chapter 5

1.4K 102 0
                                    

~😭SANADI NE😭~

~NA KHAIRAT UP~

~F.O.W~

  ~vote @wattpad khairi_muhd~

            ~05~

"matashin saurayi ne me kimanin shekaru ashirin da tara ,fari ne sol da ka gan sa kasan bafulatani ne usul,gashin kansa yalwatace ne baki sidik, da dan karamun baki idanun sa ba laifi ga hanci a tsaye (pointed),dogo ne amma ba can ba yana da budaddan kirji kasancewar yana workout. kaftan ce a jikin sa ya na sanye da hula kamshin sa ya bade dakin."

"tsugunawa yay ya gaida umma hade da tambayar ta me jiki."

"da sauki ta fada tare da cewa tashi dan kirki tashi dan allah."

"mikewa yayi ya dan saci kallan rabi da ke kwance a ransa ya ce what a beauty in ta samu kulawa da wayewa za a yi zuban kyau a birnin kano."

"murmushi ya saki ya ce da hajiyar su ina waje ."

"to sai na fito"

"to hajiya!"

"hajiya mungode sossai hakika mun fada hannu na gari a garin da bamu da kowa bamu da komai sai allah. hajiya rayuwa abun tsoro ce tamkar mafarki ce ."

"ai ba komai hauwa duk wanda ya taimaki wani allah yana tare da lamuran sa fatan mu ku maida mu tamkar en uwan ku na jiki bamu da mugun nufi a tare daku da zuciya daya da gaskiya muke kaunar ku. zamu kula da ku har ki samu abunda ki ke nema."

"umman tasa kuka ta ce mun gode Allah ya saka da alheri,ya biya ku, ya kara muku imani da daraja."

"amin ae wannan addu'ar ma ta wadatar ta isa komai. bara mu koma mu kam se da safe zan ayko khadijat da faisal da abun kari"

"mun gode fa "

"ahan seda safe mama na"

"idanu rabi kawai ta lumshe"

" a cikin mota ta same shi da alama waya yake yi yana ganin hajiya ya ajiye ya fita ya bude mata kofar gaba ya rufe ya koma yana jan su."

"yarinyar nan ta shiga raina a lokaci daya tamkar su ayshat haka nake jin ta a raina "

"murmusawa yay ya ce hajiya kenan ae ke dama saurin sabo ne da ke yarinyar da magana ma da zama be hada ku ba na one hour?"

"ba a nan take ba akwai haduwar jini and over all sunan ammi gare ta fa *RABIA'TU*"

"sunan ya maimaita  *RABI'ATU* "

"hajiya kenan kawai dai magana ta fito dan tsohuwa ake san ta"

"eh naji"

"haka suka koma gida a gajiye!"

"satin su daya da kwana uku a asibiti aka sallame su nan hajiya ta dage ta sa umma ta yarda ta dawo gidan su da zama daki guda aka gyara musu ita da diyarta a ka maida su en gida tamkar an dade da sanin juna."

"a hankali rabi ta fara motsa hannun ta ga kawa ta samu dan khady akwai magana haka ita ma rabi ."

"hakan be hana umma taimakawa ba a wajan aykn gidan ba shara, wanke2, wani zubin har da girki tana yi kaman su tuwo da dambu da su funkaso alele abuncin gargajiya dai gasu kunu da zobo.zobon ma anfi mararin sa a gidan har fridge ake lodawa da shi."

"gaba daya sun saki jiki da junan su cikin wata daya umma da rabi aka kile."

"da term ya kare alhaji ya sa a samawa rabi makarantar boko, daga js1 dai aka sata dan bata iya karatn ba kuma da lesson teacher a gida hade da malamin islamiya kuma alhamdulilah ta na picking ba laifi."

     "ayshat ce ke saukowa daga bene suka yi karo da rabi wayar ta har ta fadi a kasa ta fashe."

"a tsure rabi ta tsuguna har kasa ta tattara part's din wayar a hannu jikinta na kyarma ta ce dan allah aunty aysha kiyi hakuri wallahi ban kula kin tafe ba."

"saboda kin makance ko? wannan ae wulakanci ne dubi yadda ki ka fasan wayata me tsada? uban ki ne ze biya eh?"

"hawaye suka zubo mata ta ce aunty ki yi hakuri dan allah"

"mtsw matsiyata kawai an zo an ga arziki an nace an zaune ana ta barna ba saban ba bar nan dan ubanki jaka villager kawai."

"matsawa tayi tana kuka ta koma gefe har seda ayshat ta bar gun ta durkusa a gun tana kuka ita bata san dadin uba ba, bata san kamaninsa ba, bata san gatan sa ba, amma tana jin haushi idan an zagar mata uba. hakika ayshat ta ci wata daraja dan da wani ne seta masa barin makauniya."

"MAKYN da ke sama yana kallan su yaji wani iri a ran sa wanda be san dalili ba kai ya gyada ya koma dakin sa kawai jikin sa na masa mazari."

"dakin su ta koma ta fada kan gado ta saki kuka umman da ta fito daga toilet  ta ce ah a rabi me ne ne ya saki kuka? "

"umma ba komai kaina ne yake mun ciwo kawai"

"to me abun kuka kuma banda shirme ba se ki je ki sha magani ba kukan me ze miki?"

"to umma"

"tashi maza akwai pandol a drower ta ki dauka ki sha zanje na dafa ma hajiya tuwan alkama."

"to zan zo na taya k"

"aa huta autar mata huta abunki."

"dariya tayi tana san sunan autar mata."

"murmusawa shima yayi ya ce of course u deserve the name autar su."
"ayshat ya kwalawa kira "

"ta sauko tana kumbure2 dan an fasa mata waya ta ce gani"

"dan uban ki ni sa'an ki ne da zaki mun tsaye?"

"ta dago idanun ta ta ce uba na fa kace?"

"zaki rama ne?"

"kasa tayi da kai ta ji wasu hawaye sun zubo mata ta ce amma dai yaya me na maka ka zage ni?"

"wata tsawa ya daka mata wadda ya mugun tsorata ta ta,kuma sakin kukan ta gaba daya da karfi."

"hajiya na kitchen ta fito ah lafiya yaya me ya faru kuma? ke me kika masa?"

"hajiya ba abunda na masa hasalima ni yau in ba yanzu ba kwata2 ban gan sa ba kawai ya kirani ya zage ne"

"hajiya ina koya mata darasi ne naga wani hali ta dauko na rashin mutunci wai a kan yarinyar nan me sunan granny ta buge ta bata gani bh ta ce uban ta sau biyu harda jaka matsiyaciya ina kallan su tsugunawa tay tana bata hakuri amma seda ta mata tass ke ba villeger bace ke an zage ki kin ji haushi kina kuka amma kin san ki zagi uban wani to ki sani uba be fi uba ba stupid."

"hajiya wayata fa ta fasa mu..."

"shut up ayshat wulakanta mutum na koya miki dama ko? to nagode "

"hajiya am sorry kar ki fushi dani."

"to ki bawa mama na hakuri"

"to ta fada da sauri badan taso bh sedan bata san batawa hajiyar ta rai buh seta rama a kan rabin."

"ko ke fa ae mutum ba abun rainawa ba ne ki daina "

"to wayata fa?"

"dnt wrry anjima kuje da yaya ki zabi wata."

"thanks hajiya"

"ni ba inda zanje da mara kunya"

"am sorry yaya!"

"kar ki kuma"

"insha allah."

"ok muje"

"lemme take my veil"

"ina mota to"

"ok!"

  SANADI NEWhere stories live. Discover now