farewell

997 71 1
                                    

😭SANADI NE😭

KHAIRAT UP

F.O.W

  Vote @wattpad khairi_muhd

*_ina me baku hakuri a kan page mistake da aka samu memakon na sa 27 nasa 26 am relli sorry._*

   

          28

"cike da shasheka ta ce yah makyn please ka fitar mun a d'aki dan kai ma ban san ganin ka ni ba abun wasan ku bace da zaku na yin gare2 dani am not a toy ku bar ni kada kayi depriving right dina na yin kuka ba tunda dai hawayen nawa ne , kuma idanun nawa ne ba dukiyar ku bace kuma baku isa da hana mun zubda hawayen ba."

"mamakin kansa da ita kanta yake dama tana magana har haka, dama bata da kunya, ashe dama yana da hakuri haka?, wata zuciyar ta ce masa ba laifin ka bane so ne. to ae idan ma na barta ban cika namiji ba. ya kamata na nuna mata ni ne mijin, ni nake auran ta, ni zan juya ta ba ita ba,kuma ni zan sa ta tayi abu dole , ta kuma rubutawa kanta cewa ni ba sakaran namiji bane *i love her and i will take care of her i'll once again teach her how to luv me and trust me once again.* "

    _gefan ta ya zauna ya juyo da ita tana fusge2 a fusace kuma da karfi ya jawo ta jikin sa suna jin numfashin juna idanun su suka sarke cikin na juna nata yay ja dan kuka shi kuma tsabar bacin rai kusan 3min idanun su suka yi locking na juna, da kyar ya hadiyi yawu hade da kuma matso ta jikin sa tamkar ze maida ta cikin sa ko zasu hade su koma abu guda. da kyar yayi blinking idan sa ya ce muryar sa na rawa, uhm *sweetheart* ta wani daka masa harara, be tsaya ba ya cigaba na sani na miki laifi na boye miki kaina na ? amma Allah ne sheda ina da dalili, ina jin cewa a lokacin baza ki bani dama ba, ina ganin kamar baza ki soni ba, ina kuma kunyan ki ban san da wane ido zaki kalle ni ba banda haka wallahi banzo rayuwan ki da niyan yaudaran ki ba ko na cuce ki ba kuma ba laifina bane laifin zuciya ta ne da ta kasance raguwa, ya hadiyi yawu rabi'a na fara san ki tun ranar da na ganki a asibiti, na fara san ki tun sanda na saka idanuwana a kan ki na fara san ki badan komi ba se dan yes ina san ki tsakani da Allah, ina san ki da zuciya daya, ina san ki ba dan kyan fuskarki ba, ina sanki badan kyan dirin ki ba, ina sanki badan muryar ki ba, i just luv u becouse of who u are saboda kunyan ki,gentleness dinki, murmushin ki, tarbiyar ki, kamalar ki, kamun kan ki, i just love u so ni na sani is hard abunda kike fuskanta, ya mike na bar miki zabi na baki zabi, ki mun text zaki zauna dani ? ko ba za ki iya ba bazan cuce ki ba zan sauwaka miki and ill learn how to stop without ur luv. yaje daidai kofa ya tsaya juyo ya kalle ta ni na sani ina sanki kuma in kika kini sanki ne ajalina ni kadai nasan halin da na shiga da kike kula muhd , ki ke masa dariya, kike masa kwalliya, ki ke... hawaye yaji ya zubo masa ya ce rabi'a aure na dake nasan Allah ne ya hada kuma *SANADI NE* kafar sa daya a waje ya dakata again a karo na biyu dan Allah ki daina kukan nan i hate tear's daga nan ya fice gaba daya."

"nan ya barta da maganganun sa ta hade kai da gwiwa ta saki wani kukan hade da cewa ya zan yi? ina zan sa rayuwa ta?."
❣❣❣❣❣❣

"wajan karfe shidda da rabi na yamma aka soma hada2r kai amare ko ina ya kacame mutane nata shiri."

"da khadyjat da nasreen , sun gama shiryawa cikin laffaya me kyau sun zuba kyau a hankali suka nufi dakin da rabi ta zauna tun safe tana aykn kuka da tunani, jin budewar kofa yasa ta mike zata fada toilet , nas ta yi maza ta riko hannun ta hade da tsugunawa har kasa ta saki kuka,"

       _haba ya hajja,mesa kike san 'bata dangantakar mu? me sa kike san rusa farin cikin mu? mesa kike san daukar halin da ba naki ba? kada ki dau halin da ba naki ba, kiyi hakuri na boye miki ne saboda farin cikin ki._

"uhm nas ku je dan Allah na ji Allah ya baku zaman lafiya ameen."

