Ni da Prince 12

5.9K 347 7
                                    

☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄


*NA AYUSHER MOHD*

NO.1⃣2⃣

Asabe kam da sauri ta juya tai d'akin Abba dan sanar me.

Kamal yakaraso da sauri ya rungumeta kuka take sosai yace salma bazai yiwu ba, u are mine, muje gunsu Abban susan yanda......jin muryar mustafa sukai cikin zafin rai yace wani irin sabon iskanci ne wannan kamal😡? Dasauri salma ta janye jikinta, ya cigaba baka da hankaline? Matar wani kake rungumewa? Kamal yace Dady wai me kake fad'a haka? Yaza'ayi salma tazama matar wani bayan ni?dai_dai nan su Abba da goggo da Asabe suka karaso gun, mustafa yace bayan kai? Kai wa? Cike da mamaki kamal yakalli dadynsa zaiyi magana mustafa ya katse shi dacewa, kad'auka mudun shashashu ne? Tun yaushe ka gama karatu? Kamal yakalli salma sannan ya kalli Abban salma ya maida idanshi kan dady yace dady amma......

Mustafa yace banasan iskancin banza, dan kaga yarinya nasanka shine kadinga raina mata hankali daga kace saura 3wks ku gama sai ka kara cemata 2wks itakuma saboda shirme da yarda dakai yasa take d'auka, to bari kaji nasani sarai kafi 8month dagama makaranta dan wa'inda kwankwaso ya biya muku tare tuni suka dawo, ko sai kai kad'ane karage?

Kamal yakalli salma zaiyi magana, tsugunawa tai da sauri tace wayyo ni😭 Mustafa yakalleta sannan yakalli Abba yace Amadu dagata dakanka ka kaita mota dan 'yan daukarta sun gaji da jira yakalli kamal sannan yace to yaya, tare da karasowa ya d'agata.

Idanta ya rufe da kuka kawai sa kafa takeyi, dasauri kamal ya karaso kusa da ita yai kneel down yace salma please😥 mustafa yace Amadu ku wuce nace, cikin sanyin jiki da tausayin kamal Abba ya wuce da salma mota.

Motocine guda 20 tata tana tsakiya nan akasata mutane harda makota ganin motar bilis yasa suka shiga😜.

Salma kam zaune take a cikin mota tai kasa dakai banda kuka ba abinda takeyi zee ma kukan take dan tasan yanda salma kesan kamal, Asabe kam rungume salma tai tafara lallashi sai dai kamar zigata take.


Sun isa gidan sarki salma batamasan ina sukeyi ba tadai ji sun yi parking.
'Yan uwa na gidan sarki sun fito taryarsu, nan aka yan Rakiyar bangaren salma, ita kuma su zainab suka riketa sukai bangaren fulani da ita, zee da Asabe na biye dasu.

Sai da suka kaita duka bangaren matan sannan suka maidata bangarenta, yan rakiya sun rikice da kallo ganin irin dukiyar da aka zuba a bangaren, falone kato da kofofi uku, d'aya daki ne a cikinsa da bandaki a d'akin nan ne master bedroom, sai kuma dayar kofar da kuma daki ne da toilet aciki, sai d'ayan kitchen ne kato duk da bawani girki sukeyi ba amma anyishi ko akwai abinda zaisa ai girki aciki.

Baban dakin aka kaita tanaji mutane nata wasa kayan gidan amma ita ko kallan dakin ma batai ba bare, hawaye sai gudu suke a fuskarta, wata baiwa ce ta shigo tace wai ance duk ku fito za'a wuce, sukace amarya bata shirya ba ai, baiwar tace eh ita yanzu za'a shirya ta zasu taho dashi.

Nan suka fara fita, akabar salma ita kad'ai, kifa kanta tai tana kuka yanzu shikenan an rabata da yaya kamal? Wacce irin rayuwa zatai?jin sallama tai dasauri ta zauna tare da gyara mayafinta zeena ce da wasu mutane guda 2, zeena ta yaye mata mayafi aranta tace masha Allah sannan tace salma yanaga idanki a haka? Wani irin kuka kikai haka? Salma ta kakaro murmushi tare dayin kasa dakai.
wata daga cikin matan tace hb Amarya yanzu ai an daina irin wannan kukan, zeena ta kalli d'ayar tace Meema Yaza'ayi? Tace gata so cute I wish bata b'ata fuskarta haka ba amma ba matsala zeena tace tnx.

