Ni Da Prince 25

6.8K 383 6
                                    

*NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄


*NA AYUSHER MOHD*

NO.2⃣5⃣

Kado ya hau ga mamakinsa duk b'acin ran dake damunsa ya tafi, ahankali yake satan kallanta tana duba wayar.

Salma ta taso tazo kusa dashi ta tsaya tace kamar ba sim a ciki ko? Ya d'an dago tare da jingina a jikin gadon yamata alama da hannu ta zauna a kusa dashi, ahankali ta zauna tare da mikamai wayar, ya amsa yace ina ledar? Ta mike ta d'auko nan ya d'auko sim pack din yasa sim din sannan ya mika mata, ta kalleshi tace bakasamin numberka ba, ya amsa ya samata tare da kallan wayar so yake yaga mezatayi saving din sunan, ganin yana turo kai yasa salma tai dariya tare da rungume wayar, cikin zolaya tace me kake lekawa? Dasauri ya koma inda yake yace me kuwa? Tace me kakeso insa akan sunanka? Yace dama mutum ake tambaya me yakeso? Ta mike tare da dariya tace nama tuna, shima ya mike zaune yace me kika tuno🤔? Tace hmmm yama? Yace what? Tace to ai namanta☹ tafad'a cikin shagwaba, ya koma ya kwanta tarr da cewa bawani nan, tai murmushi tare da zama a shimfidarta azuciyarta tace mezansa? Rude? S?ahh me zansa? Tafad'a tare da rike haba, salman na kallanta yai murmushi tare da juyawa.

Wata idea ce tazo mata kawai tai dialling number salman din, ganin waya ta shigomai kuma new number yasa ya d'ag da mamaki amma baiyi magana ba, salma tai kasa da murya tace hiii🙋🏻, jin muryar mace yasa yace waye? Salma tace is me😉 jin maganar kamar a d'akin yasa ya juyo tai murmushi tare da daga wayar ta jijiga, yace ahh what is this? Tace my no.😀 ya katse tare da sakin murmushi, tace kai saving.

Ta taso a hankali tazo kusa dashi, salman daya kurawa number ido yana tunanin mai zai sa, jin motsin salma yasa ya rubuta Stubborn, salma ta fizgo wayar tace stubborn? Ni din😠 ya mike yace ba haka bane? Tace eh mana yace to yaya ne? Tace bandai sani ba amma banda wannan🤔 tafad'a tare da juya baya, hannu yasa a kugunta yaje juyo da ita ta taho gaba daya, ta fad'a jikinsa, ahankali ta d'ago nan fa suka shiga kallon juna, salman ganin tasa wayar a bayanta yasa yajawota ya rungume sannan yasa d'ayan hannun ya zare wayarsa, ya nuna mata sannan yace me kikeso insa? Tace inza'a sama mutum suna shi ake tambaya? Yai murmushi jin ta kwaikwayeshi, ta mike zata tashi ya rikota yace in baki fad'aba zan bashi a sunan d'azu, tace in kasa sunan d'azu nima zansa duk abinda yazomin arai, ka yarda?ya d'aga gira.

Nan ta mike tare da kwanciya a kasa sai dai takasa bacci, sai juyi take, abubuwan daya faru tsakaninta da salman take tunowa, lumshe ido taja bargo.....ita kanta batasan meke faruwa da ita ba.

