da wani d'an adam yasan da cutarsa harya kula dashi, hannu yasa ganin kanta yad'an lankwashe garin bacci, salma kam jin kwanciyar ta mata dadi yasa ta cigaba da baccinta.

murmushi yai ganin yanda take baccinta sannan ya kalli hannunsa da fuskarta take kai, wata zuciyar tace ahaka zaka zauna? A tsaye? Harsai ta tashi? Motsin daya d'anyi da hannunsa ne yasa salma ta bude ido da sauri ya zare hannunsa tare dayin gyaran murya, ta mike da sauri tace ka dawo? Ya juya baya yace ke kuma meye hakan?tace mekuma nai daga dawowa? Ya juya yai waje batare dayai magana ba, tace neman a d'auramin laifi dai🤔.



By Ayusher Mohd📚
[11/13

NI DA PRINCE  Where stories live. Discover now