LIE

801 55 5
                                    

SANADI NE

KHAIRAT UP

F.O.W

Vote@wattpad khairi_muhd

         34-35

A hankali  ta  fara bude idanuwan ta tana kokarin motsa bakin ta . da sauri hajian ta je inda take tana kokarin daga ta dan ta jingina da jikin pillow.

sannu suke faman mata kawai tana gyada kanta kamar kadangare tana zubda siraran hawayen karya ay nan fa hajia ta kuma rud'ewa tana mata sannu ya akai? me yake damun ki? ina ke maki ciwo? duk a tare ta jero mata tambayoyin .

ba komai hajia kawai kaina ne yake mun nauyi ciwo yake mun se kafata da take zugi kadan2.

sannu kin ji ta juya tana kallan iya ta ce a kawo mata abinci da ruwa ta ci ta sha magani.

to hajiya an gama ta fita cikin azama dan cika umarnin uwardakin ta bata jima ba ta dawo da shinkafa da miya da ruwan roba da cup.

a lokacin makyn na falo yana jiran a kira sa dan duk hankalin sa ya gama tashi ya rud'e burin sa be wuce ya ga halin da take ciki ba da kuma san jin yadda taji wannan raunukan a jikin ta.

hajia ce ta bata abincin a baki tana ci har ta ci rabi ta sha ruwa da maganin.

kwanta hajja karama ki huta kin ji?.

to hajia se da safe.

Allah tashe mu lafiya.

ameen.

ta kashe wutan dakin hade ja mata kofan.

ana fita  ya mike da sauri ya taro hajiar yana cewa hajia ya jikin nata? ta fadi yadda ta samu raunin nan?

harara ta sauke masa ta wuce sa

bayan ta ya bi da gudu ya tare ta hajia dan Allah ki saurare ni kin ji ni ban san mesa kike mun haka ba ni kinga ban san...

makyn kaje kawai ka dawo da safe idan ta ji sauki zan ji daga gare ta, ta nuna sa da yatsa ta ce masa and idan na gane kai ne ka mata hakan zaka gane kuren ka.
hajia wallahil azeem ban sani ba wae mesa baza ki yarda dani ba?.

taya zan yarda da kai makyn matar ka ce fa kuma gida daya kuke da ita ta zo nan tana cikin wani mawuyancin hali, tana zuwa ta suma tana tare da akwatin kaya and what does all that mean? tell me taya zan yarda da kai ? me zaka fada mun kuma? just go gobe ka dawo maybe by then ta farka se muji komai ka roki Allah u are nt the cause, gudnyt!.

haka ya koma gida da kyar da addu'a yana cike da fargaba hakan nan gaban sa ke faduwa ya na ji a jikin sa kamar wani abun za a masa ko rabi'a  zata danganta sa da  wannan abun after all what ya faru jiya tsakanin su.

ga yunwa yana ji hakan nan yay alwala ya dinga sallah.
❣❣❣❣❣❣

Tun bayan sallar asuba bata runtsa ba tana ta taunar farcen ta jikin ta na rawa tsorace take gaba daya , wata zuciyar ta ce tsoran me? ae ba kya san sa kuma dan farin cikin ki da na masoyin ki kike haka ita kanta mummy tana san kasancewar ki da me san ki yah muhd. so kada ki kuma damuwa khnji ko everything is fare in love and war so ki kwaci yancin ki tun wuri just do it.

bayan sallar azahar makyn ya zo gidan yadda yaga suna kallan sa seda ya sha jinin jikin sa dan har alhajin su na falon ga faisal da kyar ya tsuguna makogwaran sa duk a bushe yake yana kokarin gaida su ne yaji hajia ta fella masa mari ya dafe kuncin sa

makyn nagode dama irin tarbiyar da na baka kennan abunda yasa ka auri yarinyar kennan dan ka wulakanta ta? ka aure ta ka mata sakin wulakanci?

a razane da kidima ya dago kan sa ya na bin hajiyar da kallo kamar wani zarare ko wanda aka ce iyayan sa sun mutu.

hajiya saki? ni kuma ? wa na saka?

ka fi kowa sani matan ka nawa?

hajiya nifa ban saketa ba a kan me zan sake ta bayan ina santa ina kaunar ta.

wani marin ta kuma masa wanda a yanzu be damu da marin ba .

rabi aka kirawo ta fito tamkar mutuniyar kirki (😂)

ta zauna a kasa tana mike kafafuwan ta tana kuka a hankali.

hajiya ta ce fada mun meya faru.

ta kuma fashewa da kuka da kyar tayi shiru ta daina kukan ta fara karanto karya.

hajiya dama tun da aka yi auren yake mun mugunta be ban abunci be bari azo mun kuma ga duka da na masa dan laifi se ya dake ni to jiya kuma na gaji na ce me ya  sa ya canja mun ae sai ya fara farfasa kayan falan ya na jefa dasu ko yanzu in kika je zaki ga gidan ma a hautsine to garin hanasa ne na taka glass din shi kuma ya ce ya sake ni saki uku hade da jefani na buge da glass. (ta so rubuta sakin ta ga za a gane ta saboda rubutun su bezo iri daya ba shi sa ta canja tsarin.)

a lokacin da za a tsaga jikin sa tabbas da anga babu jini a jikin sa tsabar tsananin mamaki da kaduwa sanda wasu zazzafan hawaye suka zubo masa a kuncin sa.

explain yourself yaji hajia ta fada.

hajiya bani da abun cewa saboda bani da sheda a kan hakan se Allah wata ran gaskiya zatai halinta duk yadda zan so na fada maku baza ku yarda ba ya mike ya juya yana kallan ta ke kuma kije kiyi ta fama da igiyar aure na uku a kan ki bazan sake ki ba kuma alhakina a kan ki.

  SANADI NEحيث تعيش القصص. اكتشف الآن