SANADI NE ;14

1.3K 88 0
                                    

😭SANADI NE😭

KHAIRAT UP

F.O.W

    vote@wattpad khairi_muhd

             14

"ummata ki sauya mun wani umarnin dan Allah, rabuwa da ke tamkar rabuwa da rai na ne ki tausaya mun kar na karance cikin maraici!"

         "baza ki taba zama a cikin maraici ba hajja ta muna san ki muna kaunar ki Allah ya sani tun a ran farko da na ganki ban kyamace ki ba,kuma ban wulakanta ki ba saboda haduwar jini tsakani na da ke! ki yarda da kaddara kowa da yadda Allah yake tsara masa rayuwar sa ni zaki zauna a guri  na koda gun umar ne bazaki ba."

       "a hankali ta kalli hajiya amina ta ce nima ina son ku ina kaunar ku zan zauna daku saboda kun mana hallaci."

"alhamdulilah! suka fada a tare. cike da murna suka bar gun da kuma yanke shawarar tafiya gobe."

"hajiya taso ta taushi umma a kan ta yarda ta koma wa auran umar sedai ta tuna da cewa umar fa baya santa er sa kawai yake so gwamma ta barta ta yi rayuwar ta me dadi ta manta da baya."

"umma ba dan tana so ba zata rabu da er ta ,kuma badan ta daina san umaru bane yasa zata yi aure sedan ta lura ya mata nisa kuma baya santa. in ta tuna kalmar ita din ba kalar sa bace ba sai ta zubda hawayenta."

"washe gari da misalin karfe sha biyun rana suka bar garin katsina cike da kewa tsakanin 'ya da uwa wato(umma da rabi)"

*KANO*

"Shigar yamma suka yi ma garin kano (tumbin giwa) kai tsaye gidan su hajiya ta sa aka sauke su kuma ta ci sa'a abbi din su ma na nan koda suka shiga falon dattawan na zaune a kan carpet a zaune gaban su zagaye da kayan marmari suna tadi a tsakanin su."

"salamu alaikum"
     wa 'alaikum salam"
"aminatu kece da daddare"
"nice hajja barkan ku da dare"

"barkan mu daga ina haka na ganki da yaran ki ice dai lafiya?"

"lafiya lau hajja"

"to madala, ah 'a wace wannan tamkar NASREEN?"

"murmusawa tay ta ce ae dama jira nake naga ko wayanan idanun naki har yanzu da kwarin su ko kuma kina kwarar abbin mu ne na dawo da zama tunda ke kin zama tsohon hannu"

"(hahaha) aka sa dariya gaba daya"

"ta mata dakuma amshi naki"

"ba komi ae ni nasan kishi ne dan ni sabuwar jini ce kar nake ko abbiluv?"

"haka ne my reeyn saukar yaushe?"

"am 6days back"

"ha ke da wa fa?"

"da daddy mana"

"UMAR?"

"eh man be zo ba?"

"no"

"to i dunno why be zo ba."

"ok"

"hajiya ta ce hajja , abbi, da magana na zo fa"

"to lafiya?"

"eh lafiya ga me sunan ki (rabi) na kawo miki a karo na biyu a matsayin jikar ki jinin umar!"

"ke aminatu bamu fahimta ba ganar damu?"

"hajja wato shekarun baya da suka wuce har umar ya bar gida... tiryan2n ta fada masu komai daga biri har wutsiya!"

"cike da mamaki su abbie suke kallon amina tamkar wata sabuwar aba a gun su ran hajja ya kai kololuwar 'baci da kuma tashi kira mun umar din."
"Babu 'bata lokaci hajiya ta kira umar ashe ma yana kusa da gidan da azama ya amsa ya zo gidan wani sanyin dadi yaji ya ziyarce shi da yaga rabi a gidan mahaifan sa."

  SANADI NEWhere stories live. Discover now