chapter 2

1.9K 121 0
                                    

😭SANADI NE😭

~F.O.W~

~vote@wattpadkhairi_muhd~

  

             0⃣2⃣

"hawaye ne masu dumi suka zubo mata a kuncin ta."

"kawo ta nan ana ta magana za a ga yarinya kin kama kin rukunkume, ae kuka yanzu kika fara yin sa kuka ba."

"ta fice da jaririyar tana sababi, ya sunan er?"

"RABI'ATU"

Allah raya rabi "

"amin"

"aka ci suna aka watse aka bar me jego da maganganu bakake."

💗💗💗💗💗💗

"tafiya tay tafiya kwana ya zamo sati, sati ya zama wata ,wata ya zamo shekara haka  rayuwar hauwa da rabi ta kasance har shekaru goma sha uku babu labarin mahaifin hauwa'u."

"tafe take tana tauna aya a hannun ta dankwalin ta a kugun ta a daure, ta na rike da bokiti a hannu kawarta a gefe ladi suna tafe suna tsale2 a hanya suka debo ruwa a tuka2 suka dau hanyan zuwa gida."

   "yahane ta tankade ta da gangan , ruwanta ya zube ta soma mata gwallo da dariya da ihu."

"rabi ta kullu ta ce ke yahne bana san wulakanci da rashin kunya ji yadda kika tunkube ni ruwa na ya zube kuma kina mun gwallo da ihu."

"anyi din , me zaki iya shegiya"

"rabi ta saki ayar hannun ta ba ayi aune ba ta hau ruwan cikin ta tana surfa mata naushi a baki da hanci yahane tana ihu."

"mata suka fito kofar gida, wani matashi ne ya rabasu"

"wallahi in kika kumd ce mun shegiya sai na cire miki hakora akuya kawai daba "

"yahane na kuka aka shiga cikin gidan su da ita."

"rabi ma na kuka ta shigan nasu ta fada kasa tana birgima "

"da ta kula ba wanda ya kula ta se ta saki kukan da karfi da ihu."

"umman ta fito da sauri da mairo suka fara tambayan ta me ya faru ta ke wannan kukan."

"umma wai ina *baba nah?*

"ba na hanaki tambayata ba?"

"to ni mesa za a ki nunan babana ? kowa da baban sa a garin nan se a dinga ce mun shegiya mara uba mara asali?"

" *umma wai banda asali? waye mahaifina?*"

"hawaye suka zubo ma umman ta ce rabi'a mahaifin ki mutumin kirki ne , me tausayi ne , nasan akwai dalilin da yasa ya nesanta kansa damu."

"ke kulu tausayin me? kirkin me? ya gudu ya barku keda er taki ? ke mahaifin ki mugu ne macuci ne da cikin ki ya gudu ya bar mahaifiyar ki har yau shekara goma sha uku be waywaye ku ba."

"YAYA me sa kike fadar haka ? "

"to yaya ne? fada mun yaya ne?"

"yaya nasan wani uzurin ne ya tsaida shi"

"uzuri? ke baki ma da hankali kulu baki da tunani har yanzu kina da bakin tare wa umaru? kina da bakin kare shi? to idan mafarki kike ki farka ki tashi ki bude idanun ki kuma ki nutsu umaru mugu ne yayi amfani da damar sa ya yaudare ki ya barki da ya. ke kuma rabi zagi da gori yanzu aka fara miki shi ehe se ki shirya ki tarbe shi uban ki ne ya jawo miki!"

"umman da rabi suka saki kuka a tare suna rike da juna hakika SANADI NE haduwa ta da umaru.!"

"umma ta da gaske baba na guduwa yayi?"

"baki ta kulle mata ta ce ya isa kar na kuma ji."

"tashi maza kije ki hado mana icce muje mu hada sanwa"

"to umma."

  SANADI NEWhere stories live. Discover now