Ni da prince 11

5.5K 354 1
                                    

☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄


*NA AYUSHER MOHD*

NO.1⃣1⃣

Haka salman yashirya cikin dakakun kayan sarauta da Mai martaba ya aikomai dashi, shi kanshi yasan yayi kyau najib sai kodashi yake, yai dan karamin tsaki yace I wish wannan auran da budurwar danakeso akeyi,amma meye amfanin kwalliyar? Najib yace zaka fara ko? Dan Allah kazo mu wuce, turarensa ya fesa sannan yasa hula da takalmi ya fito cikin kasaitarsa.

Tunda ya fito bayi da 'yan uwa kemai sannu da Allah yasanya alkairi amma kasaita da jin kai irin na salman ba wanda ya amsawa sai najib ne yashiga amsawa.

Yana zuwa hanyar fada wasu bayi sukazo suka kewayeshi yace kun fara ko? Najib yace wad'annan fa? Salman yace ai aiki yaganka dan hakannan zasuyi tabinmu har agama, najib yace lalai kace alamace ta ango ya taho, salman ya juya kai ba tare dayai magana ba.

Guri yacika sosai su Abba kam suna wani guri da aka ware musu, tsoro ya fara kama Abba shikanshi yafara tunanin kodai saida 'yarsa yai?.

Salman haka yai ta ratsawa cikin manyan mutane suna gaisawa, basu dade ba aka shiga huduba ta sallar juma'a, bayan anyi sallah ne aka d'aura auran *SALMAN DA SALMA* akan sadaki dubu hamsin, dan Abba yace sadaki kad'an yafi daraja a aure duk yanda sukaso ko dari abada amma yaki yace hamsin ya isa hakan yasa aka hakura aka bada hamsin.

Salman kam baimasan an d'aura auran ba yana waje suna hira da Amir da Najib sai dayaji masu busa da kirari sun matso kusa dashi sunayi nan fa mutane suka zagayeshi, haushi duk ya isheshi jin wai sunan matar salma, wato salman da salma kenan😡? Inama ace wacce yakeso ne take da wannan sunan kuma sukai aure? Da baisan irin kyautar dazaiyi ba yau.

Najib ne yaja hannun salman yakaishi gunsu Abba, har kasa salman ya tsugunna yagaidasu, Mustafa yace ikon Allah sai yau mukaga sirikin namu, salman yai kasa dakai, Abba yadaure yace salman ko? Nan prince yace eh, Abba yace kada kamanta amana muka baka😊 salman aranshi yace amana🤔? Amma afili sai ya d'aga kai Abba yakaraji yaran ya birgeshi yace Allah yabaku aman lafiya, Najib cikin murna yace Amin.



Salma na tsugunne tana alwala dan baccine ya d'auketa sai da aka tasheta, jin busa a waje da kid'an kalangu yasa mutanen gidan suka shiga sa mayafi suna fita kallo, salma kam abin dake faruwa a gidan sam haushi yake bata, da gudu taga mutane sun shigo suna guda sun tsaya akanta, takarasa d'auraye kafa ta d'ago jitai sunce Alhamdulila an d'aura auran *SALMAH DA SALMAN* jitai gabanta ya yenke ya fad'I cikin rawar murya tace ma naau gud'ar kud'an matsa in wuce, jitai an rungumeta idanta ta rufe kwalla ta zubo mata Asabe tace Alhamdulila salma naji dadi, Allah yakareki daga sharrin makiya.

Ahankali hawaye suka shiga zubo mata ta d'aure tace Aunty sallah zanyi, Asabe tace muje in kaiki nan gida ya kara kaurewa da murna zee ma ta iso, sai dai ganin kawarta a wannan hali yasa jikinta yai sanyi.


Wajen karfe 6 na yamma Asabe da goggo sun zauna sai gyara amarya sukeyi, dakyar suka lalabata tai shiru har zee tasamu damar yi mata kwalliya, motocin d'aukar amarya suna waje, dan wasu yan zumudin harsun shige.

Lifaya ce aka nad'a mata wacce Matar mustafa dakanta ta siyo mata mai tsadar gaske tayi kyau sosai acikin orange din lifayar, ga zee ta mata kwalliya, tasha sarka da d'ankunne silver hakama takalmin kafarta.
Sai kamshin humra da turaren wuta takeyi.

Bayan sun gamane suka kaita d'akin Abba Tana zaune kusa dashi, Abba yace salma? Tace naam yace kiyi hakuri kinji? Tace Abba kadaina bani hakuri, yace naga salman a gaskiya ya kwantamin tai murmushin yake yace kuje mutane na jira gashi naji ance jarfe 8 akwaI abinda za'ayi acan tace umm...

Nan suka mike ta kalli umma datai kasa dakai, kusa da ita taje tare da cewa Umma natafi d'agowa umma tai idanta yai jaa tace Allah yabada zaman lafiya salma bata amsa ba tai waje da sauri jin kuka zai kubce mata.

Zee ce a gefenta sai Asabe dake kusa da ita sunzo fita kofa salma tasa kai shima yasa kai aikam suka gwari juna, zee tace sannu sannan ta d'ago tace malam la.......cikin wata irin murya salma taji ance mekuke nufi da nad'e mata kai? Dasauri ta yaye mayafin da aka rufeta tad'ago jikinta ne yashiga rawa ahankali tafara ja da baya tana girgiza kai wasu hawayen bakin ciki na zubo mata.

Asabe ta d'aure tace meye hakan kuma? Tafad'a tana kallan mai maganar? Yace Aunty ni...
Asabe ta katseshi bamu hanya nace?
Yace Aunty..
Takara katseshi
tace ka bamu hanya ko?

Ahankali ya matsa idanshi taf kwalla Asabe ta fizgo hannun salma da karfi tafara janta sun zo fita kawai ya kama d'ayan hannun salma yace salma haka alkawari yace? Dama akwai ranar dazaki wuce gidan wani namiji bani ba? Takalleshi a zabure hawaye yakeyi shima runtse idanta tai dakarfe batasan sanda kuka ya kufce mata ba, yace isowata kenan ko gidan banjeba nace dan taxi yakawoni infara ganinki amma me? Sai infara ganin motoci, sannan in ganki kinfito da sufar amarya wacce za'a kai gidan wani? Salma mekeke shirin aikatawa rayuwar mu? Girgiza kai kawai take cikin matsanancin kuka tace Yaya *KAMAL* na shiga uku........yaxanyi?



Hmmmmmmm babar magana inji kawata koxali🤔


By Ayusher Mohd📚

NI DA PRINCE  Where stories live. Discover now