Ni Da Prince 29

7.1K 362 3
                                    

☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄


*NA AYUSHER MOHD*

NO.2⃣9⃣

Salman ciki kid'ima yai hanyar airport gudu kawai yakeyi, yana isa ya shiga kiran farha a gigice sai dayai kira 2 ana ukun tad'aga tace yayana har nayi fishi, salman yace farha? Dariya tai tace yayana kana ina? Nan ya mata kwatance.

Sanye take da riga da wando na 'yan kanti, sai dai rigar takai gwiwa, tayane kanta da bakin mayafi karami, jakar dake jikinta irin doguwarnan ce itama black sai takalmi flat akafarta black,tana jan trolley d'Inta.

Karasowa tai inda salman yamata kwatance, daga d'an nesa ta hangoshi tasaki murmushi tare da karasowa, sai datazo daf dashi ta ajiye trolley d'in tayi d'age tasa hannu ta rufemai ido, salman yai ajiyar zuciya tare da zare hannun ya juyo a sukwane, tofa kallon juna suka shiga yi, farha ta rufe idanta tace yaya wannan kallon fa? Salman yai gyaran murya yace farha? Kece? Dama zan ganki? Ta turo baki tace ba wani nan bayan kamanta dani?☹ tai maganar cikin shagwaba, salman yace wasa kike kema kinsan I can't, tace nasani yayana kaima kasani ai ko? Tafad'a tana kallansa, yai murmushi yace ina nasani ko mazan paris sun mantar dake ni🤔.

Tace su sun isa? Yace waya sani, atare sukai dariya yace muje mota ko? Ta kalli akwatinta sannan ta kalleshi, yace hmm badai ni akeson ind'au jakar ba? Tace yayana nifa mace ce☹kallanta yai ya wucewarsa mota, takalleshi tare da jan jakarta tace har yanzu dai halin nanan.

A baya tasa jakar sannan ta bude gaba ta shiga, farha ta kalleshi tace yayana how many years?yace hmm 4 ko? Tace ahh gaskiya mun dade ko? Yai murmushi yace sosai ma, hannu tasa takamo nashi tace yaya kasan meyasa nazo? Ya kalleta yace a'a, tace yaya jinai inban gankaba akwanakin nan kila mutuwa zanyi😪 salman yace haba farha meyasa kike fad'an haka? Tace yaya bakasan yanda nakeji ba, gashi narasa dalili dana ma mum maganar zuwa hanani tai, yace y? Yace cemin tai wai ko kayi aure😄ta d'auka zan yanda in hakura da zuwa, salman ya kalleta yace gaskiya tafad'a farha, cikin tsananin mamaki tace what?me kake nufi da hakan? Bai bata amsa ba yaja motar yace gida ko? Tace eh amma....ganin ya d'auke kai yasa kawai tasa kuka, daurewa kawai yake dan sam bayasan kuka, ganin yanda take shesheka yasa kawai yai parking ya kalleta yace farha?dasauri ta matso ta rungumeshi, janyeta yad'anyi sannan ya miko mata tissue yace bansan kukan nan kinsani sarai, bari in fita inkin gama sai inshigo, yafad'a tare da mikewa zai fita, dasauri tajawo hannunsa tace nadaina, karka fita plz.

Yakalleta sannan ya shafa gefen fuskarta yace yauwa farha, kallanta tai tace yaya amma......yace farha please karkibatan rai bayan inajin farincikin ganinki, tace cewa fa zan kasai min icecream😰murmushi yai yasan waskewa tai amma sai yace bari muje a siya.

Haka farha taita sashi yawo daga tace ka za sai tace ka za har suka kai 5 sannan sukai gida.

Farha kanwar matar sarkice wato mahaifin salman, lokacin salman na 10yrs Abbansa yakaishi paris gun kanwarsa bayan mahaifiyar salman din ta rasu, anan suka kulla wata muguwar soyayya da shakuwa tsakaninsa da farha, sai dai Abba yabada umarnin gaggawa akan salman ya dawo gida, wannan dalilin yasa salman ya rabu da farha kuma bai karasa karatunshi daya fara acan ba.

Salma kam na zaune sai kallan waya take amma sam bataga salman ya kira ba, kamal dake zaune yana mata magana sam batasan me yake cewa ba kawai dai tanacewa eh, ganin hankalinta ba'a kansa yake ba yasa yafit, Abbane ya kwalla mata kira dasauri ta mike ta karasa gunshi.

Abba yakalleta yace salma dare yafarayi kinga ankusa kiran magriba, ki kira salman kiji, tace to Abba.

D'akinta tashiga tare da kiran wayarsa, sai dai har kira uku tai bai d'aga ba kuma bai kira ba, zama tai taredayin shiru tace ina ya shiga?

Salman kam shiya raka farha gun fulani, nan akasa aka gyara mata d'akin dazata zauna, tajashi tace yarakata d'akin nan suka shiga taitamai zance sam yamanta da d'auko salma ga wayarsa na kan madubin farha,a silent take, sarai ta kula da wayar na haske amma ita batasan salman ya tafi, hakan yasa ta juya wayar.

Sai da salman ya mike zashi masallacin jin kiran sallar magrib yad'au wayarsa missed call din daya gani na salma ne yasa ya kalli farha yace farha am sry bari inje indawo, takalleshi da shagwaba tace yayana yaushe rabon mu hadu? Ina laifin kai sallah a nan? Ya kalleta kamar baisan metake nufi ba yace zanje mosque daganan zanje wani guri, ta mike tace yaya ina kuma? Nifa yau so nak........ga mamakinta bata karasa maganarta ba taga ya fita.

Salman kam yana fita ya kira wayar salma,itakam hartagaji da mitar goggo na tazo ta tafi, ganin kiran salman yasa ta mike da sauri ta d'aga, salman yace kinjini shiru ko? Tace wani abun ne ya tsare ka? Yai murmushi yace ganinan zuwa, kafin tai magana ya katse, ta girgiza kai sannan tai murmushi, goggo tace shi ne? Salma tace eh gashinan, goggo tace ah to gwara dai, dan naga akwai wata yarinya a garinmu daga zuwa ganin gida mijin bai kara komawa ba sai takarda tagani, salma tace shi ai ba haka yake ba😒goggo tace iye? Lalai su bera, salma ta juya zatai d'aki ganin kamal tai a tsaye da alama yaji me suka ce ta, dasauri tai d'aki.


Salman ya iso ya kira salma tafito, kamal na kallanta kamar yai kuka sai dai ba yanda zaiyi, salma ta shiga mota ta kalli salman tace irin wannan jirgawa?ya juya yace don't tell me harkin gaji da ganin gidan kinaso ki tafi naki🤔? Dasauri tace bafa haka nake nufi ba nufina ba kira🙄.

Wata sansanyar dariya yai yace abinda na dade bangani ba yau nagani shiyasa na sha'afa, duk da gaban salma ya fad'I amma tadaure tace da alama wannan abun nada matsayi, salman yace ehm sosai,yafad'a yana kallanta, ta bata rai tace mutum ne?yace eh, cikin tsoro tace mace?kallanta yai yace lawyer kika koma? Tace bahaka bane yanda kai maganar ne ai☹yace hmm.



By Ayusher Mohd📚

NI DA PRINCE  Donde viven las historias. Descúbrelo ahora