Ni da Prince 13

5.5K 368 4
                                    

*NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄


*NA AYUSHER MOHD*

NO.1⃣3⃣

Tafe suke yana gaba tana baya, har suka isa kusa da motar najib ya fito da sauri yanacewa Amarya ansha kanshi, salma ta hade rai dan tagane shi, najib yace hmm salman Amaryarmu bata magana ne? Salman yai tsaki yace kaifa banza ne kamar bakasan munafircin wasu matan ba, najib yai saurin kauda maganar tare da cewa bismillah Ango ya budema Amarya kofa dan gimbiya ce😊

Salman yace wa? Nizan bude mata? Salma tace nima ban nema ba😏 ta zagaya ta d'aya bangaren ta bude ta shiga tare da rufo kofar da karfi.

Salman ya kalli najib yace zakasha mamaki inkasan wacece najib yace naga itama ba sauki🤔 daga haduwa harkun fara fad'a? Da alama dai kunsan juna.

Salman yace abar maganar shiga mutafi yafara kokarin bude gidan gaba najib yace yada haka? Ai a kusa da ita zaka zauna salman yace dalili? Najib yace naga an d'aura auran? Salman ganin baisan doguwar magana yasa kawai ya bude baya ya shiga, salma ta juyo ta makamai harara, yace ke wa kike harara? Tace wanda ya tsargu tafada tare da juyawa tana kallan window.

Salman yad'auko waya yana dannawa, najib kam sai lekensu yake ta glass yana mamaki koda ace salman baisan yarinyar amma kyanta ai ya isa yasa yasota, shi jiyake inama za'amai auran dolen indai zai sami irin salma😜.

Ba wanda yasake magana acikinsu sai najib dakebin wakar Aashiqui dake tashi a cikin motar, salma kam tunanin duniya ya d'auru akanta jitake kamar duk duniya ba wanda aka tsana kamar ita.

A hankali najib yai parking, salman yace nifa natsani irin wannan gun na hayaniya😏najib yace haba salman ka hana ayi komai yanzu d'an dinner din ma bazaka bari ayi lafiya ba?salman Ya kalli salma dake cikin duniyar tunani yace ke tamai shiru yakara cewa ke limamiya! Ta juyo cikin bacin rai ta bugamai wani kallo kuma taki d'auke idanta, mamaki yakama salma yace ke who are u staring at? Tace in baxaka kirani da sunan da aka rad'amin ba kabarshi ya matso daf da ita har tanajin saukar numfashinsa akan fuskarta ya kai bakinsa saitin kunnenta dasauri najib yafita, salma kam numfashinta ne ya tsaya cak!! Salman yai wani murmushi yace how dare u talk to me like that? Dakyar numfashin salma yad'awo tad'aure tad'an turashi tace meye hakan? Yai murmushi yace u have to be careful bakomai nake d'auke ba.

Yana fad'ar haka yai waje ta sauke wani numfashi tace wannan wani irin mutum ne? Najib ne ya kwankwasa mata glass a hankali ta zuru kafa ta fito, najib yace salman ku tafi atare plz? Yace kace ta matso, najib yace kid'an matsa ta matsa kusa dashi, najib yace dan Allah ku tafi a tare, salma ta kalli najib tace kacemai karyai sauri, salman yai wani murmushi wato tafi karfin tamai magana, itama aranta tace kaji ko da dadi.

Ahankali suka fara tafiya sunje shiga aka ce su tsaya nan 'yan yara da akama anko suka zo suka tsaya a gabansu kuyangi kuma suka fara zuba flower ahankali suke tafiya har suka isa masaukinsu.

Abin ya kayatar da mutane ganin shima salman light blue din shadda, mutane sun yaba kyan salma sosai,ga salman ma ba bayaba abun nasu chakwas😜

Sukansu 'yan uwanta dabadan sunsan itace Amarya ba da bazasu yadda salma bace ganin kyan datai.

Anfara gudanar da shirye_shiryen da aka tanadar anyi gada, anyi kid'an gwarya sannan yan busa da kalangu, sai kuma DJ.

DJ ya kira Amarya da Ango tsakiyar fili, sai dai duk maganar dayakeyi daga salma har salman ba wanda yake kokarin tashi, ganin haka yasa najib yazo kusa da salman yace hb salman so kake ka bamu kunya? Yai tsaki yace toshi Dj din cemai akai yakirani? Najib yace kayi hakuri plz, salman yace to kace ta taso, najib yakalli salma dake daf dashi yai murmushi shikanshi yasan ma'auratan kowa ba sauki amma yazaiyI? Haka ya juya yace Amarya kitashi kuje, salma tace kacemai yafara mikewa ai shine namiji😗 Salman yakalleta tad'auke kanta ganin mutane na kallansu ga dj ya saki murya sai kiransu yake yasa ya mike, ahankali itama ta mike suka nufi tsakiyar fili.

Suna tsaye mutane sai barnar kudi suke suna musu liki, salma kam mamaki take sai kace takarda? Suna tsaye har dj yace su koma gunsu, ahankali suka fara tafiya zasu koma, tsautsayi yasa takalmin salma ya turgude tai baya luu zata fadi, da sauri salman yasa hannu ya tarota, nan suka kalli juna salman yace Will u stop pretending?dasauri ta mike tare da matsawa kad'an, ranta duk a b'ace.

Nan mutane suka shiga tafi abin ya burgesu......

Nace hmmm

By Ayusher Mohd

11/2013

NI DA PRINCE  حيث تعيش القصص. اكتشف الآن