HOME SWEET HOME

1.1K 75 4
                                    

SANADI NE

KHAIRAT UP

48

shigar dare yayi ma garin kano napep ya samu ya masa kwatancen inda za a kai sa.

wanka ta fito amma gaban ta dukan uku2 yake sam ta kasa samun nutsuwa da kwanciyan hankali. duk da ta samu ta fadi damuwan ta still hankalin ta ya kasa kwantawa gaba daya tunanin ta yana ga makyn.

gidan hajja ya sauka dan ya tabbatar cewa suna can tunda hajia ta sanar masa.

dukan su suna zaune ne a falo tare da mummy da dady umar ana san jin me ya sa aka yi sakin wanda mum ta tada hankalin kowa ta kasa hakuri rokan su hajja take a kan a roka mata afuwa a gun mijin ta ya maida ta dakin ta kuma tayi alkawari baza ta kuma yin komi na mugunta ba a gun en dangin kuma anyi2 ta fadi me ya jawo sakin taki hakan ya kuma kular da hajja ta daka mata tsawa hade da shan mur ta ce da ita wai zaki fada mun me ya faru ko kuma kukan zaki cigaba da yi?

ta kalli umar cike da fushi ta ce masa kai bana san shashanci kana ji na ko a wannan stage din da kuka aurar da yara zaku fara shirme ko me ? na ce ku fada mun me ke faru kun ki to naji amma ka maida matar ka tunda ko ma mene ne ta bada hakuri ko kuwa?

kan sa a kasa ya ce hajja dan Allah ki yi hakuri bana san ki sa mun doka na karya,bana burin kin miki biyayya a rayuwa ta amma hajja dan Allah kada ki shiga maganan nan.

hajja tai shiru tana nazarin maganan omar da kyau dan tasan halin sa ta san na mum kuma tasan lallai abunda ya hada su me girma ne tunda ya kasa fada mata kuma ya ki maida mummyn yaran.

ita kam mummy sai ta kuma fashewa da wani kukan tamkar ranta ze fita haka taji.

haba daddyn yara ni ce fa ina neman alfarma badam hali na ba dan darajar ya'ya na ka maida auran nan....

ki daina sa mun sunan ya'ya a harkar ki dan kuwa ke din baki san girma da darajar su ba, idan na ce zan zauna dake na miki karya, kuma baki da hujjan zama mun a gidan na dan ya'yan sun yi aure suna gidajen su , karamin kuma yana makaranta kuma hauwa'u zata kula mun da tarbiyan sa iya zaman ma da muka yi tare ya wadatar ki godewa Allah.

hannu ta dora a kan ta tana kallan hajia amina tana san ta sata a maganar ita kuma taki sa bakin ta balle ma ta kalle ta har ta tausaya mata.

haba alhaji da girma na da ya'ya na kace wai ka sake ni? adalci kenan ko me?

...yana niyan magana ne suka jiyo sallama gaba daya suka juya a mamakance ,

wa'alaikum salam abbie ya amsa masa.

hajia amina ta bisa da kallo na mamaki da jindadi

haka ma omar

karasowa yayi ciki ya tsuguna gaban hajiar sa ba tare da ya kalli ragowan en dakin ba ya ce da ita hajia ina RABI'A ?

kan sa ta shafa tare da nuna masa dakin da take.

da azama ya mike ya nufi dakin

tura wa yayi kawai ya shiga

tana zaune kan gado tana aikin da ya zame mata jiki kwana biyu wato kuka taji alamun bude kofa duk da tasan dama akwai yuwuwar shigowan wani a ko wane lokaci juyawa tayi dan wani irin strange feeling ta daban taji kanta a ciki.

mikewa tayi kamar ta sa gudu haka taji kanta, a lokacin bazata iya fadan irin murna da take ciki ba bakin ta na rawa ta ce da shi YAH MAKYN kai ne ko kuma mafarkin da na saba ne nake yi? ya Allah idan mafarki nake kada kasa na farka idan kuma gaske ne kada wannan lokacin ya tafi ya tsaya a haka ta fada tana hawaye.

a hankali ya karasa inda take direct cikin ta ya dora hannun sa a kai, ya shafa yaji tudu wani irin dadi da sanyi yaji a ransa ya tsinci kan sa da zubda hawaye hade da tsugunawa a gaban ta ya kai ma cikin kiss, ya rungume cikin yana kuka ya ce Allah nagode maka.

  SANADI NEWhere stories live. Discover now