chapter 13

1.2K 69 1
                                    

😭SANADI NE!😭

KHAIRAT UP

F.O.W

vote @wattpad khairi_muhd

~13~

"washe gari en sannu da zuwa suka dinga zarya ba wai a zahirin sannu da zuwan suka zo ba aa sun zo ne dan ganin dangin rabi. kuma sun gamsu dan kuwa suna kama da rabi da umaru sossai aka dinga cewa oh ikon Allah, dama masu kudi ne kai maganganu dai iri2 haka aka dinga fadar su."

"wata kawar mairo ce dai ta jihadi ta ce to ina hi umarun yake?."

"Rabi ta ce zaki goya sa ne ?"

"o'o ni fa ba da wani abu na tambaya ba dama kawai ina san sanin ko yana da rai..."

"to yana da rai garau yake a kasar waje yake da zama an fada miki komai shi kennan?."

"um daga tambaya se cibi ya zama kari? Allah baki hakuri sai anjima kulu. "

"to mu jima lafiya mun gode."

"haka ta tafi tana sababi a hanya."

"Umma ta ma rabi fada kar ta kuma tanka ma maganar su. "

" ta ce to. "

"da yamma su khadyjat suka takura wa rabi ta zagaya dasu garin su hakan aka yi suka sha abaya masu kyau suka yi rolling aka fantsama ganin kauye."

"duk da cewa nasreen a turai ta tashi mahaifiyar ta bata yarda ta yi wani shigar banza ba dogwayen riguna masu kyau da tsari take sawa, in ko ta sa wando pencil to rigar zata kai gwiwa kuma ta sa boy friend jacket a kai me dogon hannu ta daure da belt, ta kuma yi irin rolling din nan tamkar hijabi haka ce shigar ta . nasreen fara ce sol tana da gashi dan daidai tana da hanci siririya ce tana da kokari ga biyayya bata da girman kai kwata2 ita kam kuma sun yi arabi a can ba boko kawai ba."

"bayan fitar en matan ne kulu ta labarta ma dan'uwan ta komai duk da yaji ba dadi dake shi babba ne sai yace da ita"

"kulu idan rai ya baci hankali baze gushe ba ban ce umaru ya kyauta ba kuma bance ina goyan bayan sa ba amma ae kin san ita rabi diyar shi ce? "

"haka ne ta fada"

"madala, kuma amanar sa dole ki nusar da ita muhimamanci da girma na mahaifi, ki nuna mata su iyaye gaba suke da kowa kuma ba a fushi dasu bata isa ba bata kai ba kuma ba dabi'ar musulmi ta gari ba ce"

"haka yake yaya."

"dole ki nuna mata dolen dai da shi uban nata zata yi ado ba da mu ba yadda Allah ya ce uwa ya fadi uba ko wanne a bishi. (wa ummuhi wa abbi) bata da hurumin kin sa da dangin sa saboda haka zata koma da en uwan ta ke kuma zan aura miki wani ki shimfida sabuwar rayuwa me tsafta da inganci ki manta baya ki manta da duk wani abu da ya faru a baya shi Allah me yafiya ne kuma yana san masu yafiya ki yafe masa abunda ya miki ki cigaba a rayuwar ki kema dama na kyale ki ne dan naga an samu dangin rabi kuma alhamdulilahi tunda an samu ni zan sama miki miji kiyi aure ki yi ibada kamar ko wacce ya mace a gidan auran ta."

"zuwa nan kuka kulu take jin zata rabu da er ta tilo wadda suka shaqu suka saba da juna."

"ni bazan takura miki ba ko na nuna miki iko ko kuma kiyi tunanin cewa na gaji da ciyar daku ne aa ba haka bane DARAJAR KI nake san kwato miki ita ma rabi DARAJAR TA dangin ta taje ta saba dasu ta zauna dasu duk tsiya zata na zuwa gun mu babu wanda ze kuma daga kan sa ya mata gorin uba ko asali kin fahimta ko?"

