Ni da prince 10

5.9K 340 2
                                    

☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄


*NA AYUSHER MOHD*

NO.1⃣0⃣

Salman zaune a gaban sarki, mai martaba yace za'a kwashe kayan bangarenka a sake wasu ko kana bukatar wani abun? Salman yace a'a duk yanda kuka gani, sarki yace inafatan kaje gun yarinyar kaji ko tana bukatar wani abun na biki? Salman yaji gabansa ya fad'I amma yad'aure yace tace bata bukatar komaI, sarki yace zancen banza kenan kai bakasan kawaici ba? Ko kataba ganin inda amarya tace bata bukatar kudi? Salman yai kasa dakai yace zan aika mata wani abun, sarki yace dakanka zaka koma, salman yadaure yace to Abba.


Lefen da aka kai sai daya tsorata duk yan uwan dasukaje, mamakin irin kayan da aka zuba suke, kamar ba'a talauci a duniya? Kanwar maman salma kam kasa jurewa tai tace kai JAMA'A kayan nan ai sunyi yawa, zainab tace haba hajiya bakomai ai nan kowa yashiga jinjina wa salma lalai kam tagama warkewa, dan gidan sarki? Hmmm.

Zeena kam zaune kawai take amma sam ranta badadi yama za'ayi ace salman guda a aura masa yarinyar da iyayenta basufi bayin gidansu ba😡 nan suka ajiye kudin dinkin amarya dana kwalliya, dubu dari biyu mamaki yakama mutane nan aka shiga gulma daga gani Abba saida 'yarsa yai inba haka ba wannan kudi da kaya haka? Shiyasa ma bikin ba'a wani ja shi ba, sudai 'yan kawo lefe nan suka tafi suma suna gulma.

A gidan akabar kayan dan kamwar maman salma tace in aka kai kayan can gulma yawa zatai, nan suka debi d'inkakun kaya a karamar jaka suka fita.

Salma na kwance zazzabin jikinta yafara raguwar dan bacci ya d'auketa taji guda a saitin kunnenta da sauri ta mike a zabure, dangin mamanta ne suke guda, wata daga cikinsu tace kai yarinya tayi goshi irin wannan al'amura haka? Salma kam kallansu kawai takeyi Asabe kanwar mamansu tace tashi kiyi wanka dalla kinwani zauna kamar wacce za'a kaita gidan marii, salma tace nifa.....Asabe tace so kike kibamu kunya?kin tashi ko sai na miki wanka dakaina? Salma ta mike tare da turo baki tai waje, nan aka shiga guda.

Suna zaune ita da kawayenta 'yan uwa, sun sata agaba suna tsokana idanta duk ya cika da kwalla, Asabe tazo tace wai ma taci abinci? Sukace anya kuwa? Nan ta kama hannun salma tai dakin umma da ita tasa aka siyo maltina da madarar ruwa ta juye a kofi tace kafa kai? Salma tace nifa banajin yunwa☹ tace kin kafa kai kosai na mareki? Nan salma ta amsa tana sha tana kuka inta tuno kamal sai taji kamar ta kwalla ihu.

Ran Alhamis da safe gida ya cika taf salma na kwance zazzabi yadawo sabo, jin gobe za'a d'aura aure kuma akaita, wank yaro ne yai sallama yace wai ana sallama da salma, Asabe ta shigo d'akin tace tashi kiji inaji angon ne salma ta hade rai takuma ki tashi, asabe tace kin tashi ko kuwa? Salma ta mike ta yayimi hijabin sallarta ta zura tai waje Asabe na kiranta amma ina hartakai kofa, zuciyarta taf take da masifa, sai dai me? Tana zuwa taga wannan bafaden na rannan, yana ganinta ya zube a kasa yashiga jera gaisuwa ita abin ma mamaki ya bata dakyar tace menene hakan? Yana tsugunne ya miko mata envelope takalleshi tace namiye? Yace aikoni akai inkawo miki, tace inji wa fa? Yace mai gidana, tace ina nasanshi?yace wanda zaki aurafa? Sai yanzu ta gane, haushi ya isheta tai tsaki tace kamaidamai kudinsa kace bana bukatar wannan, in yanaso ya birgeni to ya......tunowa tai dakalmar mahaifinta dayace nasani bazaki bani kunya ba, idanta ya ciko da kwalla tace ka maidamai kudinsa bana bukata tana fad'a tai ciki da sauri.


Tana shiga kowa ya shiga kallanta ana tsokana, wato dan rashin hakuri shida za'a kaimasa ke gobe shine sai daya aiko aga lafiyarki?haushi ya kamata ko kulasu batai ba tai d'aki ta shiga bargo tasaki kuka.

Salma kam hidimarsa yake kamar ba aurensa za'ayi ba su Amir ma abakin mannir sukaji zancen auren.

Yau juma'a tun safe gida ya cika makil, salma kam tana d'akin goggo a kwance, Abba ne ya shigo tana kwance idanta duk ya kumbura, ahankali yakalleta tare da zama kusa da ita.

Idanunta ta bude ganin Abba yasa ta kakaro murmushi tace Abba, tafad'a ta a kokarin mikewa hannu yasa a kafad'arta yace yi kwanciyarki salma, ta kwanta tare da yin shiru, yace salma ni najamiki ciwon nan ko? Tace a'a Abba, yace nasani salma kiyi hakuri laifinane dana bari yaya ya amsa tun farkon maganar, dasauri tace haba Abba ai nasan dan kun isa danine yasa kuka amsa, yace to meya saki zazzabi? Aranta tace ko mijin fa bansani ba? Nadaisan yana da hadi da gidan saraura tunda taji 'yan uwa nazancen, sai kuma bafaden nan data gani, amma afili tace cutace kawai, Abba yace salma Allah yamiki Albarka, da izinin Allab bazakiyi danasanin wannan auran ba, tai murmushi tare da cewa yaya kamal ya sani? Abba yace ai kamal sam ko babansa yakirashi baya d'agawa bamusan me yake tunani ba, tai shiru.....

Abba yace da daddare za'a kaiki nasani ke yarinyace tagari amma gidan dazaki sai kinyi hakuri, tace wani iri ne? Yacr gidan sarauta tad'an juya kai kodai d'an gidan waziri zata aura? Abba dakanshi yasa aka kawo mata koko da kosai taci.


Auren in anyi sallar juma'a ne hakan yasa Massallacin gidan sarki ya cika taf da mutane, manyan mutane na sarauta da kuma na milki.

Salman na kwance a d'aki yana sharar baccinsa, sai nemanshi akeyi, najib ne ya shigo dakin kamar wasa dan baiyi tunanin zai ganshi anan ba,mamaki ya kamashi ganin salman daI_dai akan gado yana bacci karasawa yai kusa dashi tare da tabashi, cikin abin bacci salman ya bude ido, Najib yace prince me kakeyi hakan? Salman yace don't u see? Najib yace anacan ana nemanka amma kana nan kana bacci😳? Salman yace oh!!! Lokacin auran nasu yayi ne? Yafad'a tare da duba agoggon bango na d'akin, najib yace auransu ko auranka? Salman yai tsaki yace ni wannan shirman auran badamuna yai ba yarinyarce koma wacece kawai ina tausayinta, sannan ina tausayin kaina dan za'asani sharing din daki da wata kucaka😡 ko dayake servant zansamu, Najib yace salman kasan me kake fad'a kuwa? Yace malam kyaleni, najib yace naji amma tashi ka shirya kafin ran mai martaba ya baci, salman ya mike yasaki kwafa irin ta muguntarnan.




By Ayusher Mohd📚

NI DA PRINCE  Where stories live. Discover now