Nan meema ta matso ta yaye ma salma mayafin gaba daya ta zare d'ankwalin kanta, itakanta zeena sai datai mamakin gashin kanta, ahankali meema tashiga yima salma kwalliya sun d'au lokaci kafin su gama sai dai me? Duk wanda yaga salma to ba karya sai ya kara kallanta tayi kyau na garari....

Zeena ta shiga fasama meema kai, nan suka d'auko wani ratsatsen kaya wanda kyansa ya wuce tunanin mutum, dark blue ne sai kwalliyar jikinta da akai da golden rigar doguwa ce, ta baya jan kasa takeyi, nan aka d'aura mata gwagwaronta dark blue sannan aka yafa mata wani shara_sharan net golden, aka miko mata takalmi mai d'an tsini golden.
Salma tayi kyau na karshe sai dai bata farin ciki sam.

Zeena tace kai Amaryarmu karfa kisa kanina ya fad'I garin kallanki nan sukai murmushi salma kam ta juya kai.

Nan suka ce mu mun wuce yanzu salman Zai zo ku tafi, nan suka fita suna murmushi.

Salma na zaune tana tunanin rayuwa ita dake tunanin auranta da kamal sai gata a gidan wani can da bata sani ba, sannan tace a fili wai ahaka suke nufi zanje? Da wannan net din? Tasaki tsaki daidai nan salman yashigo ko salama baiba dan duk ranshi a b'ace yake da akace wai shi zaizo ya d'auketa.

A bakin kofa yatsaya yace ke! Salma taki d'agowa yakaracewa ke! Takara kim d'agowa haushi ya isheshi yakaraso kusa da ita tana kallan kafarsa na tahowa duk da a tsorace take amma bazata yarda yace mata ke ba jitai ansa sanda a tabo mata kafad'a da mamaki tad'ago dan ganin wannan rainin hankalin.

*tofah*🙄

Nan idanun ma'auratan ya hadu cikin tsananin mamaki mara misaltuwa salma ta mike tace *YOU?* salman yakalleta ba laifi kyanta ya wuce misali sai dai kamar yasanta, jikin salma ya shiga bari? Tad'aure tace me kake anan Prince? Yace oh kinsani dama? Tace ohhh baka ganeni ba? Wace ka cima mutunci a Buk? Me kazoyi nan? Ko nan din ma biyoni kai? Salman yai wata dariya mai karfi wacce tasa zuciyar salma tagama tsinkewa, sai daya gama sannan yace *SALMA*?

Da mamaki ta kalleshi tace eh meye? Yakara dariya sannan kuma ya hade rai kamar zaki yace kina nufin kece matar? Ta kalleshi batare data amsa ba yace yar gidan Amadu u are really something, wato sai da kikasan yanda kikai kika aureni ko? Sai dai kuma I really pity you dan tun daga yau zaki fara regretting yar gidan masu gini.

Salma tunda taji yace wai auranshi jikinta yafara rawa, zama tai a gadon dabas tace kai ne mijin😳? Yace ke banasan pretending din banza, zatai magana ringing din wayarshi ya katseta yad'aga.
Najib ne yace to ango wato anga mata shine aka ahanyani a mota ko? Salman yakalli salma yace u will be really surprise inka ganta, najib yace to please kazo mutafI yaya zainab sai waya take, salman yace ok gamunan.

Salma yakalla yace ke taso muje tace amma....ya katseta banasan wani munafirci taso muje, tace munafirci kuma? Yashareta tace wai da wannan mayafin zani? Yai tsaki yace ke bansan iskanci inkinga dama ki fito, yanakai nan yafara tafiya, itama tsakin tai tare da binshi, ya kalleta kawai yai kwafa yaga alama sai ya mata service😜😜😜😜



By Ayusher Mohd📚

NI DA PRINCE  Where stories live. Discover now