sanadi ne

912 61 0
                                    

Nasreen dai ta sha mita da jin zagin daddyn su ta mummyn tayi bata ce komai ba kar a hada da ita.

Haka ta gama wunin ta da daddare yah muhd ya zo ya dauke ta suka rankaya gidan su.

A garin abuja kam sabon shafin soyayya aka bude tsakanin rabi da makyn nan nan yake ds ita da abunda yake cikin ta haka ma ita ma.

Kullum se sunyi waya da en'uwan su da su umma da hajiya amina.

Watan su biyu a abuja umma ta sambalo mata kanne en biyu duk maza masha Allah daddy da kan sa ya turo mata hotunan jariran a watsaap tmkr tay tsuntsuwa taje kano haka take ji.

Yaran sak abban su, ana saura kwana uku suna ya barta tje kano da sharadin washe garin suna zata dawo tace ta amince.

Tunda taje ta manne en kannen ta a kirjinta tna jin wani irin dadi a ranta yau ga kannen ta uwa daya uba daya ,har kwalla tayi umman na mata dariya.

En kauyen su suka zo ana gobe suna bangaren mummy aka dinga saukar bski kai kace ba a taba yi ma alh.umar haihuwa ba.

Aka kawo raguna biyu da sa guda aka yi yanka dasu, abinci kan ksla kala aka yo daga waje Friedrice,tuwo,masa,spageeti,kaji,nama,harda sy fura ga surveniers da aka raba me dauke da memo da biro da jaka dauke d hotunan jariran ga snacks a ciki ,

Ai ko an sha magaganu dangin su umma an ga sabon abu harda masu kukan dadi umman ma nayi tana godewa Allah bata manta sanda ta haifi rabi sunan ma da yaya aka yi shi ana ta habaice2 yau ga ikon allah.

Yara suka ci suna
Muhammad kabir
Muhammad adnan.

Mummy data ga hotunan yaran da daddy da na umman mu har kukan bakin ciki seda tayi ta sha labarin irin shagalin da aka yi a gun kawarta.

Barni haka kawata barni kar zuciyata ta buga na mutu sabida bakin cikin omaru.

Anyi suya kowa ya koma gidn sa ranan da zata taho ne ta gama shab pics da kannen ta d umman ta da daddy  su dasu nasreen yah khusan ya bugo waya aysha ta haihu yanzun nan ta samu mace, aka nufi asibiti,ana  murna nan aka ce musu en biyu ma fa sun sauka kar kaso kaga familyn nan nan  baki yaki rufuwa.

Washe gari ma nasreen ta haifo dan ta namiji sak yah muhd

Makyn ya mata rada a kunne
Saura mu my life

Murmusa masa kawai nayi.

Anyi shagalin suna sossai duk rana daya aka yi sunan jariran hudu

Amina (minal)
Umar(faruk)
Ahmad(daddy)
Ummukulsum (khulsum).

   Mummy ta raina kanta ran sunan nan dan taga wariya gub dangin daddy ta cika fam kamar ta fashe kuka kam ta sha shi tamkar ba gobe yadds taga umman mu da haj.amina suna wadaka a gun taron seta tsRgu ta raina kanta ta koma tamkar er gayya tun kan a tashi ta tafi se nema ta en uwa ta Sukeyi suka yi suka rasa.

  SANADI NEOn viuen les histories. Descobreix ara