Ni Da Prince 6

5.7K 360 2
                                    

☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄


*NA AYUSHER MOHD*

NO.6⃣

Kuka sosai takeyi yi abinda ya kara tunzurata umma na zaune a waje tana goge kubewa amma ko ta tambayeta, ta dade tana kuka ganin ba mai lalasarta yasa ta mike tare da fitowa tad'au kwandam wanka tai toilet umma ta bita da kallo.

Qur'ani ta d'auko tashiga karantawa ahankali tafara jin sanyi na ziyarta zuciyarta, jin motsin Abba yasa ta fito da sauri takarasa tare da mai sannu da zuwa yai murmushi tare da cewa 'yar Abba meya sami idanunki? Tai kasa dakai yakamo hannunta yace muje inji matsalar 'yata tunda duk gidan ba mutanen da zasu tambayeki.

A falo suka zauna yace menene salma? Tace Abba aran wayarka nakira yaya kamal yace to naji amma fad'amin menene? Tace bakomai Abba banajin dadi ne, yace ayya sannu ko muje asibiti? Tace A'a Abba naji sauki yace to sannu sannan yamika mata wayarsa ta amsa tare da mikewa tabar falon.

D'aki tashiga tareda yima kamal flashing sau 6 tamai amma abin haushi bai biyoba, daga baya tai deciding ta kirashi sai dai shima no answer tadanyi tsaki tace kila yana wanI sabgar ne☹.....nace hmmm.

Ishaq ne zaune gaban sarki, sarki ya kalleshi yace nasani ishaq kaimesan d'an uwankane, ishaq yai kasa dakai cikin sanyin murya yace Abba yazamuyi da matsalar yarinyar daya kora daga makaranta? Abin na damuna😞, gashi mutane an fara gulmar abin ina tsoron kar hakan yajama salman tsana daga mutane😕.

Sarki yace ni kaina abin na damuna amma bari insa akira waziri inji yazamuyi, ishaq yai murmushi😏 ba b'ata lokaci sarki yasa akira waziri nan ishaq yafad'amai abinda ke faruwa.

Waziri yai shiru can yace yarinyar ya take? Ishaq ya shiga yin bayani akan binciken dayasa ayi akan salma da kyawawan halin yarinyar, waziri ya nisa yace mezai hana muyi haka? Sarki yace me? Mu nunama mutane bawai korarta yasa akai ba dalili ba matar dazai aurace yakesan abata lokacin shirye shirye tahakan ne kowa zaisan salman ba mutum ne mara mutunci ba mai wulakanta mace, sarki yai shiru yana tunani.

Ishaq kam baiso ba amma saboda san ya wulakanta salman jin yarinyar 'yar talakace ba jinin sarauta ba ko 'yar masu kudi yasa yace waziri ka kawo shawara Abba ya kagani? Sarki yace kasa a kara bincike akanta waziri banaso salman ya auri matar da bazata rufamai asiri ba waziri yace to ranka ya dade angama, ya mike yai waje.

Salman kam yau weekend bacci yake sosai sai azahar yai wanka ya fito, al'adar gidan ne aje gaida duk matan gidan da ranar asabar hakan yasa salman ya fito bangaren hajiya karama(Amarya)yafara zuwa, bawani shiri sukeba gaisawa kawai sukai ya mike ya fita ta bishi da harara itakam gadarar yaron na bata haushi gashi ita d'anta namiji shekararashi 7😠.

Bangaren Hajiya babba yaje(ta tsakiya) sun gaisa cikin sakin fuska sannan ya fito saidai yasani itama ba sanshi takeba.

Yakarasa bangaren fulani itakam yasan halinta sarai amma ita gani take baisan komai ba cikin farinciki tasa aka damomai fura tace salman sha fura dan musamman saboda kai nasa aka dama yai murmushi yace nagode fulani tace sai kace wani bare? Kaifa d'ana ne yace haka ne😏.

Bayan ya fito yakoma d'akinshi ya kwanta tare da runtse ido kaf 'yan gidan yasani 'yan uwansa mata 2 ne kesansa kuma sunyi aure sai yara dabasusan rayuwar gidan ba.

Shima kuma kallan kowa yake tunda haryau bai manta abinda sukai mai ba yana yaro har sarkin kuwa☹.


By Ayusher Mohd📚

NI DA PRINCE  Where stories live. Discover now