"na gane kuma da yardar Allah zan kasance me biyayya a gare ka dan banda kowa sama da kai yadda ka ce haka za a yi"

"nagode da hakan shi komai kika gani a rayuwa me wuce wa ne kuma SANADI NE kinga zuwan sa garin nan SANADI NE kuma SANADIN rabo ne , rabon kuma na auran ki da kuma samun zuri'a dake wato SANADIN rabon rabi! hakuri za a yi kawai."

"haka ne yaya zan yi kokarin yin yadda ka ce dani."

"shi kenan kije Allah ya shige mana gaba.!"

"Amin"
"su rabi kuwa na can suna zaga gari har wasu samari suka biyo su suma su uku sun sha gayu 🤣 irin na en kauye an kafa hula ana ta dagawa za a gun en mata kyawawa."

"salamu alaikum"

"wa'alaikum salam"

"en mata ku dan bamu aron lokacin ku zamu yi magana daku"

"nasreen ta bushe da dariya ta ce wa rabi haka ake dama a garin ku? ji hular wancan kamaan za a zuba wake a ciki ni dai pls spare me nayi gaba ae se a mun dariya in na ma tsaya da wannan harda su kwalli🤣 "

"khadyjat tana murmushi ta ce nas ae shi mutum daraja ne da shi me abun dariya a nan kowa da inda ya taso da abunda ya nakalta ba a raina dan'adam dan kuma baka san inda ze taimake ka ba a duniya kin gane ko?"

"ta tabe baki ta ce yeah"

"samarin sun ji dadin yadda khady ta kare su dan su din a garin en mata rububin su suke suna san su kula su saboda wankan su wanda yau suka raina wankan a gun nas."

_(dama haka ne abincin wani gubar wani)_

"bayin Allah kuyi hakuri dan Allah mu ba en garin nan bane se anjima"

"mun gode muma"

"nas ta ce am um nima ku min hakuri"

"ba komai ae"

"nagode"

"youwa se anjiman ku"

"haka suka koma gida suna nas nasiha ta ce taji."

"da daddare ne kulu ta kira diyar ta soron gidan ta shimfida masu tabarma suka zauna."

"umma yau kuma soro ake son zama?"

"eh man ana bukatar canji ae"

"eh haka ne kam"

"Rabi"

"na'am"

"magana nake so muyi dake ta nutsuwa"

"to umma ta"

"Rabi kin kasance me biyayya a gare ni, me hakuri a al'amuran ta me kuma dauke kai. rabi ita rayuwa dukanin ta na dan lokaci ne sannan ni ban baki tarbiyar da zaki raina na gaba dake ba, ballanta na kuma mahaifin ki wanda yay silar ki zuwa duniyar gaba daya, nasan be kyauta mana ba amma har ga Allah ni na yafe masa duniya da lahira kuma kema ina umartar ki da ki koma gare sa ki yafe masa saboda iyaye ba abun wasa bane kuma su din sun kai sun kuma isa ba a isa ay fushi dasu ba."

"umma na hakura na yafe masa in dai zaki farin ciki da hakan."

"😊 murmushin jindadi tayi ta cigaba uhm rabi ni yanzu na sauke nauyin da yake kaina ma'ana na hada ki da dangin ki alhamdulilah nima nan da en kwanaki zan yi auren na tare a gida na, saboda haka ina miki umarni da komawa gidan mahaifin ki dn nima zan bude sabon shafi a rayuwata na sauke nauyi na dan na hada ki da dangin ki."

" a matukar rude da tashin hankali ta saki kuka ta rungume umman ta ta tana kuka ta na cewa umma na yarda zan biki gidan auran naki amma kada ki raba ni da kan ki umma da ke ta taso, na saba, na rayu ban taba yin nesa dake ba umma bazan iya tafiya na barki ba umma ta ki sake mun wani umarnin banda na rabuwa da ke umma ta 😭😭"

"ita ma umman hawayen take yi ta ce rabi'a rabuwa ta zama dole amma bata har abada ba keda zaki dinga zuwa ganina akai2 me a ciki gata nake miki fa nima ba so nake ba amma hakan ya zama dole"

"innallilahi wa 'illahir rajun ta dinga fada tana hawaye"

"Umma ta ki..."

_yawan comment dinku yawan shafi da posting!_

  SANADI NEWhere stories live. Discover now