Yau saturday hakan yasa salman ba inda zashi da safe bayan sun tashi, kawai yau tasamu kanta dacemai ina kwana? Mamaki ya kamashi a hankali ya amsa tare da cewa duk farin cikin ganin wayar ne? Ta rufe ido tace bafa haka bane☹ yace to naji, ki tashi mu shirya muje asibiti ko? Tace kasanar da sarki dalilin fitarmu ta jiya ne? Yace sai na sanar? Mamaki ya kamata tace kasan fa abinda yafaru jiya, yace to sai me? Zaki fasa zuwa duba mahaifinkine saboda wasu suna kai gulma? Tace ba abinda nake nufi kenan ba amma jiya anma fad'a yau.....yace ke akama? Tace a'a amm...yace ki tashi ki shirya in zaki, in bazaki ba kuma ki zauna, yana kainan yad'au kaya ya shiga toilet,salma ta rike kai tace yazanyi? Number Abba tasa ta kira, kamal ne ya d'aga tace yaya ya jikin Abba? Yace da sauki dan gashima a zaune nan ya mikama Abba suka gaisa, Abba yace basai kinzo ba yau kinga bai kamata daga aure kidinga yawo haka ba tace Abba amma ai yakamata inzo, yace na yafe zuwan, tadaure tace wannan ce numberta Abba kayi saving yace lalai ina murna tace na gode, nan ta kashe wayar.

Salman na fitowa ta kalleshi tanaso tamai magana sai dai ganin ya d'aure fuska yasata tai shiru, mai yashafa yasa turare ya fita falo, tai tsuru a zaune can ta mike tai wanka ta fito falon, yana ganinta yad'an saki rai takaraso dinning ta zauna har suka ci abinci ba wanda yai magana suna gamawa ya shigo d'aki da niyyar d'aukan makuli, salma ta biyoshi,ta tsaya a bayanshi tace dan Allah kabari na tambaya inzamu fita, ya juyo cikin b'acin rai, harzai yi magana ko me ya tuna kawai taga ya fita da sauri, tabi bayanshi da kallo idanta taf da kwalla tace yazanyi😥?

Salman na fita mota ya fad'a yazauna yana tunanin zata fito, salma kam ganin tsayuwar bazata mata amfani ba yasa ta jawo mayafi ta fito da sauri sai dai ba salman a falon ganin haka yasa ta zura takalmi tai waje bayinta suka biyota, da sauri ta bude kofar tsakar gidan zata fito dai_dai nan ishaq ya taho ai kuwa su kai gware baya tai da sauri tare da kallan wa ta bige? Ishaq ne ya d'ago cikin fad'a shima sai dai ganin fuskar daya dade yana bege yasa ya saki ajiyar zuciya, salma tai kasa dakai tace yahkuri yarima ban kula bane, murmushi yai yace are u alright? Tace eh kayi hakuri plz, yace indai bakiji ciwo ba is okay😉, ta d'ago da mamaki ta kalleshi yace yes that's what I hope😊, kasa tai dakai tare da juyawa cikin gida ta turo kofar, hanne tace kinfasa fitar? Tace eh.

Salman ganin ba alamar salma yasa yai waje da gudu ranshi a b'ace, dakin najib ya wuce, yana shiga ya fad'a gado, najib yace prince meya faru? Naga kamar kana kan fire😂.

Salman yace banasan magana yau, najib zaiyi magana wayar salman tai kara ya kalli wayar stubborn ne yafito ajiki, ture wayar yai gefe, najib ya kalleshi yace waye stubborn? Salman yace ina ruwanka? Najib yace don't tell me salma😂? Lalai taci sunnan itama naga ba kanwar lasa bace amma salman stubborn a waya? Lol so childish😜.

Salman yace ina ruwanka? Zan fita daga d'akin nan fa? Najib yace sorry amma kana kallo bazaka d'aga ba? Salman ya kalli wayar harta tsinke, salma takara kira, najib yace salman please, salman yace ba ruwanka malam bakasan metamin ba😠 najib yasa dariya yace har anfara love_ fight hahh lalai prince.

Cikin zafin rai salman ya mike yace love fight? Lalai kaci mutincina nida wa? Najib yace haba salman, cool down meye da zafin ran ko dai haka ne? Kakesan ka waske? Salman ya kwanta tare da juya baya, yanaji salma tai kira na 3, sai dai yaki d'auka itama batasake kira ba.



NI DA PRINCE  Donde viven las historias. Descúbrelo ahora