" _zamu tafi kuma nagode na san cewa ni ba ciki daya muka fito dake ba dalilin da yasa kike mun haka kennan ba komai ta juya hade da jan hannun deejat zasu fita_ "

" _da hanzari tana kuka ta juyo ta hadasu ta rungume su tana kuka haka suma suka saki kuka, ta zaunar dasu hade da hada hannayen su gu daya da nata, ba wai ina kuka ko fushi daku bane saboda auren nan ba, ina fushi daku ne saboda a matsayin ku na shakikai na kuka iya boye mun abu me muhimmanci a rayuwata, amma ta wuce mu yafi juna dukkanin mu zamu shiga sabuwar rayuwa ne, zamu sake sabon takun a sabon guri da bakin mutane. da kyar deejat ta sa ta tayi wanka ta nada tata laffayar suka dasa hira a kan gado_ "

"rabi ki yafe mun ni nafi kowa lefi dan ni sheda ce a kan irin san da yah makyn ke miki ni na sani sau da dama nakan tura masa pics dinki, da abubuwan da kike so komai na rayuwar ki yana biye... ta dakata saboda umma da hajiya da suka shigo dakin da wasu gwagwonin su suka zauna hade da umartar su da su bada hankalin su gun su, nasiha suka sha sossai a kan aure, da me nene ma auran , da kuma me zamantakewa, da matsayin miji da girman sa hade da lada da ke cikin auran da irin girma da mace keda shi darajar wannan auran."

"sun sha kuka har a gun iyayen su maza sun sha fad'a kam, mummy ce ma ta ki fitowa tace su tarkata su bar mata gida seda aka gama munafurci za a wani mata iyayi wae tayi nasiha? taki fafur."

"nas ce ta shiga dakin data shiga tana kuka ta rungume uwar ta baya, tana kuka mummy ki yafe mun, kisa mun albarka kada ki kasance me fushi da ni a matsayina na er ki fushin ki a gare ni babbar illah ne a gareni da rayuwar aure na ki manta da komai kisa mun albarka nice fa nasreen dinki wadda kike so kike kauna kike alfahari da samun ta a matsayin er ki ni kuma a matsayin mahaifiyata ki sa mun albarka bazan samu farin ciki ba, se da albarka."

"tsakanin d'a da mahaifi se Allah uwa uwa ce ta juyo tana hawaye ta rungume ta hade da cewa Allah miki albarka Allah sanya alheri kibi mijin ki da iyayen sa."
"haka aka tafi da amare gidajen su,suna kuka suka rabu."

"nan aka bar amare da hallayen su."

*INA LABARIN ANGO?*

"Tun fitar sa daga dakin bin ammar yayi, suka wuce gidan su zayd. a daki ya kule kan sa yana hawaye shi kam besan ma irin san da yake rabi'a ba dama akwai mace da zata sa shi kuka? to me zata yanke? zata zauna dani? zata soni shi yasan fada kawai yayi da yace ta zaba wai ina ze iya sakin ta ma? no i can't i love her limitless and unconditionally."

"har magrib yana gun seda zayd ya dafa sa hade da mika masa wata leda ango ga kayan ka ya kamata ka fara shiri lokaci ya kusa amare na hanya fa."

"da mamaki ya daga kan sa ya bishi da 👀 ya ce um me kace ? harda rabi?"

"ha to da fa ba matar ka bace naji faisal ya kira muhd ya fada muku wai ku shirya."

"wayar sa ya dauka ya amsa ledar yana nagode, hajiya ya kira ya na tambayan ta. dariya masa ta ce kai kaniyar ka ni kake tambaya? please mum fada mun ko naji sanyi a raina!   eh suna hanya sun shirya maybe ma an kai deejat yanzun..."

"be bari ta karasa ba ya katse kiran yana murmusawa ya fada toilet."

"wanka yay ya sha wani yard fari ya fesa turare ya daura agogon sa ya sa takalmin sa ya same su a falo suna kallo da alama angwayen biyu sun tafi sai shi da nasa abokanan aka soma tsokanan sa ango ango gandoki  wai da wajan karfe 9 zamu tafi ko? wata harara ya banka masa a mafrki ko? suka bushe da dariya. da shi da zayd da ammar da ahmad suka shiga mota. naman kaza suka siyo da lemu da ruwa da yogourt. sannan suka dau hanyan gidan makyn dake *RIBADAU ROAD*"

  SANADI NEWhere stories live. Discover now