chapter 4

1.4K 98 0
                                    

~😭SANADI NE😭~

~F.O.W~

~KHAIRAT UP~

~Vote @wattpad khairi_muhd~

              ~04~

"tafe suke da kafa duk sun sha rana se gumi suke da hakki ga yunwa ga gajiya ga ba gun da suka sani ba sannaya."

"a gajiye rabi ta kalli mahaifiyar ta tace umma ta ruwa yunwa na gaji mu huta."

"idanuwan ta farare kal ta daga sama rana ya doke ta tuni taji wani jiri ya kwashe ta tana jin juwa na daukan ta."

"rabi mu tsallaka can mu siya ruwan "

"a garin tsallakawa wani tautsayi ya afku ji kake kuuuuu mota ta ja burki da karfi bayan naji faduwar abu ragwaf a kasa."

"innallilahi wa inna illahir raju'un me motar ke fada."

"sabi'u me ya faru?"

"wani dattijo ya fada yana ajiye jaridar hannun sa da sauri"

"alhaji ae tsautsayi ne ya afku hatsari aka yi"

"subahanallahi! asha asha fita mana ka duba lafiya dai ko?"

"ae mutane ma sun taru suna jajantawa driver ya dauki rabi ya sa a bayan mota , umman ta na kuka ta shiga gidan gaba."

"wani private aka kaisu a emergency aka amshi rabi wadda kanta ya bugu yana ta jini"

"wayar alhajin ce ta dinga kara ya dauka hello hajiya!"

"hello alhaji baku karaso bane?"

"awanni na biyu da shigowa kano muna asibiti ne."

"subahanallahi me ya same ka? me ya faru?"

"cool down tsautsayi ne da kaddara wata yarinya muka buge garin wucewa ita kuma zata tsallaka titi."

"subahanallah. alhaji kamun texting din gun ina nan zuwa "

"ok"

"baiwar allah ki daina kuka zata tashi insha allah ki mata addu'a ina mahaifin ta?"

"bamu san inda yake ba muma shi muke nema mu en garin bugaje ne dake katsina mun zo nan neman mijina ne bamu da kowa bamu da komai a garin nan."

"tausayin su ya kama alhaji ahmad ya ce ki daina kuka allah yana tare da ku kuma zan taimaka muku iyakar iyawata dan ganin kun samu kulawa."

"nagode alhaji allah ya saka da alheri"

"amin!"

"jim kadan hajiya ta zo tare da khadijat da faisal da flask din abinc"

"gun mijin ta ta nufa tna masa jajen abun."

"wato aminatu akwai tausayi a gun bayin allahn nan  zan taimaka musu har taga mijin ta da fatan zaki goya mun baya kamar koda yaushe?"

"insha allah "

"zuwa tayi ta dafa umman ta juyo gaban ta ya fadi dam tana san gano wani abu amman ta kasa gasgata hakan kawai ta gyada kan ta tana hawaye."

"baiwar allah kiyi hakuri kinji cuta ba mutuwa ba ce ki dauri ki taso ki ci abinci yarinyar ki zata tashi kin ji?"

"kai ta gyada kawai ta mike."

"sai dare rabi ta farka an nanada mata bandeji a kai hannun ta ma da karaya "

"umman ta mike da sauri ta rungume ta tana mata sannu da jiki!"

"umma zafi"

"sannu hakuri zaki"

"haj.amina ta shigo da fara'a ta ce au ta tashi? bara a kira likita ya duba ta"

"MAKYN ka je ka kira doc."

"juyawa yayi ya fita daga dakin"

"sannu mama na sannu"

"youwa ta fada a hankali"

"likita ya duba ta da kyau ya ce a bata abinci a kuma bata magani"

"haj.amina ta bata abinci a baki ta kuma bata magani! "

"MAKYN ka zo mana ka duba me jikin ka damu zaka zo kazo kuma tsaya a waje kaman pole"

  SANADI NEWhere stories live. Discover now