Ni da Prince 16

5.8K 364 0
                                    

*NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄


*NA AYUSHER MOHD*

NO.1⃣6⃣

Mayafin kalar kayan tad'auko sannan tasa takalmi flat ta fito falon, salman na zaune a dinning kuyangi na tsaye a bayansa, ta karasa gun cikin nutsuwa.

Kuyangin ne suka gaisheta a tare ta amsa tare da zama a falon, salman yai gyaran murya da alama magana yakesan yi salma ta mannamai, yasake yi hakan yasa tad'an dago yamata alama da fuska akan tazo taci abinci, ta juya kai tace nakoshi in ka gama mu wuce, ya d'aga kafad'a alamar ruwanta sannan ya kammala tare da mikewa yai hanyar waje, salma ta mike tare dayin tsaki tace mutum sai girman kai ai yacemin in taso😠, ta mike hanne da wata baiwar nabinta a baya salman tagani tsaye a waje takarasa nan bayi maza suka rufo musu baya, salman yad'aga kai sama mutane na gaisheshi amma ga mamaki salma ko amsawa bayayi.

Sai da suka kusa isa fadar sarki, salman ya matso daf da ita yace u have to be careful dan karki kuskura ki bari wani a cikin gidan nan yasan irin zaman da muke, mark my word.

Salma ta d'ago ta kalleshi gabanta ne ke fad'uwa tadaure tace sai ka fad'amin😗? Bai bata amsa ba ya cigaba da tafiya, sun isa fadar nan aka musu iso, bayan sun shiga salman ya tsuguna itama ta tsugunna nan suka gaida sarki ya amsa cikin farin ciki, nan 'yan fada suka fita suka barsu, sarki yakalli salma yai murmushi lalai yama d'anshi zabi mai kyau dan yarinyar ta kwantamai, yamaida idansa kan salman yace salman ina tsananin farin cikin wannan auran dan Allah ka rike yarinyarnan amana, kaji? Salman yai kasa dakai yace insha Allahu Abba, salma ta kalleshi ta gefen ido tace sai kace gaske ji yanda yakoma innocent😏.

Sarki yace jeka waje salman inasan magana da sirikata salman ya d'ago tare da kallan salma sannan ya mike yai waje, sarki ya kalli salma yace 'yata matso, cikin kunya salma ta matsa kad'an sarki yace salma agaskiya ba yaba da yanda kike Allah yasa abinda nagani hakan yake, tai kasa dakai batare datace komai ba, yace salma dan Allah ki rike yaron can da mutunci ki kula dashi, yaro ne maraya he is so lonely, salma tad'an dago idanta maraya? Ta maimaita aranta yace eh salma maraya ne mamaki ya kamata ya akai yasan abinda ke ranta? Sarki yakatse tunaninta dacewa Allah yabaku zaman lafiya tai kasa da kai batace komai ba, yace jeki salma ta mike tare damai sallama.

Tana fita ta saki ajiyar zuciya tare da dubawa ko zataga salman, sai dai ba alamarsa, hannece ta karaso tace ranki ya dade muje inkin gama, salma har zatai magana sai kuma ta fasa tace muje.

Part dinta suka koma hanne tace sai gobe zaku gaidasu fulani tace to tare da shiga ciki, daki ta koma ga mamakinta salman taganI zaune yasa earphone a kunnensa haushi yakamata ko kallansa batai ba ta karasa kan karamar kujerar d'akin ta zauna tare da kifa kanta ajikin kujerar, tunanin rayuwarsu da kamal tafara, yanda yasota yakuma kula da ita, dashi ta aura tasan da sunanan suna diga luv💖 amma gata yau ta auri wanda kallansa batasan yi shima haka.

Tunaninta yayi zurfi batasan sanda hawaye yafara zubo mata ba, muryar salman taji da alama waya yake, jitai yace kai fa dan iska ne najib ni kakema zancen wata amarya? Bataji mai akaceba sai jiganI tai yad'an kalleta sannan yace kai har kana tunanin akwai wata 'ya mace daxanyi lokacin ta? Ni ai a tarihin rayuwata ba mace kaima kasani, ganin yanda salman yai shiru daga ji magana ake sai jitai yace banda lokacinka sannan zancen lokaci kuma mu zuba mugani, yana kainan ya katse wayar sannan yakalli salma yace ke kuma meye na kallona ina magana? Tace mezan kalla? Yace banasan kallo gwara ki sani, haushi ya isheta dama a wuya take tace malam nifa nagaji da bakaken maganganunka salman nifa nasan nafika san rashin auren nan dan ni inada wanda nake so kaifa? Bana tunanin kasan me kalmar so take nufi, sannan.....dasauri ya katseta yace kinada magana ne? Tace ai maganar nakeyi yanzu😡 yace banjiba ko zaki maimaita😏? Bakin ciki ne yazoma salma wuya tarasa mema zatace kawai ta harareshi tare da cewa haka maraya yake?I thought mara uwa ba haka suke ba? Cikin hanzari taga salman ya sauko idanunsa ya kad'a yai jaa yakaraso inda take ya fizgota daga kan kujera sannan ya matseta a jikin bango, idanta ta runtse da karfi, ko miyau takasa yad'iya salman cikin zafin rai da wata irin murya yace *WHAT DO U KNOW*? Jikin salma yafara rawa, salman ya kara matse mata hannu har saidatai karamin kara yace *HOW DARE U TALK TO ME LIKE THAT?* I can tolerate anything but don't u dare to say something like that😡..
Salma kam jikinta rawa kawai yake yana gama fad'ar haka ya saketa tare da d'aukan makullin mota yabar dakin, idanta na rufe sai dataji ya bugo kofa da karfi sannan ta bude ido a hankali jikinta har a lokacin bai daina rawa ba ta kalli hannunta dake mata zafi, ganin guntai yayi jaa dakyar ta furzar da wata iska sannan ta tsugunna tare da rike kanta, tace me nace da ranshi ya b'aci haka? Ahankali hawaye yafara zubo mata tace yaya kamal yazanyi?


Nima kaina jikina rawa yake ganin salma acikin wannan yanayin📚
[11/13, 10:23]

NI DA PRINCE  Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang