Ni Da Prince 9

5.8K 348 8
                                    

☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄

*NA AYUSHER MOHD*

NO.9⃣

Wanka salma ta shiga bayan tagama komai ta shirya cikin less d'inta na sallah haka kawai ta kosa taga bakon da Abbanta yake magana.

Salman ma ya shirya cikin kayansu na sarauta shida bawanshi suka fito dakuma driver, su biyu suna gaba shikuma yana baya rike da waya yana dane_dane, sam bai kula da inda suke shigaba dan driver dashi akazo ganin gidan tun farkon zancen auran, salman jin ana jugub_jugub a mota yasa ya dago kai, cikim tsananin mamaki yake kallan dan lokon da suke shiga, cike da mamaki ya kalli driver nasa yasa mamman ina kake kaini? Yace yalab'ai kayi hakuri mun kusa zuwa, cikin b'acin rai yace Mun kusa zuwa ina😡? Mamman yace gidan matar taka, salman da sauri ya juya baya tacikin glass yana kara kallan unguwar yace anan unguwar take? Yace eh tare dayin parking awani karamin gida salman yace me kenan? Yace an iso ga gidan nan, ya nuna wani karamin gida mai kofa karama salman yashiga yin wata dariya mai karfi, wanda hakan yasa suka razana bawan yace Ranka ya dade menene?salman yace bakuda hankali ne kuka kawoni nan? Mamman yace yallabai ai.....da karfi salman ya katsesu yace kuyi gaggawar fitar dani daga unguwarnan kafin kwalara takamani, mamman yace yallabai bakaga matar taka ba ai, yace wace mata kuma? Nace ku fita dani ko? Bawan yace to yallabai amma bari in ajiye mata sakon da sarki yabada yace aikin banza, ka fita ka kaimata inyaso ka taho daga baya yace yahkri yallabai ajiyewa kawai zanyi intaho yace komadai meye to kayi saurin dawowa inka wuce minti 5 tafiya zamuyi dasauri yace to yallabai.

Boot din motar ya bude ya dauko manyan jakukuna guda 3 ya nufi gidan ya kwankwasa ciki sauri salma ta bude, sanye take da hijab amma batasa nikaf ba, kallanta tare da sakin baki, tadaure ganin kayan fadawa ajikinsa tace sannu? cikin in_in na yacs yauwa dan Allah hajiya salma nanan? Tadan kalleshi da mamaki tace nice salma tafad'a tare da nuna kanta, yace hmm gashi ance inkawo miki tace ni kuma? Yace eh kiyi hakuri ya shirya zuwa kuma sai wani uzuri yataso mai, tace wafa🤔?Zaiyi magana yaji anmai horn dasauri yajuya yace eh, tabishi da kallo tare da cewa shine bakon Abban? Sai kuma ta d'an daga kafada tare da kallan waje can taga motar ta kulle tad'au jakukunan ta shiga ciki tare da ajiyewa a falon Abba takoma d'aki ta kwanta, tunani take me katin bikin nan yake nufi?


Bafaden kam na shiga mota yai ajiyar zuciya tare da cewa kai yallabai kayi sa'a wannan ita kad'ai ma kyanta ai ya isa ka wuni kana kallanta, salman ko kallanshi bai ba asari ma ranshi ne yakara b'aci.

Sanda yana yaro mahaifiyarsa ta rasu, matan babansa basanshi sukeba haka 'yan uwansa, sannan yanzu matar dazai aurama maimakon abarshi yasamu wacce zataso shi shima yasota amma sai abashi auran kara buta? Lalai zai d'au mataki bayan auran nan.

Salma kam duk abin duniya ya dameta tanajin motsin Abba ta mike da sauri taje ta gaidashi ya amsa tare da cewa kinga bakon? Tace eh wani bafadene yace wanda zaizo din wani uzuri ya hanashi zuwa, Abba yace toh😳? Yaza'ai haka? Tace gashi wanda yazo ya ajiye, Abba yace toh da alama uzurin mai karfine tunda ansanar dani ya fito daga gida, salma tace Abba katin can kamar na biki, Abba yace salma matso nan ta matso kusa dashi tana murmushi yace ki nutsu zan fad'a miki wata magana mai tace to Abba.

Yace dani da yayana mun yanke hukunci yi miki aure tad'ago da mamaki tace aure kuma? Yace nasanki salma yarinyace mai biyayya kadaki bani kunya, idanta ya ciko da kwalla tace Abba yaya kamal fa? Yace salma kibar zancen kamal dan mahaifinshine yafara ansar maganar auran, tai shiru zuciyarta sai bigawa take, yace wannan juma'ar za'ayi yini da d'aurin aure da daddare akaiki saidai bansan koda wani abu dazakuyi keda kawayenki ba, tace Abba juma'a?yace eh salma kada ki manta ni mahaifin kene bazan tabayin abinda zai cutar dake ba sannan inaji ajikina auran nan alheri ne.

Hawaye take sosai yace salma Allah yamiki albarka ta runtse idanta da karfi meke shirin faruwa da ita? Mafarkin datai dama na rabuwa da kamal ne?😭😭.

Abba yace bazaki tambayi sunan mijin ba? Tace basai naji ba Abba tunda kun amince dashi ai shikenan yai murmushi tausayinta yakeji sosai.

Mikewa tai tashiga d'aki ta hau kuka, umma najinta amma batako shigo dakin ba ga batare suka dawo da goggo ba ta dawo ba.

Yau laraba gida ya fara cika salma kam na kwance ba lafiya sai dai hakan baisa an daina hidima ba, tun safe aka kwashi 'yan uwan umma da Abba suka tafi gidan mustafa acan za'a anshi lefe.

By Ayusher Mohd📚

NI DA PRINCE  Where stories live. Discover now